Ministocin harkokin Masar da Tnisia sun tattauna batutuwan Gaza, Libya, da Sudan
Published: 26th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdel Aty ya tattauna da takwaransa na Tunisiya Mohamed Ali Nafti kan batutuwa da dama da suka shafi yankin gabas ta tsakiya a gefen taron majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.
Dangane da ci gaban da halin da ake ciki a Gaza, Abdel Aty ya gabatar da kokarin Masar tare da hadin gwiwar bangarorin shiyya da na kasa da kasa, na cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta ba da tabbacin sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni da kuma bude hanyar shigar da kayan agaji.
Dangane da halin da ake ciki a kasar Libya, ministocin biyu sun jaddada muhimmancin tallafawa tsarin siyasar Libya, da janyewar sojojin haya da na kasashen waje, da kuma ci gaba da aiwatar da tsarin sassa uku na kasashen dake makwabtaka da Libya.
A cikin wannan yanayi, ministan na Masar ya yi maraba da sanarwar da manzon musamman na babban magatakardar MDD ya bayar game da taswirar warware rikicin kasar Libya, musamman dangane da batun kafa gwamnatin wucin gadi da za ta shirya gudanar da zabukan kasa a kasar Libya cikin wa’adin watanni 12 zuwa 18.
Bangarorin biyu sun kuma tattauna batutuwan da suke faruwa a Sudan, inda Abdel Aty ya jaddada matsayar Masar na goyon bayan hadin kan kasar Sudan, da ‘yancin kanta, da kuma kudurinta na tallafawa hukumomin kasar Sudan. A cikin wannan yanayi, ya tabbatar da cewa Masar a shirye take ta shiga shirye-shirye da nufin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take da kuma kawo karshen matsalolin jin kai da al’ummar Sudan suke ciki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Mutane sama da rabin miliyan sun koma Khartoum duk da matsalar yaki August 26, 2025 Iran Ta godewa Rasha Dangane Goyon bayanta Kan Hakkinta Na Tace Yuranium August 25, 2025 Iran da saudiya Sun Bukaci Hadin Kan Musumi Don Kawo Karshen Yaki A Gaza August 25, 2025 Iran Ta Yi Kira Ga Kasashen Musulmi Su Yanke Hulda Da HKI A Taron OIC A Jedda August 25, 2025 Iran Da Kasahen E3 Zasu Tattauna Batun Shirin Nukliyar Kasar A Sitziland A Gobe Talata August 25, 2025 Bangaladesh Ta Kasa Samun Kudaden Kula da Yan Gudun Hijiran Rohinga August 25, 2025 Jagora: Hadin Kan Al’umma, Jami’ai Da Sojojin Kasa Da Suke Dauke Da Makamai Jan Layi Ne August 25, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Bukatar Gudanar Da Hidima Ga Al’umma Daga Kowane Dan Kasa August 25, 2025 Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Aniyar Iran Na Wurga Makiya Cikin Nadama August 25, 2025 Kafofin Watsa Labaran Isra’ila Sun Ce: Ba Za A Iya Hana Sojojin Yemen Kai Hare-Hare Kan Isra’ila Ba August 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin
Kasashen Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan hadin kan Musulmi game da halin da ake ci a yankin
Wannan bayannin ya fito ne a yayin ganawar sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani da yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Mohammed bin Salman a birnin Riyadh inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin.
Ganawar dai ta nuna wani muhimmin mataki a huldar diflomasiyya ta tsakanin Tehran da Riyadh.
Larijani ya tafi Saudiyya ne bisa gayyatar da ministan tsaron kasar ya yi masa, inda ya jagoranci tawagar da ta hada da mataimakin sakataren harkokin kasa da kasa Ali Bagheri Kani da mai ba da shawara kan harkokin yankin Gulf na Farisa Mohammad Ali Bek.
Ganawar na zuwa ne kwana guda kacal bayan da shugaba Masoud Pezeshkian ya gana da bin Salman a gefen taron gaggawa na kasashen Larabawa da Musulunci da aka yi a birnin Doha, inda bangarorin biyu suka nuna gamsuwarsu da yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke kara habaka.
Ziyarar Larijani a Riyadh ita ce ziyararsa ta uku a yankin tun bayan hawansa mulki a ranar 5 ga watan Agusta, biyo bayan ziyarar da ya kai a Iraki da Lebanon.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci