Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji
Published: 11th, April 2025 GMT
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi wata muhimmiyar ganawar sirri da shugabannin sojojin Nijeriya a Abuja ranar Alhamis.
Taron wanda ya gudana daban-daban tare da babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede da babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ikechukwu Ogalla da babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hasan Bala Abubakar na shirin sake tura wani sabon yunƙuri na ɗaukar matakin haɗa kai kan maharan Boko Haram.
Majiyoyi daga taron sun bayyana cewa, tattaunawar ta ta’allaka ne kan ƙarfafa ayyukan soji a yankin Arewa maso Gabas, da inganta musayar bayanan sirri da magance yawaitar hare-haren da ’yan tada ƙayar baya ke yi a baya-bayan nan.
Gwamna Zulum a ranar Talatar da ta gabata, yayin wani taron tsaro da aka gudanar a Maiduguri, ya koka kan yawaitar hare-haren da ’yan ta’addan ke kai wa a cibiyoyin farar hula da na sojoji, inda ya yi kira da a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki don kaucewa halin da ake ciki.
Zulum ya samu rakiyar Sanatoci masu wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, Borno ta Arewa Mohammed Tahir Monguno da Borno ta tsakiya Barista Kaka Shehu Lawan.
Sauran a tawagar gwamnan sun haɗa da: Mukhtar Betera Aliyu da Injiniya Bukar Talba, ‘yan majalisar wakilai da Farfesa Usman Tar, kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida na Jihar Borno.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum Boko Haram
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan ta’adda na kafa doka da karɓar haraji a Arewa — Dambazau
’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a.
Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.”
Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga.
“Mun kai wani matsayi da ’yan ta’adda da ’yan bindiga suka karɓe wasu yankuna, suna karɓar haraji da kuma kafa dokoki a cikinsu.
Sarkin Musulmi ya ba wa makarantu tallafin N1.3bn a Kebbi Matan sojojin da suka mutu na neman agaji“An kashe dubban mutane, an raba miliyoyi da muhallansu. Yawan zawarawa da marayu ya ƙaru, manoma sun rasa gonakinsu, makiyaya kuma sun rasa dabbobinsu — ba tare da wani mataki daga hukumomin gwamnati ba,” in ji shi.
Dambazau ya shawarci gwamnonin Arewa su kafa ma’aikatar ma’adinai a jihohinsu domin haɗa kai da hukumomin tarayya wajen sarrafa albarkatun ƙasa da ke yankunansu, don ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage talauci da kuma kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Ya kara da cewa, domin magance kashe-kashe da rashin tsaro a Arewa, dole gwamnatocin jihohi su dawo da martabar sarakunan gargajiya, su farfaɗo da harkar noma da yankin ya shahara da ita, su kuma magance matsalar yara marasa zuwa makaranta, tare da tabbatar da haɗa kan jama’a.
“Ina so in jaddada cewa sama da kashi 70 cikin 100 na masu fama da talauci sakamakon rashin tsaro suna Arewa. Tsattsauran ra’ayin addini babban barazana ne ga tsaro a yankin, wanda ya haifar da ƙungiyoyin Boko Haramnda Lakurawa da sauran ’yan ta’adda da ke addabar jama’a,” in ji shi.
Tun da fari, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya jaddada cewa batun tsaro ya shafi kowa da kowa, yana mai cewa: “Dole mu zauna tare mu tattauna yadda za mu magance wannan matsala.
“A da va haka muke ba. Najeriya ba haka take ba. Idan muka haɗa kai, muka fahimci juna, muka aiwatar da shawarwarin da muka cimma, za mu samu zaman lafiya.”
A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta haɗe kai domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar ta.
“Ina damuwa da yadda matsalar tsaro ke ƙara kamari a yankin Arewa maso Yamma. Ya kamata wannan taron ya nazarci tushen matsalar — watakila tana da nasaba da sauyin yanayi da wasu abubuwa,” in ji shi.
Shi ma Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bayyana cewa taron zai bayar da dama wajen tattauna matsalolin da ke addabar Arewa tare da neman mafita mai ɗorewa ga yankin.