Rasha Ta Sanar Da Kakkabo Da Jirage Marasa Matuki 57 Da Ukiraniya Ta Harba
Published: 19th, March 2025 GMT
Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki 57 da kasar Ukiraniya ta harba zuwa yankuna mabanbanta na kasar.
A yau Laraba ne ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta sanar da cewa; An harbo jiragen marasa matuki 35 da aka harba wa yankin Kursk dake yammacin Syria a jiya da dare.
Kwanaki biyu da su ka gabaa ma dai sojojin na Rasha sun sanar da kakkabo wasu jirage marasa matuki na Kasar Ukiraniya 31 da aka harba a yankuna mabanbanta na kasar.
A gefe daya sojojin na kasar Ukiraniya sun kai wasu hare-hare akan garuruwan da suke kan iyaka da Rasha, da su ka hada garuruwan Zawalishnika da Korsta.
Majiyar tsaron Rasha ta ce, sun kashe sojojin Ukiraniya 220 a cikin sa’oi 24.
A gefe daya Amurka ta sanar da cewa a ranar Lahadi mai zuwa za a bude tattaunawa a tsakanin Rasha da Amurka a birnin Jidda na kasar Saudiyya.
Manzon musamman na Amurka Steve Vitcov ya bayyana cewa,tattaunawar za ta mayar da hankali ne akan yadda za a kawo karshen yakin kasar Ukiraniya.
A jiya Talata an yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin kasashen Rasha da na Amurka akan batun kasar ta Ukiraniya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Ukiraniya ta sanar da
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.
Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan