Hizbullah ta yi Allah wadai da harin Amurka da Birtaniya a kan Yemen
Published: 16th, March 2025 GMT
Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da harin da Amurka da Birtaniya suka kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula da dama a daren jiya Asabar.
Kungiyar Hizbullah ta yi Allah wadai da wadannan hare-haren wuce gona da iri da Amurka da Birtaniya suka kai kan wasu unguwanni a Sanaa babban birnin kasar, da kuma wasu larduna da dama, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.
Bayanin ya kara da cewa, “Wannan zaluncin ya zo ne a matsayin wani yunkuri na murkushe wannan al’umma mai girma mai tsayin daka wajen ci gaba da nuna goyon bayanta ga al’ummar Gaza da kuma ci gaba da nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu.”
Sanarwar ta yi nuni da cewa, hare-haren da ake kaiwa fararen hula da muhimman ababen more rayuwa a kasar Yaman, ya sake bayyana hakikanin gaskiya da mummunar fuskar gwamnatin Amurka, wadda ke aiwatar da ayyukan cin zarafi ga kasashen da ke adawa da manufofinta a yankin da ma duniya baki daya.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bayyana harin da Amurka ta kai birnin San’a a matsayin laifin yaki da kuma keta dokokin kasa da kasa, wanda kuma ya yi dai-dai da irin hare-haren Isra’ila a kan Gaza, Siriya, kuma Lebanon.
Hizbullah ta ci gaba da cewa: Al’ummar kasar Yemen masu tsayin daka, wadanda suka rubuta kasidu na jarumtaka tare da jinin shahidansu na goyon bayan al’ummar Palastinu da Gaza, kuma suka tsaya tsayin daka a karkashin jajircewar shugabanninsu, irin wannan al’umma ba za su ja da baya ba wajen tinkarar wannan zalunci na makiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu da suka rasu.
Ya ce, “Sun taru ne domin yin addu’a lokacin da ’yan ta’addan suka sauka a kansu. Mun kwashe mutane da yawa da suka samu raunukan harsashi zuwa Babban Asibitin Mubi da ke maƙwabtaka da Jihar Adamawa.
“Adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, saboda wasu sun tsere cikin daji da raunukan harsashi. Ana ci gaba da aikin nemowa da ceto waɗanda ke cikin daji,” in ji shi.
Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya ya rasuSanatan Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya ci gaba da yin Allah wadai da hare-haren, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin abin da ya wuce tunanin dan Adam.
“Ko jiya ma, na samu kiran gaggawa cewa an kashe sama da ’yan banga 10 a wani yankin da ke tsakanin Karamar Hukumar Hawul ta Jihar Borno da garin Garkida a Jihar Adamawa.
“Al’ummata na fama da munanan asara ba tare da wani faɗa ba. A cikin wata guda da ya gabata kaɗai, an kashe sama da mutum dari a hare-hare da dama yankunan Sabon Gari da Izge da Kirawa da Pulka da Damboada Chibok da Askira Uba da wasu da yawa da ba zan iya lissafawa ba,” in ji Sanata Ndume.