Gwamnatin Da Mutanen Kasar Somalia Sun Ki Amincewa Da Karban Mutanen Gaza
Published: 16th, March 2025 GMT
Gwamnatin da kuma mutanen kasar Somalia sun ki amincewa da shawarar shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa a Gaza zuwa kasar Somalia.
Shafin yanar Gizo na ‘Africa News’ ya nakalto yan kasar Somalia da dama suna fadar cewa yan kasar da kuma gwamnati ba zasu amince da korar Falasdinawa a Gaza, zuwa kasar Somalia kamar yadda shugaban kasar Amurka Donal Trump yake bada shawara ba.
Mohamed Mohamed Elmi Afrah daya daga cikin mutanen kasar Somalia wanda Shafin labarai na ‘Africa News’ yayi wa tambayoyi danganne da haka, yace: Ban tsamman cewa mutanen kasar Somalia zasu aminjce ba haka ma gwamnatin kasar.
Kafin haka dai wasu da dama suna ganin korar Falasdinawa daga Gaza ra’ayin yahudawan sahyoniyya ne, amma bayan da shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda yahudawa suke jujjuyawa ya gabatar da shi a fadar white House al-amarin ya sami maida martani mai tsananai daga shuwagabannin kasashen duniya. Da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
Trump ta farko ya bada shawarar cewa kasashen Jordan da Masar su karbi mutanen Gaza, da suka ki sai ya koma kan sudan da Somaliya Somali landa da wasu kasashen kamar saudiya da sauransu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mutanen kasar Somalia
এছাড়াও পড়ুন:
Syria: Adadin Wadanda Aka Kashe A Rikicin Bangaranci Sun Kai 70
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Syria ta nuna kin amincewarta da tsoma bakin kasashen waje a rikicin da kasar take fuskanta.
Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ta kuma ce; gwamnatin kasar za ta kare dukkanin ‘yan kasar.
Kasar Syria tana fuskantar fada a tsakanin ‘yan Duruz da kuma sojojin gwamnatin kasar a yankin Sahanaya da Ashrafiyyah a yankin Suwaida.
Ya zuwa yanzu dai adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 70.