Jumhuriyar Najer Ta Bukaci Tarayyar Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi A Kasar
Published: 15th, March 2025 GMT
Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Najer tana fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yemai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar.
Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar.
Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300.
Wasu wadanda suka san al-amura a Jumhuriyar ta Niger sun bayyana cewa matsalar ta taso ne bayan da gwamnatin sojojin kasar suka sami matsala da kamfanin kasar China wanda yake haka da tashen man fetur a matatan mai ta Soraz, wanda ya kai da sojojin suka bukaci mutanen china su bar kasar.
JMI tana haka da sarrafa danyen man fetur tun shekara ta 2011, amma matsala tsakanin gwamnatin sojojin kasar da kasar China ta sa sun kasa samar da man da zai water da kasar, ballanta na a yi maganar ganga 100,000 da kasar take son fara saida shi ga kasashen waje, ta hanyar bututun mai wanda zai bi ta kasar Benin zuwa kasuwannin duniya.
Juye-juyen mulkin da aka yi a yankin Sahel dai ya sa Jumhuriyar Niger bata jituwa da kasashen kungiyar ECoWAW. Wacce Najeriya take jagoranta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An harbe manomi saboda rikici kan filin kiwo a Borno
Rikici kan filin kiwo tsakanin wani makiyayi da wani manomi ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai shekaru 32 a kauyen Muva da ke cikin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, a ranar 2 ga watan Disamba, 2025, da misalin karfe 4:00 na yamma, Alhaji Usman, wanda ke kiwon shanu, ya samu rashin jituwa da Jauro Ishaya mai shekaru 43, kan rikicin filin kiwo.
A cewar majiyar, yayin takaddamar ne aka zargi Jauro Ishaya da harba bindigar gida wadda ta sami Alhaji Usman a ciki, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.
An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Askira, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa nan take.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce ta kama wanda ake zargi, kuma tana ci gaba da kokarin kwato bindigar da aka yi amfani da ita a lamarin.
Majiyoyi sun kara da cewa, sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ’yan sanda a Maiduguri ya fara gudanar da bincike kan lamarin.