‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’
Published: 11th, March 2025 GMT
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris.
Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira.
An hana tashe bana a Kano — Nalako NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar NajeriyaSanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko.
Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba haka lamarin yake, yana mai cewa sai a ƙarshen watan nan na Maris yarjejeniyar za ta ƙare.
“Ya kamata a fahimci cewa yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a farashin naira ta wata shida ce, kuma da sharaɗin akwai man, wadda za ta ƙare a ƙarshen watan Maris na 2025.
“A ƙarƙashin wannan yarjejeniyar mun sayar wa Matatar Dangote gangan miliyan 48 ta ɗanyen man fetur tun daga watan Oktoba na 2024 zuwa yanzu.
“A yanzu muna ci gaba da tattaunawa domin ƙulla wata sabuwar yarjejeniya,” in ji shi.
Masana na cewa idan NNPC ya daina sayar wa Matatar Dangote mai a naira hakan zai iya haddasa hauhawar farashin man, maimakon sauƙin da ake tunanin hakan ya jawo a baya-bayan nan.
Dangote da NNPC sun rage farashi a gidajen maiA makon jiya ne NNPC ya rage farashin litar man fetur a gidajen mansa da ke faɗin Nijeriya kwanaki bayan matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man a gidajen sayar da mai masu alaƙa da ita.
Ɗaya daga cikin manyan dillalan man fetur a Najeriya ya tabbatar da cewa a yanzu “NNPC na sayar muna da man fetur ne kan naira 840 a Legas, sai kuma naira 875 a Calabar da kuma Fatakwal.”
Hakan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan Matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar man, inda mutanen Nijeriya ke sayen fetur ɗin cikin farashin da ya yi ƙasa da na NNPC a gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar.
Wannan ya sanya aka riƙa ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen man fetur ɗin da ke da alaƙa da matatar ta Dangote.
Farashin da Dangote ya sanar zai riƙa sayar wa dillalai abokan hulɗarsa shi ne naira 825 daga 890, ragin naira 65 ke nan kan kowace lita.
Karo na biyu ke nan kamfanin yana rage farashin man a watan Fabrairun 2025, abin da dillalan man suka bayyana da “abin a yaba.”
Rage farashin ya sa man na Dangote ya zama mafi rahusa idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi ƙasar daga ƙetare.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗanyen Man Fetur Matatar Dangote sayar wa Matatar a farashin naira sayar wa matatar Matatar Dangote rage farashin za ta ƙare
এছাড়াও পড়ুন:
Araghchi : Iran a shirye take ta shiga tattaunawa da Turawa bisa mutunta juna
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen.
Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya – Birtaniya, Faransa da Jamus – sun kasa cika alkawarin da suka dauka na dawo da Washington cikin yarjejeniyar.