Gina Mutane Don Bunkasa Hazakarsu Na Daga Cikin Ajendar Sin Na 2025
Published: 10th, March 2025 GMT
Kirkira ita ce kashin bayan ci gaba, kuma hazaka ita ce ginshikin kirkira. A zamanin yau, fannoni masu tasowa musamman na fasahar zamani kamar kirkirarriyar basira (AI) da sauransu suna bunkasa, kuma akwai bukatu na matukar gaggawa ga sabbin hazaka. Hakan ya sanya kasar Sin ta maida hankali kan raya hazaka tun wuri-wuri, da kara zuba jari a fannin ilimi, da dasa iri na kirkire-kirkire don ya tsira a cikin zukatan matasa ta hanyar “zuba jari kan gina mutane”.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron tattaunawa da nazari kan ganawar da wakilan jam’iyyar CPPCC daga fannonin kimiyya, fasaha da ilimi, wanda ya fitar da kwakkwaran matakai game da hangen nesa a ranar 6 ga watan nan da muke ciki, wanda ya jaddada muhimmancin kimiyya da fasaha da ilimi da hazaka ga zamanantar da kasar Sin, inda shugaba Xi ya jaddada cewa a nan gaba, ya kamata kasar Sin ta rungumi wani yanayi mai haske, inda za a samu masu kwazo da hazaka masu dimbin yawa, ta yadda kowa da kowa zai baje kolin basirarsa kuma a yi amfani da su yadda ya kamata. Har ila yau, a cikin rahoton aikin gwamnati na bana, an gabatar da sabbin dabarun “zuba jari kan gina mutane” a karon farko, wanda kamar fitila, ya haskaka muhimmin alkibla ga ci gaban kasar Sin a nan gaba. Sanin kowa ne cewa, a cikin ’yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin a dukkan matakai ta samu sakamako mai ban mamaki a fannonin zuba jari na zahiri wadanda suka shafi ababen more rayuwa, da kawo sabbin salon gudanar da harkokin birane da kauyuka. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana
A gun taron manema labarai na musamman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Talata, jami’ai masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, yayin da manufofi da matakai daban daban na fadada kashe kudi ke ci gaba da yin tasiri a bana, kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin baki daya, sun ci gaba da nuna yanayin bunkasa bisa daidaito.
Jami’an sun kuma ce ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta inganta ayyuka na musamman don bunkasa kashe kudi, da gudanar da ayyuka a fannoni hudu, wato inganta yadda ake amfani da kayayyaki, da fadada amfani da hidimomi, da samar da gajiya daga sabbin kayayyaki, da kuma kirkirar sabbin yanayin cimma gajiya.
Ma’aikatar kasuwancin ta kuma bayyana cewa, za ta karfafa bincike kan manufofin da suka shafi amfani da fasahohin zamani, da kuma inganta ci gaba da amfani da kayayyakin dijital. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp