Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kano, Sun Sace Mutum Ɗaya
Published: 10th, March 2025 GMT
Wasu ‘yan bindiga sun farmaki gidan Alhaji Yusha’u Ma’aruf, mamallakin wani asibiti mai zaman kansa, a garin Zakirai da ke ƙaramar hukumar Gabasawa a jihar Kano, inda suka sace wani matashi mai shekaru 20 tare da jikkata ɗan uwansa.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan uku ɗauke da bindigogi da adduna sun afka wa gidan da misalin ƙarfe 2:15 na dare, suka sare yatsan hannun Abubakar Yusha’u mai shekaru 23 sannan suka sace ɗan uwansa, Mohammed Bello Yusha’u.
Daily Trust ta ruwaito cewa, sun kwashe wayoyi da kuɗaɗe kafin su tsere.
Tinubu Ya Buƙaci A Mayar Wa BUK Filin Rimin Zakara Da Ake Taƙaddama A Kai Ɗan Uwan Gwamnan Kano Da Malaman NNPP Sun Koma APCKakakin rundunar ‘yansandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun fara bincike don ceto wanda aka sace da kuma kamo waɗanda suka aikata harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Zikirai
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda
Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta.
Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran karya na iya tayar da hankalin jama’a da haddasa tashin hankali ba tare da dalili ba.
Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya RasuRundunar ta kuma shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan wajen yaɗa bayanan da ba su tabbata ba, tare da samar da sahihan hanyoyin samun bayanai idan wani abu ya taso. Ta ce kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya shi ne babban aikin da rundunar ta sa a gaba.
ADVERTISEMENTA ƙarshe, rundunar ta buƙaci mazauna Abuja da su riƙa kai rahoton duk wani abin da suka ga ya saɓa wa tsaro ga ofishin ƴansanda mafi kusa, ko kuma su tuntuɓi shalƙwatar rundunar ta hanyar layukan gaggawa: 08032003913 da 08068587311 domin samun kulawa cikin gaggawa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA