Tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa na fuskantar zargin zamba
Published: 9th, March 2025 GMT
Wata kotu a Birnin Paris na Ƙasar Faransa, ta samu tsohon shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Faransa, Bernard Squarcini, da laifin zamba da amfani da dukiyar jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
Squarcini, mai shekaru 69, ya jagoranci hukumar tsaron cikin gida ta Faransa daga 2008 zuwa 2012.
Makahon da ke sana’ar POS Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — RahotoBayan ya bar aiki, kamfanin LVMH ya ɗauke shi aiki a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin tsaro.
A ranar Juma’a da ta gabata, kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari, inda biyu daga ciki aka dakatar da su.
An same shi da laifin amfani da abokan tsaronsa don cimma burinsa, har da samun bayanan sirri na kamfanin LVMH.
Za a ba Squarcini damar yin zaman gidansa, amma sanye da munduwa ta lantarki.
Haka kuma, an ci shi tarar Yuro 200,000 tare da dakatar da shi daga duk wani aiki da ya shafi leƙen asiri ko bayar da shawara na tsawon shekaru biyar.
Lauyoyinsa sun ce za su ɗaukaka kara kan hukuncin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Faransa Tsohon Shugaban Tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars Ta Dakatar Da Babban Kocinta Bisa Rashin Katabus A Kakar Wasa Ta NPFL
Hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta sanar da dakatar da Mai Ba da Shawara a harkokin koyarwa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Koci, Ahmed Garba (Yaro Yaro), saboda rashin gamsasshen sakamako da ƙungiyar ke samu a farkon kakar wasa ta 2025/2026 Nigeria Premier Football League (NPFL).
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne sakamakon jerin sakamakon wasanni marasa kyau da suka gaza cika tsammanin masoya da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar.
Ya yanzu dai, kungiyar ta Sai Masu Gida ta buga wasanni takwas, inda ta samu nasara a biyu kacal, ta kuma tashi kunnen doki a wasanni 2, sannan suka sha kaye a wasanni huɗu — sakamakon da ƙungiyar ta bayyana a matsayin abin da bai dace da ƙungiya mai irin wannan matsayi ba.
A halin da ake, tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, zai jagoranci harkokin koyarwa tare da kocin masu tsaron raga, Suleiman Shuaibu, yayin da Coach Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai shiga cikin tawagar masu koyarwa ta wucin gadi har sai an bayar da umarni na gaba.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta ta sake gina ƙungiyar domin samun sakamako mafi kyau da kuma ci gaba da kare martabar ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Daga Khadijah Aliyu