An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden
Published: 30th, January 2025 GMT
An harbe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani, Salwan Momika, ɗan asalin ƙasar Iraƙi mai shekaru 38, a gidansa da ke Södertälje, kusa da birnin Stockholm a Sweden.
A harbe shi lokacin da yake ƙoƙarin wallafa bidiyo a kafar TikTok.
Sarkin yaƙin Zazzau ya rasu ana tsaka da taro Hisbah ta kama masoya kan yin aure ba tare da amincewar iyayensu baSalwan Momika, ya ƙone Al-Ƙur’ani a 2023 a wajen Babban Masallacin Birnin Stockholm, lamarin da ya jawo cece-ku-ce da zanga-zanga a ƙasashen Musulmi.
Lamarin ya haifar da rikicin diflomasiyya, ciki har da kai hari ofishin jakadancin Sweden da ke Bagdad, da kuma korar jakadan Sweden da ke Iraƙi.
A halin yanzu, ’yan sanda sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan, kuma suna ci gaba da bincike don gano musabbabin harin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Al Ƙurani Salwan Momika
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp