2025-06-16@10:35:24 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1020
«a Majalisar Wakilai»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Majalisar Wakilai za ta gabatar da kudurori guda biyar da za su magance manyan kalubale da ke hana ingantaccen aiki a harkar man fetur ta kasa. Shugaban kwamitin Majalisar kan Albarkatun Man Fetur, Alhaji Alhassan Ado Doguwa, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na hadin gwiwa da kwamitin musamman kan matsalar satar danyen mai a Abuja. Alhaji Alhassan Ado Doguwa ya ce kudurorin da ake shirin gabatarwa, za a gabatar da su ne tare da shugabannin kwamitocin biyu, kuma wani bangare ne na matakan dokoki don tallafawa kokarin gwamnati wajen kare kadarorin man fetur da gas da kuma dakile matsalar satar danyen mai. Ya bayyana cewa daya daga cikin kudurorin na neman kafa Hukumar Kasa da za ta sami...
Sakataren harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwaryar Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makonni Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa: Gwamnatin rikon kwarya a Siriya na iya rugujewa cikin ‘yan makwanni, lamarin da zai sa kasar ta fada cikin yakin basasa matukar Amurka ba ta ba ta hadin kai ba. A yayin zaman Majalisar Dattijan Amurka, Sakataren harkokin wajen kasar Rubio ya yi furuci da cewa: Idan Amurka ta yi aiki da gwamnatin Siriya, yana iya yiwuwa, gwamnatin ta samu nasara, ko kuma gwamnatin ta kasa samun nasara idan Amureka ba yi aiki da ita ba, kuma tabbas ba zata taba samu nasara ba. Ya kara da cewa: “A hasashen Amurka, idan aka yi...

Babban Muftin Oman Ya Yi Suka Kan Taron Kungiyar Larabawa Saboda Rashin Saboda Rashin Ba Wa Gaza Muhimmanci
Babban Mufti na kasar Oman ya bayyana cewa: Matakin taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ya fi kankara sanyi da rashin muhimmanci Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya jaddada yabonsa ga fitaccen matsayi na kasar Yemen da kuma matsin lamba da dakarun kasar Yemen suke yi na kai kayan agaji a zirin Gaza. A gefe guda kuma, ya nuna rashin jin dadinsa da raunin kudirin taron kasashen Larabawa kan daukan matakan matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar Falasdinu. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, Al-Khalili ya bayyana godiyarsa ga jaruman kasar Yemen da kuma kasashen da suka bayar da gudumawa wajen matsin lamba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mahaifinta, Everistus Nnadozie, ya ce an sanar da shi cewa surukinsa Esosa Imasuen ne ya yi wa ‘yarsa duka har ta samu raunika sosai. Ya ƙara da cewa an kai ta asibiti inda likita ya tabbatar da cewa tana fama da zubar jini a cikin jikinta. Ya ce kafin ya isa asibitin, ‘yarsa ta rasu. Bayan haka kuma, Esosa ya ɗauki gawarta ya kai wani waje ba tare da ya sanar da iyayenta ba. “Na je gidansa, sai aka ce ya tsere,” in ji mahaifin. Ya ce yana ta kiran Esosa domin ya nuna masa inda aka kai gawar ‘yarsa, amma ya ƙi amsa waya. Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Edo, ya ce sun duba wurare da dama...
Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta sanar da dakatar da duk wani nau’in tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai, a kan titi ko amfani da lasifika. Wannan na cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, wadda Jami’in Yaɗa Labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya raba wa manema labarai. ’Yan sanda sun cafke ’yan fashi 6, sun ƙwato motocin sata 4 a Kano Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Shugaban hukumar ya ce wannan matakin na da nufin kare martabar masana’antar fina-finai da kuma tabbatar da cewa duk wani bayani da ke zuwa ga jama’a ya bi ƙa’idoji da doka. “Yawancin tallace-tallacen maganin gargajiya da ake...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda yake mayarwa da Amurka martani ya bayyana cewa: Ya kamata su daina yin Magana maras ma’ana, fadin cewa Iran ba ta da izinin tace sanadarin Uranium, ganganci ne,domin jamhuriyar musulunci ba ta da bukatar izinin wani mahaluki.” Jagoran juyin musuluncin na Iran wanda ya gana da iyalan shahid Ra’isi da sauran shahidan hidima, da safiyar yau Talata, ya kara da cewa: Manufar girmama shahidai da kuma jinjinawa ayyukan da su ka yi, shi ne daukar darussa daga rayuwarsu. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Abinda ake fada dangane da shahid Ra’isi shi ne cewa ya kasance mai dukkanin siffofin jami’in da yake wakiltar hukumar da ta ginu...
Cikakkue bayanai daga baya… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Talata shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar bude dandalin hadin gwiwa na Shanghai ko SCO na 2025, game da rage talauci da wanzar da ci gaba, wanda ke gudana a birnin Xi’an, na lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin. Cikin sakon na sa shugaba Xi ya bayyana cewa, rage talauci wanda batu ne da ya shafi duniya baki daya, buri ne na daukacin kasashen duniya. Ya ce duk da cewa aiki ne mai matukar wahala, amma duk da haka kasar Sin ta cimma nasarar rage shi daidai da ajandar samar da ci gaba mai dorewa ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, shekaru 10 gabanin wa’adin karshe na ajandar. Hakan ya shaida ingancin...
Wani harin kwanton bauna da rundunar sojin al-Qassam suka kai kan sojojin mamayar Isra’ila a Beit Lahiya ya yi sanadiyar halaka tare da jikkatan sojojin mamaya masu yawa Rundunar Izzuddeen al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta sanar da cewa: Mayakanta sun kai wani kazamin harin kwantan bauna a yankin al-Atatra da ke yammacin Beit Lahiya a arewacin zirin Gaza, inda suka yi nasarar ritsawa da sojojin mamaya masu yawa da suka yi sanadaiyyar halakar wasu daga cikinsu bayan jikkata wasu da dama. Rundunar ta Al-Qassam ta ce: Mayakanta sun kai hari kan motocin sojin mamayar Isra’ila uku da bama-baman Shawaz guda biyu da kuma makami mai linzami, sannan kuma suka yi arangama da wata rundunar mamayar Isra’ila....
Wasu shugabannin kasashen Yamma suna barazana ga gwamnatin mamayar Isra’ila kan daukan matakan ladabtarwa kanta Shugabannin kasashen Faransa da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila da su dakatar da kai farmakin da suke kai wa Zirin Gaza tare da yin barazanar daukar matakin hukunta Isra’ila. Wannan bayani dai ya samu karbuwa daga fadar shugabancin hukumar cin kwarya-kwaryan gashin kan Falasdinawa da kungiyar Hamas, amma fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shi. Wannan dai ya zo daidai da gargadin da kasashen duniya suka yi na fuskantar bala’in jin kai da ke kara tabarbarewa a Gaza sakamakon killace yankin da bullar masifar yunwa...
Gwamnatin kasar Masar na shirin yin arangama ta soji da haramtacciyar kasar Isra’ila Kafofin yada labaran Isra’ila, musamman tashar talabijin ta 14, sun watsa wani rahoto cewa: Gwamnatin kasar Masar na kokarin karfafa karfinta na soji a tsibirin Sinai, tana mai gargadin abin da ta bayyana a matsayin “yiwuwar rugujewar yarjejeniyar zaman lafiya” da aka rattaba hannu tsakanin kasashen biyu a shekara ta 1979. Tashar talabijin ta NAN ta nakalto Eliyahu Dekel, tsohon shugaban hukumar leken asirin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma masani kan al’amuran Masar na cewa: Masar na cikin gaggawar shirin tunkarar rikicin soji, yana mai cewa “yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla tsakanin kasashen biyu a shekarar 1979 ta kasance cikin yanayi na rugujewa tun lokacin da...

Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama
Kwanan baya, yayin taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawar Sin da CELAC, shugaban kasar Colombia, Gustavo Petro ya ziyarci kasar Sin, inda kuma ya zanta da kafar CMG a shirin “Hira da shugabanni”. Yayin tattaunawar, shugaba Petro ya ce ya sha ziyartar kasar Sin cikin shekaru 20 da suka gabata. Ya kuma yi imanin cewa, ayyukan kasar Sin sun nuna wani sabon salo na ci gaban zamantakewar al’ummar bil’adama. Ya ce kasar Sin ta samu gagarumar nasara a fannin raya tattalin arziki da kawar da talauci, daruruwan miliyoyin mutane sun tsira daga kangin talauci, kuma sha’anin kawar da talauci a duniya ya samu gagarumin ci gaba. Shugaba Petro ya kara da cewa, wadannan nasarori ba a iya raba...
An shirya sake zama a ranar Alhamis mai zuwa don kammala tattaunawar gaba ɗaya. Cikin waɗanda suka halarci ganawar har da wakilan MOPPAN kamar su Abdul Amart, Nazifi Asnanic, da Abubakar Bashir Maishadda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an Sashen Binciken Laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Nasarawa (SCID) sun kama wani mai garkuwa da mutane a Kasuwar Shinge da ke Lafia, bisa rahotonnin sirri da suka samu. An samu nasarar cafke wanda ake zargin bayan shafe dogon lokaci rundunar na nemasa ruwa a jallo saboda laifuka da dama da suka hada da garkuwa da mutane da kuma satar shanu. A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sannan ya jagoranci jami’an tsaro zuwa maboyarsa da ke kauyen Ruwan Baka a karamar hukumar Doma, inda aka samu bindiga kirar AK-49 mai lamba 453144 tare da alburusai. Wannan nasarar ta biyo bayan kama wata Fatima Salisu a ‘yan kwanakin baya, wadda aka tare tana jigilar makamai daga...
Wadanda ake tuhumar dai, a cewar rahoton farko, sun yi wa mamacin dukan tsiya har sai da ya suma, inda aka garzaya da shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Hong inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa. Dukkan wadanda ake tuhumar dai sun ki amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen. Kotun da ke karkashin Alkali Uwani Danladi, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a gidan gyaran hali don bai wa ‘yansanda damar kammala bincike tun da har yanzu akwai sauran mutum daya da ake tuhuma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Gwamnatin HKI ta bude kofofin shigar kayakin Agaji zuwa cikin zirin Gaza bayan takurawan kasashen duniya daga ciki har da kawayen ta kan cewa ba zasu iya ci gaba da ganin Falasdinawa suna mutuwa saboda da yunwa ba. Tashar talabijin ta Almayadeen ta nakalto wata majiyar jami’an gwamnatin HKI na fada a yau litinin kan cewa zasu fara barin kayakin agaji su shiga zirin Gaza daga yau zuwa shawarar da zasu dauka nan gaba. Labarin ya kara da cewa a safiyar yau litinin tawagar motoci dauke da kayakin abinci da magungun sun shiga zirin gaza ta kofar Karim Abusaleh, sannan MDD zata kula da shigowar kayakin agaji zuwa zirin na Gaza, a fadin tashar radiyo ta sojojin HKI. Wasu majiyoyin...
Kyaftin din kungiyar, Achu Gabriel, ya yabawa takwarorinsa da suka nuna kwazo, inda ya kara da cewa tawagar za ta ci gaba da mai da hankali wajen kwato kofin da ta lashe a shekarar 2018, tawagar ta Abuja za ta kara da mai masaukin baki, jihar Ogun a wasan rukuni na biyu a ranar Talata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya aika ta’aziyya ga iyalan mutane 37 da hatsarin kwale-kwalen Gbajibo ya rutsa da su daga jihar Neja a karshen mako. A cikin sanarwar gwamna AbdulRazaq ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Neja kan wannan lamari mai ban tausayi. Gwamnan ya bukaci ma’aikatan jirgin da fasinjoji da su bi ka’idojin tsaro domin amfanin kowa. Ya bayyana a matsayin al’ada mai raɗaɗi kuma ba za a yarda da ita ta rashin amfani da na’urorin kariya da gwamnati ta bayar akai-akai. Yana rokon Allah ya jikan wadanda aka kashe. REL/ALI MUHAMMAD RABIU
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango 22 sakamakon zarginsu da saɓa ƙa’idar hukumar. Cikin wata sanarwa da jami’in hul da jama’a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ya ce shugaban hukumar Abba Al-Mustapha ne bayar da umarcin saboda a cewarsa masu shirya fina-finan sun saɓa ƙa’idojin hukumar waɗanda suka tanadi cewa dole ne hukumar ta tace su kafin fitar da su. Wasu daga cikin fina-finan da dakatarwa ta shafa sun haɗa da Dadin Kowa Labarina Gidan Sarauta Manyan Mata Dakin Amarya Kishiyata Garwashi Jamilun Jiddan Mashahuri Wasiyya Tawakkaltu Mijina Wani Zamani Mallaka Kudin Ruwa Boka Ko Malam Wayasan Gobe Rana Dubu Fatake Shahadar Nabila Tabarmar Rigar Aro An umurci...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Kasarsa Ta Jajirce Kan Harkokin Diflomasiyya Domin Kare Hakkokinta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Iran ta jajirce kan harkokin diflomasiyya kuma tana neman yarjejeniya ta gaskiya Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada kudurin kasar Iran kan harkokin diflomasiyya da kuma cimma daidaito bisa tsarin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, tare da cikakken mutunta hakkin nukiliyar kasar Iran, da kuma tabbatar da manufar dage takunkuman da aka sanya mata. Wannan dai ya zo ne a cikin jawabin da Araqchi ya gabatar a ranar Lahadin da ta gabata a wajen taron tattaunawa na birnin Tehran, wanda cibiyar nazarin harkokin siyasa da kasa da kasa ta ma’aikatar harkokin wajen kasar ta dauki nauyin shiryawa, tare da halartar tawagogi 200 na manyan jami’ai daga kasashe 53 da...
Iran ta yi watsi da zarge-zargen taron kasashen Larabawa game da tsibirai uku na Tekun Fasha Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da zarge-zargen da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kasashen Larabawa a Bagadaza dangane da tsibiran Iran guda uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa. Isma’il Baqa’i ya tabbatar a jiya Litinin 19 ga watan Mayu cewa: Tsibiran nan uku na Babban Tunb, Karamin Tunb da Abu Musa wasu bangarori ne na kasar Iran, yana mai cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ganin duk wani da’awar a wannan fanni ya sabawa ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa, da kuma keta mutuncin yankunan kasa da ka’idojin...
Gwamnatin jihar Kebbi ta jajanta wa al’ummar Waje da ke karamar hukumar Danko Wasagu sakamakon harin ‘yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar manoma 15 tare da jikkata wasu 3. Mataimakin gwamnan jihar, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya mika sakon ta’aziyyar gwamnati tare da bayar da tallafin Naira miliyan 24 ga iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata. Ya bayyana hakan a matsayin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a wannan lokaci mai cike da kalubale. Sanata Abubakar, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta dauki matakan da suka dace don magance matsalar rashin tsaro, tare da baiwa manoma damar gudanar da ayyukansu cikin...

Wata ‘Yar Jarida Ta Nuna Mamaki Kan Nuna Damuwa Da Ciwon Biden Maimakon Kisan Gillar ‘Yan Sahayoniyya
A lokacin da kasashen Yamma suka yi biris da kisan gillar da ake yi a Gaza, kuma suna kuka kan cutar da tsohon shugaban Amurka Biden ke fama ita Marubuciya kuma ‘yar jarida kasar Autraliya Caitlin Jahnstone a cikin wani makala da ta rubuta ta siffanta abin da ta kira matsayin munafuncin ƙasashen yamma wajen mu’amala da kimar ɗan adamtaka da gwada alhini kan batun ciwon tsohon shugaban Amurka Joe Biden game da cutar sankara da ke fama da ita a matsayin mafarin fallasa sabanin da ke cikin maganganun siyasa da kyawawan ɗabi’u na Amurka dangane da laifukan yaƙi musamman abin da ke faruwa a Gaza. Tana cewa: Ciwon daji na Prostate yana da ‘yancin wanzuwa. Yayin da ciwon daji...
Allah ya yiwa fitaccen ɗan jarida kuma wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurika (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa a ranar Lahadi a Maiduguri. Marigayin, wanda ya kuma kasance tsohon shugaban ƙungiyar ‘yan jarida (Correspondents Chapel) na jihar Borno, ya rasu ne bayan doguwar jinya. Na Dauki Karramawar Jaridar LEADERSHIP Da Matukar Muhimmanci – Gwamna Abba Babu Wani Dan Jarida Da Aka Hana Shiga Taron Gwamnonin Arewa – CPS Ibrahim Musa An shirya gudanar da sallar jana’izarsa yau Litinin a ƙofar gidansa da ke unguwar State Low-Cost, Maiduguri. Abokan aiki da ‘yan uwa sun bayyana baƙin ciki game da rasuwar, suna yaba masa da halayensa na kirki da ƙwarewarsa a fannin jarida. Daga kanmu, magana ta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a? NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba. Domin sauke shirin latsa nan
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar. Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance? Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai...
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja. Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano. Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa Hatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa. Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar...
Aƙalla mutane bakwai sun mutu yayin da wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Essa da ke kan hanyar Agaie-Badeggi, ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja. Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa motar ɗauke da hatsi ta gwamnatin tarayya ce, kuma fasinjojinta maza ne kimanin 36, daga Legas zuwa Kano. Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato An Tsinci Gawarwakin Yara Biyar Cikin Tsohuwar Mota A Nasarawa Hatsarin ya faru ne da ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, lokacin da direban ya yi ƙoƙarin ƙetare wani ɓangare mara kyau na hanyar da ake ginawa. Daraktan hukumar kula da sufuri na Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar...
Shugaban karamar hukumar Kaiama, Honarabul Abdullah Danladi ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da LEADERSHIP ta wayar tarho. Danladi ya ce ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa. Ya kara da cewa, gwamnati za ta kafa wani kwamiti wanda za a dora masa alhakin tilasta wa fasinjojin jirgin ruwa yin amfani da rigar tsira don dole. Danladi ya ce gwamnati za ta kuma dakatar da tafiye-tafiye da daddare a wani bangare na matakan kawo karshen yawaitar haduran Kwale-kwale da ake fama da shi a yankunan da ke zagaye da ruwa. Shi ma mai martaba Sarkin Kaiama, Alh Muazu Omar ya nuna alhininsa kan wannan lamari da ya...
A cewarsa, baban dalilin da ya sa suke wannan aiki shi ne, domin a rage wa al’umma musamman masu karamin karfi wahalwalun da suke sha wajen neman lafiya. Malam Hussaini ya yi kira ga sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su ba da tasu gudummawa wajen irin wannan aiki ta yadda za su taimaka wa kokarin gwamanti kan harkokin kiwon lafiya. Wasu daga cikin wadanda suka amfana da wannan taimako na aikin kaba sun yaba da kokarin wannan gidauniya, inda suka ce hakan zai taimaka wa kokarin gwamanti da sauran kungiyoyi da masu hannu da shuni da su yi ko yi da wannan gidauniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Hukumar kula da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta ce masu bincike sun tabbatar da wata sabuwar halitta da aka samu a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, wanda aka yi wa lakabi da Niallia Tiangongensis A watan Mayun 2023 ne, tawagar ‘yan sama jannati ta kumbon Shenzhou-15 ta gano wani samfurin halitta a cikin tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin yayin da take cikin da’irarta. An kuma adana ta cikin yanayi mai sanyi, sannan daga bisani aka kawo ta duniyar dan Adam domin gudanar da nazari. Kuma bayan binciken kimiyya da ya shafi nazarin sauyawar yanayinta da tsarin kwayar halittarta da sauransu, masana sun tabbatar da cewa sabuwar halitta ce da ba a taba...

Jagora: Jawaban Trump A Ziyar Da Ya Kai Wasu Kasashen Larabawa Na Yankin Tekun Farisa Abin Kunya Ne Gare Shi Ga Kuma Amurkawa
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya yi watsi da wasu kalaman shugaban kasar Amurka Donal Trump a ziyar da ya kammala a wasu kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, ya kuma bayyana wasu kalamansa a matsayin kungiya ga kansa da kuma mutanen Amurka. Har’ila yau Jagoran ya kara da cewa da dama daga cikin maganganunsa basu cancanci maida martani ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a yau Asabar, a lokacinda yake ganawa da wasu malaman makaransu daga larduna daban daban na kasar, a Husainiyyar Imam Khonaini (q) a nan Tehran. Jagoran ya kara da cewa : Trump yace yana son amfani da karfin da Amurka...
A makon da ya gabata, wasu ma’aikatan hukumar ilimi ta ƙaramar hukumar Damboa guda biyu sun mutu a irin wannan hari a hanyar Damboa zuwa Maiduguri. ’Yan ta’addan Boko Haram sun dawo da amfani da bama-bamai da suke birnewa a hanya domin kai hari kan matafiya da motocin da ke amfani da manyan hanyoyin Jihar Borno, abin da ya janyo asarar rayuka da dama a baya-bayan nan. A halin yanzu kuma, dakarun sojin Nijeriya na ci gaba da kai farmaki a dazukan Sambisa da sauran maɓoyar ’yan ta’adda a faɗin jihar domin murƙushe su da kawar da su gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya jaddadacewa: Sun yi Imani da tattaunawa, amma ba su jin tsoron duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa: Tabbas Iran tana gudanar da zaman tattaunawa da Amurka amma ba ta tsoron duk wata barazanarta, yana mai nuni da kalaman Trump da ke cin karo da juna, wani lokaci yana magana kan zaman lafiya sannan a wasu lokutan yana barazana da yaki. A jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru biyu da samun nasarar tawagar “Rukunin Jirgin Ruwa na 86” na sojojin ruwan Iran, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yaba da sadaukarwar da jaruman da suka yi wannan hidimar, yana mai cewa: “Suna alfahari da kasancewar dakarunsu, yana mai...
Sai ya ce “Na riga na amsa wannan tambayar amma har yanzu kana sake maimaita ta. Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jarida 43 mazauna Kaduna ne suka halarci taron, ciki har da wasu ‘yan jarida daga wasu jihohin da suka raka gwamnonin nasu. Don haka, ba daidai ba ne a ce na hana ‘yan jarida shiga taron gwamnonin Arewa. Duk jaridun kasar nan sun je a wurin. Duk gidajen rediyo da talbijin na Kaduna suna wurin. Duk wakilan manyan gidajen Talabijin da Rediyo da ke wajen Kaduna su ma suna nan. Kada ka dauki maganata a wani bangare daban, je ka bincika. Duk wadannan labarai ne irin na teburin mai shayi. Ni kuma ban sani ba. Abin da...
Sai dai dan majalisar wakilai Ali Isah na (PDP, Gombe), bai amince da matsayin Madaki ba. Ya ce sanya shugaban kasa na a tsarin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai samar da adalci da sanin ya kamata ga dukkan shiyyoyin siyasar kasar nan. Dan majalisa Sada Soli na (APC, Katsina), yayin da yake adawa da kudurin, ya ce dokar da aka gabatar “Na da illa sosai ga hadin kan kasa.” Ya ce sanya ka’idar shugabancin karba-karba a cikin kundin tsarin mulkin kasar zai kai ga samar da abubuwa bisa cancanta. “Hakan zai iya sanya muradun yanki da na kabilanci a gaba su zamo mafi cancanta. Zai karfafin zabin mutanen da za su iya tsayawa takara kuma zai kara...
A kokarin da yake yi na jigilar maniyyatan aikin hajjin bana, Kamfanin jiragen sama na Max Air yace zai kwashe daukacin Alhazan Jihar Jigawa cikin kwanaki biyu. Mataimakin mai kula da ofishin kamfanin dake jihar kano, Mr Barnabas Anderson ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a shelkwatar hukumar Jin dadin alhazan jihar Jigawa dake Dutse babban birnin jihar. A cewarsa, ana sa fara jigilar maniyatan jihar zuwa kasar Saudi Arabia a ranar 20 da kuma 21 ga watan Mayun 2025. Ya ce jirgin Max air zai yi sawun farko da maniyata su 550 zuwa kasa mai tsarki a ranar 20 ga watan Mayu. Mr Anderson yace a ranar 21...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Katsina ta samu sahalewar Hukumar Wasanni ta Kasa domin gina Birnin Dawakai na farko a nahiyar Afirka. Wannan amincewa ta biyo bayan wata ganawa ta musammam tsakanin Gwamna Dikko Umaru Radda — wanda Daraktan Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina Dokta Kabir Ali Masanawa ya wakilta — da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa, Malam Shehu Dikko da Ministar Al’adu, Yawon Bude da kuma Tattalin Arziqin Kirkire-kirkire Barista Hannatu Musa Musawa. Gwamna Radda wanda ya bayyana cewa, gagarumin aikin Birnin Dawakan zai lakume biliyoyin Naira kuma zai kara inganta qokarin gwamnatin jihar na raya al’adun jihar tare da samar da hanyoyin tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar da arewacin Najeriya gaba daya. Sabon birnin Dawakan na...
Ma’aikatar kiwon lafiya a kasar Saudia ta kaddamarda wata manhaja don kula da lafiyan mahajjata a hajjin bana, wanda aka tarjamata zuwa harsuna 8 a duniya. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto kamfanin dillancin labaran Saudi Press Agency (SPA) na fadar haka a yau Jumma’a. Ya kuma kara da cewa harsunan da ake samun manhajar a ciki suna hada da Arabiyya, Inglishi, Faransaci, Urdu, Farisanci, Indonesia, Malay da kuma Turkanci. Manufar wannan manhajar ita ce bada shawara ga mahajjata kan yadda zasu kula da lafiyarsu a cikin wannan lokacinda Hajji na bana, wanda yake zuwa tare da zafi sosai. Da farko manhajan ya bukaci mahajjata su yi amfani da laima don rage zafin da ke fadawa a kansu....
Wakilan kafafen yada labaran, sun tattauna kan kalubalen da fannin aikin noman kasar ke fuskanta da suka hada da rashin samar ainahin bayanai kan abin da ya shafi aikin noma. Rashin bayar da ingantaccen dauki ga fannin daga bangaren gwamnati, kalubalen rashin tsaro da zabar wasu ‘yan lelen kafafen yada labarai, musaman da gwamnatin kasar ke yi, wajen bayar da tallace-tallacen da suka shafi bangaren aikin noma, inda suka yi nuni da cewa, kafafen yada labarai; sun dogara ne kacokan a kan samun tallace-tallace, wanda akasari shi ne ke rike da su. Sun kuma bukaci a samar wa da kafafen yada labaran kasar, wata hanyar sadarwa ta bai daya, musamman domin su kara wallafa rahotannin da suka shafi ayyukan gwamnatin...
Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara da karfin sojanta, kuma shi ne ya tilasta wa makiya zaman tattaunawa da ita. A ziyarar da ya kai wajen baje kolin littafai na birnin Tehran, Araqchi ya ce dangane da tattaunawa wand aba na kai tsaye ba da Amurka: Idan da a ce Amurka na da karfin lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba ta shiga tattaunawa ita ba. Araqcgi ya kara da cewa:...
Majalisar wakilai za ta binciki yadda aka samu mummunar faduwa a jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (UTME) ta 2025 da hukumar shirya jarabawar (JAMB) ta gudanar kwanan nan. Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa, Adewale Adebayo ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Da yake gabatar da kudirin, ya koka da cewa, da yawa daga cikin daliban, sun yi tafiya mai nisa domin zana jarabawar UTME a cibiyoyin jarabawar. Amma abin takaici, sai ga sakamakon ya fito da koma baya da yawa. Duk da cewa, hukumar JAMB ta amince cewa, tangardar na’ura ce ta janyo faduwar amma akwai bukatar a binciki hukumar. Idan za a iya tunawa, sakamakon jarabawar UTME na 2025 da JAMB...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da amfani da katangewar da ta yi wa Gaza a matsayin makamin kawar da wata al’umma. A wani rahoto data fitar yau Alhamis, kungiyar ta Human Rights Watch ta zargi Isra’ila da yin amfani da shingen da aka yi wa Zirin Gaza a matsayin “wani makami na share al’umma,” yayin da hukumomin Isra’ila suka hana shigar da duk wani agajin jin kai cikin yankin Falasdinu tun ranar 2 ga Maris. Katange zirin da Isra’ila ta yi ya fi karfin dabarun soji, ya kai wani yunkuri na share al’umma inji Federico Borello, darakan zatarwa mai riko na kungiyar a cikin wata sanarwa da ya caccaki shirin Isra’ila na zaunar da...
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci zauren Majalisar Wakilai a ranar Alhamis domin ganewa idanunsa ficewar wasu mambobi biyu na Jam’iyyar adawa ta NNPP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC. ’Yan majalisar biyu, sun haɗa da: Dan Majalisar Wakilai, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar mazaɓar Rogo/Karaye da kuma Ɗan Majalisar Wakilai Kabiru Alhassan Rurum mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Rano/Bunkure/Kibiya, sun sauya sheƙa a ranar Alhamis. Sabon Hari: An kashe makiyayi da shanu sama da 100 a Filato Dalilin da ya sa gwamna Bala ya yi ƙoƙarin mari na – In ji Minista Hakazalika mamba mai wakiltar mazaɓar Ijesha Oriade/Obokun na Jihar Osun, Wole Oke, ya kuma bayyana ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC....
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da jagoran da ya kafa majalisar bunkasa cinikayya ta Denmark dake kasar Sin ya aike masa, yana mai karfafa gwiwar cibiyar da kamfanoni mambobinta, da su samar da sabbin gudummawar raya alakar Sin da Denmark, da kawancen Sin da Turai, kana su zurfafa hadin gwiwa na cimma moriyar juna tsakanin sassan. Shugaba Xi ya kuma bayyana fatan cibiyar da kamfanoni mambobinta za su ci gaba da taka rawar gani, wajen karfafa cudanya tsakanin Sin da Denmark da ma tsakanin Sin da Turai baki daya, kana su ba da gudummawa wajen bunkasa fahimtar juna da abota, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriyar juna tsakanin sassan. A baya bayan nan, a matsayinsa, da kuma...
Rundunar ta ce ta gudanar da aikin bisa ƙa’ida da bin doka, kuma tana Allah-wadai da masu yaɗa ƙarya da nufin ɓata mata suna. Ƴansandan sun jaddada cewa za su ci gaba da aikinsu na yaƙi da laifi da bin doka da ƙwarewa a duk faɗin ƙasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Hukumar Makamin Nukliya Ta Kasar Iran Yace, Kasarsa Bata Buye Wani Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
Shugaban hukumar Makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Eslami ya bayyana cewa kasarsa bata boye wani wuri inda take sarrafa makamashin Nukliya wanda bata fadawa hukumar IAEA ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Islami yana fadar haka a jiya Laraba, kuma don kare matsayin Iran na mallakar fasahar nukliya ta zama lafiya, wanda kasashen yamma suke zarginta da kokarin kere makaman nukliya. Shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ya bayyana haka ne a gefen taro Makamashin Nukliya na kasar Iran karo na 31 wanda aka gudanar a nan birnin Tehran, ya kuma kara da cewa babu wata cibiyar sarrafa makamashin nukliya wanda Iran ta boyewa hukumar IAEA a da ko yanzu. Kuma da akwai...

Wata Kotu A Amurka Ta Bukaci A Saki Wani Malami Mai Goyon Bayan Palasdinawa A Jami’ar Georgetown academic
A wata koma baya ga shirin gwamnatin Trump na dirar mikiya a kan Amurkawa magoya bayan Falasdinawa a Jami’o’iin Amurka, wata kotu ta kare hakkin bil\adama ya yanke hukuncin sallamar Dr. Khan Suri malami a Jami’ar Georgetown ta Amurka wanda jami’an tsaro na shige-da fice suka kama a cikin makonnin da suka gabata saboda jawabin da yayi a taron gangami na goyon bayan Falasdinawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kotun ta gwamnatin tarayya ta bukaci jami’an custom da kuma shige da fice na AMurka (ICE) suka sake Dr Khan Suri daga inda suke tsare da shi makonni 8 da suka gabata, ya koma Texas inda yake zama tare da iyalansa, daga Viginia inda ake tsare da...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da zargin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayiwa JMI a lokacinda yake ziyarar aiki a birnin Riyar na kasar Saudiya a ranar talatan da ta gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Laraba ta kuma kara da cewa zargin da shugaba Trump yakewa JMI na kokarin wargaza tsarin zamantakewa a yankin Asiya da yamma ba gaskiya bane, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurka ne suke son dagula al-amura a yankin tare da goyon baya HKI ta kashe mutanen yankin a gaza da lebanonm da kuma siriya. Inda a gaza kadai ya zuwa yanzu ta kashe Falasdinawa fiye dubu 52.
Kasar Sin ta zage damtse kan wannan aiki inda ta kuduri aniyar yin ginin tashar da kayan da aka sarrafa da albarkatun duniyar wata, tare da tabbatar da cewa suna da ingancin da za a iya dogaro da su. Wannan zai zama ta harbi tsuntsu biyu da dutse guda, na farko zai saukaka sufurin jigila da kuma kula da gyaran tashar yadda ya kamata. Babban jagoran tsara aikin binciken duniyar watan, Wu Weiren ya ce kasar Sin ita ce ta farko a duniya da ta kera injin buga tubali ko bulon gini na kasar duniyar wata ta hanyar amfani da kayan aiki da aka sarrafa daga albarkatun duniyar watan. Injin yana aiki ne ta hanyar janyo makamashin hasken rana tare...
Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da Iran Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Amurka ita ce ta kawo cikas ga ci gaban al’ummar Iran ta hanyar kakaba takunkumai, matsin lamba da kuma barazanar soji da ba na soji ba, don haka ne Amurka ke haddasa matsalolin tattalin arzikin Iran. A gefen taron majalisar ministocin a yau Laraba, Araqchi ya bayyana cewa, abin da Trump ya fada game da kasashen yankin da suke son bin hanyar samun ci gaba da wadata shi ne, a hakikanin gaskiya irin tafarkin da al’ummar Iran suka bi a lokacin juyin juya halinsu, da kuma tafarkin da suka zaba na...
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Jigawa ta naɗa Kwamared Sani Muhammad Gumel da Kwamared Usman Mohammed Usman a matsayin mambobin majalisar kungiyar na musamman (Ex-Officio). Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakatariyar ta kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed, ta sanya wa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Dutse. Ta bayyana cewa, an yi waɗannan naɗe-naɗen ne a matsayin girmamawa da yabo ga jajircewarsu, ƙwarewa, da kuma gudummawar da suke bayarwa wajen haɓaka aikin jarida a Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya. Aisha Abba Ahmed ta ƙara da cewa, duka waɗannan mutane biyu sun dade suna nuna ƙwazo da biyayya ga manufofi da burin ƙungiyar. Ta ce, ana sa ran waɗannan mambobin na...
Idris ya ce: “Wannan ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa da jarumtaka, daidaito, da jajircewa ga tsarin dimokiraɗiyya suka bayyana. “Ko da yake Alhaji Sule Lamiɗo babban jigo ne a jam’iyyar adawa kuma sau da dama mai suka ga gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu (GCFR), har yanzu yana daga cikin manyan ginshiƙai na cigaban siyasar Nijeriya.” Ministan ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya yarda da siyasar da ke bai wa kowa dama, inda ake maraba da ra’ayoyi mabanbanta, kuma suna da muhimmanci ga tattaunawa kan makomar ƙasa. “Kowane ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakar sa da jam’iyya ba, yana da gurbin zama a teburin tattaunawa kan makomar ƙasa.” Idris...
Tsohon shugaban kasar Sin marigayi Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ” Idan an dauki mataki mai karfi wajen neman zaman lafiya, to, za a samu. Amma idan an nuna sassauci a kokarin neman tabbatar da zaman lafiya, to, ba za a samu biyan bukata ba. ” Wannan tunani ya sa kasar Sin nuna ra’ayin kin amincewa da matakin kasar Amurka na karbar karin harajin fito ba tare da wasiwasi ba. Musamman ma ta la’akari da yadda kasar ba ta rasa “kati” a hannunta ba, inda karfin tattalin arzikinta, da manufar bude kofa da ta dauka, dukkansu suka kasance karfinta na tinkarar kalubale. Sai dai, idan babu “kati” a hannu, yaya za a yi? Ga shi, abu na biyu da...
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta bukaci Gwamnatin Jiha da kananan hukumomin jihar goma sha uku da su gaggauta bayar da kayayyakin tallafi ga wadanda guguwar iska ta shafa a fadin jihar. Majalisar ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin inganta rayuwar wadanda abin ya shafa da rage musu radadin halin da suke ciki. Shugaban Majalisar, Dr. Danladi Jatau, ne ya bayyana hakan bayan Hon. Hudu A Hudu ya gabatar da batun a matsayin lamari mai muhimmanci ga jama’a, yayin zaman majalisar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar. Shugaban majalisar ya ce abin jimami ne kwarai yadda guguwar iska ta lalata gidaje, makarantu, gine-gine da wasu muhimman kayayyaki da suka kai daruruwan miliyoyin Naira tare da jikkata mutane...
Rundunar “Sarayal-Kudus” ta kungiyar jihadul-Islami ta harba makamai masu linzami akan sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Asqalan” da “Ushdud”. A jiya Talata ne dai rundunar ta Sarayal-Qudus’ ta sanar da harba makamai masu linzamin kaan sansanonin ‘yan share wuri zauna, a matsayin ci gaba da mayar da martani ga hare-haren wuce gona da irin na HKI akan al’ummar Falasdinu. Sanarwar da rundunar ta fitar ta kunshi cewa: Harin nata yana a matsayin mayar da martani ne akan kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a Gaza. A wani labarin na daban, rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas ta sanar da cewa ta yi taho-mu-gama da sojojin mamaya a unguwar “Shuja’iyya” dake gabashin birnin Gaza. Sojojin HKI suna ci...
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta amince da dokar kafa doka da za ta samar da tsari da kula da bada izinin filaye da yarjejeniyoyin al’umma ga masu hakar ma’adanai da sauran batutuwan da suka shafi hakan. Shugaban Majalisar Dokta Danladi Jatau, ya sanar da amincewa da kudirin a zaman majalisar a Lafiya. Shugaban majalisar ya ce kudirin dokar idan Gwamna Abdullahi Sule ya amince da shi zai magance kalubalen hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar. Shugaban majalisar ya ce sashe na uku na kudirin ya ba da umarnin kafa Asusun Raya Al’umma na CDF don inganta walwalar al’ummomin da ke hakar ma’adanai ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da ayyukan jin kai. “Kamfanonin...
A yanzu haka ana zargin wasu dakarun sojin sun ɓace tun bayan kai harin na ranar Litinin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
A cikin binciken jin ra’ayoyin, kashi 91 cikin 100 na masu bayyana ra’ayoyi, sun yi imanin cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga rayuwar Amurkawa. An wallafa sakamakon binciken a dandalolin CGTN a cikin harsuna biyar da suka hada da Ingilishi, Sifaniyanci, Faransanci, Larabci, da Rashanci. A tsakanin sa’o’i 24 da kaddamar da binciken, masu amfani da intanet fiye da 12,000 ne suka shiga cikin binciken tare da bayyana ra’ayoyinsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
Babu wata ’yantacciyar kasa da za ta hakura da muradunta domin wata ta biya bukatunta na son rai. Yayin da Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kasashe haraje-harajen kwastam na babu gaira ba dalili, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kin amincewa da salon cin zali, inda ta sha nanata cewa, sai ta ga abun da ya ture wa buzu nadi, a yakin cinikayya da Amurkar ta tayar. Lallai tsayuwar kasar Sin ya ba kasashe masu tasowa kwarin gwiwa, kuma ya nuna cewa, lokaci ya wuce da za a rika yi wa ’yantattun kasashe danniya da cin zali domin biyan bukatu na kashin kai. Hakika kasar Sin ta gina tubali mai karfi da ta dora tattalin arzikinta a...

Hadin Kai Da Cin Moriya Tare Ne Hanya Mafi Dacewa Wajen Daidaita Matsalar Dake Tsakanin Sin Da Amurka
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga gwamnatin HKI kan hare-haren da ta kaiwa wani sansanin yan gudun hijira a gaza inda ta kashe ko takai mutanen da dama ga shahada, daga ciki har da mata da yara jarirai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei yana fadar haka a jiya Litinin, a jawabinda ta saba gabatarwa a ko wace litinin. Esmaeil Baghaei ya kara da cewa nauyin MDD ce ta dakatar da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza, kuma kasa yin haka wani abin kunya ne ga majalisar. Ya kuma kara da cewa ya zama wajini kutunan kasa da kasa wadanda suka hada da ICJ ta...
Wannan rangwamen farashin duk da cewa ba a hukumance yake ba, amma ya bai wa kwastomomin Dangote damar siyar da mai akan farashi mai rahusa a tsakanin Naira 830 zuwa N835 kan kowacce lita. Wannan nasarar ta zo ne makonni kadan bayan da matatar ta yi ragin farashi sau biyu a jere a cikin mako guda a cikin watan Afrilu, inda ta rage farashin man ta daga N880 zuwa N835 kan kowace lita. Ana kyautata zaton cewa, ragin na da nasaba da sabunta tsarin sayen danyen mai da takardar Naira, biyo bayan dakatarwar da aka yi na wucin gadi. Kokarin samun wata sanarwa a hukumance daga Kakakin Rukunin Dangote, Anthony Chiejina, kan batun rangwamen ya ci tura...
Sojojin HKI sun ci gaba da kai hare hare kan birane da garuruwan yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, hare-haren jiya sum sun fi maida hankali ne a garin Tulkaram da kuma sansanin yan gudun hijirar yankin A wannan karomma sojojin HKI sun bada umurni ga ma zauna garin Tullaram mata da maza da yara da tsoffi duk su fice daga gidajensu. Kwanaki 105 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta fara wannan shirin na korar falasdinwa da kuma rusa gidajensu da nufin korarsu kwatakwata daga yankin. MDD ta bayyana a baya ya zuwa yanzu sun kori falasdinawa kimani 40,000 daga gidajensu, inda suka rusa su suka kuma . A wani...
“Babu shakka cewa INEC na fuskantar matsin lamba mai tsanani, daga mambobin APC da sauran abokan huldarsu wadanda ke tsoron TNN, domin sun shirya yin magudi a zaben 2027 wajen samun nasararsu. “Amma muna kira ga INEC da ka da ta bayar da kai bori ya hau a matsayinta na hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa tare da kare mutuncnta ta hanyar kin yin abin da ya saba wa doka. “Muna tunatar da hukumar INEC cewa ‘yan Nijeriya suna sa ido sosai kan yadda za ta magance wannan batun na TNN, kuma duk abin da za ta yi zai tantance ko ‘yan Nijeriya za su iya dogaro da ita don shirya sahihin zabbe mai cike da adalci a 2027,”...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana fatan ganin kasashen India da Pakistan sun kai zuciya nesa, tare da warware sabani ta hanyar shawarwari da tattaunawa, kana su gujewa sake rura wutar tashin hankali. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Asabar, yayin tattaunawa ta wayar tarho da mashawarcin gwamnatin India ta fuskar tsaro Ajit Doval, inda ya ce Sin na goyon baya, da fatan sassan biyu za su kai ga cimma cikakken yanayi mai dorewa na dakatar da bude wuta ta hanyar tattaunawa, wanda hakan muhimmiyar moriya ce ta kasashen biyu, kuma zai cika burin sassan kasa da kasa. Ya ce Sin ta yi tir da harin ta’addanci da ya auku a yankin Pahalgam, tana kuma adawa...
Wasa na uku da kungiyoyin suka hadu a bana shi ne wasan karshe na kofin Copa Del Rey inda nan na Barcelona ta sake samun nasarar doke Madrid da ci 3-2, a wannan karon kocin Madrid Carlo Ancelotti na fatan ganin kungiyarsa ta samu nasara akan Barcelona duba da cewar wannan ka iya zama wasan karshe da ita a matsayinsa na kocin Real Madrid. Manyan yan wasan da bazasu buga wannan wasa sakamakon raunin da suka samu sun hada da Joules Kounde da Pablo Torre a bangaren Barcelona, sai kuma Antonio Rudiger, Eduordo Camavinga da Ferlnad Mendy a bangaren Real Madrid. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Miliyoyin mutane, mafi yawansu mabiya mazhabar iyalan gidan manzon All..(s) sun taru a hubbaren limami na 8 daga limamai masu tsarki wasiyan manzon All..(s)..12. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, miliyoyin mutanen kasar Iran da kuma wasu bakin da suka zo daga kasashen waje sun yi cincirindo a hubbaren Imam Aliyu dan Musa Al-rida(a) limamai na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Alll..(s) da ke birnin Mashad na arewa maso gabacin kasar Iran don tunawa da ranar haihuwarsa. An kawata hubbaren na sa da fulawowi wasu na lantarki sannan malamai suna bayyana matsayinsa a wajen raya addinin kakakinsa manzon All..(s), musamman a lokacinda sarki Mamun daga cikin sarakunan Abbasiyawa ya tilasta masa...
Manistan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Saudiya Faisal Bin Farhan a birnin Jeddah inda bangarorin biyu suka tattauna kan al-amuran da suka shafi yankin, musamman batun Falasdinawa da kuma halin da suke ciki musamman a yankin gaza. Inda HKI take kashesu da yuwan, sannan tana ci gaba da rusa gidajensu a yankin yamma da kogin Jordan. Har’ila yau, kasashen biyu a matsayin manya-manyan kasashen a yankin yammacin Asiya sun yi kokarin kyautata dangantaka a tsakaninsu. Kuma Aragchi ya je kasar ta saudiya ne don kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma zurgaga al-adu da al-amura da suka hada kasashen biyu daga ciki har da kasancewarsu kasashe musulmi. A wani bangare Aragchi ya fadawa...
Amma sha’awar taka leda a Real tare da babban abokinsa kuma abokin wasansa na Ingila Jude Bellingham ya sa shi canza ra’ayi, yunkurin da Alexander-Arnold ya yi zuwa Real Madrid ya raba kan magoya bayan Liverpool, inda wasu ke ganin ya kamata ya zauna ya zama gwarzon kulob daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Dole ne duniya ta dauki matakin kalubalantar laifukan ‘yan sahayoniyya da magoya bayansu kan zaluncin Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake karbar bakwancin dimbin ma’aikata a yau Asabar, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan “Makon ayyuyka da Ma’aikata” ya bayyana cewa: A yau duniya ta shaida yadda ake daukar manufofin son zuciya kan wasu kasashe. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa daga cikin wadannan manufofi na son zuciya da ake aiwatarwa a yau akwai kokarin mantar da al’umma batun da suka shafi Falasdinawa, yana mai cewa: Kada al’ummar musulmi su kuskura wannan kyale hakan ya faru, domin ko dan...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Allah Wadai Da Kai Hari Kan Ofishin Jakadancin Kasarsa A Kasar Sweden
Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi Allah wadai da harin da aka kai kan ginin ofishin jakadancin kasarsa da ke Stockholm na kasar sweden Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancin Iran da ke Stockholm tare da yin kira ga gwamnatin Sweden da ta dauki mataki mai tsanani kan wadanda suka kai harin. A yayin wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da ministar harkokin wajen Sweden Maria Malmer Stenergård, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma na ofishin jakadancin. A yayin tattaunawar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin...
Shugaban kungiyar ya yi magana Ibrahim Yusuf Babayo,Shugaban kungiyar Miyetti Allah masu kiwon dabbobi na kasa ya bayyanawa jaridar karshen mako cewar dukkan hare- haren da ake kaiwa dabbobin da kuma kashesu an sanar da jami’an tsaro daban- daban,da suka hada da Kwamanda na rundunar soja ta,3 kuma kwamandan Operation Safe Haben (OPSH), Manjo- Janar Foluaho Oyinlola,Kwamishinan‘yansanda na Jihar, Emmanuel Adesina,da kuma darekta na bangaren jami’an farin kaya DSS. Ya ce jami’an tsaro da suke a bangaren Karamar Hukuma an kai su can wuraren da aka kai hare- haren domin su ganewa idanunsu yadda lamarin yake. Sa Wa Shanu 110 guba Kamar yadda jagorancin kungiyar MACBAN a Jihar yace,an kashe Shanu a kalla 110 ta hanyar guba a hare- haren...

ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
Na yi wannan wannan ziyara ne saboda shaukin da nike da shi a kan abin da ya shafi kishin kasata Nijeriya, da kuma neman hadin kan kasashen Afirika ta yamma mu zama tsintsiya madaurinki daya,da son zaman lafiya da ci gaban Dimokaradiyya. Kazalika, na yi wannan rangadi ne domin murnar cikar kungiyar ECOWAS shekara 50 da kafuwa. Kasan an kafa kungiyar ne ranar 28 ga watan Mayu,1975 bana kungiyar za ta cika shekaru 50. To kasancewa shekaru 50 sun wuce wasa na ga cewa, kungiyar ta cancanci a yaba mata, kuma a kara matakaimi da azama. Kuma za ka yarda da ni idan na ce ma cikin wadannan shekaru 50, Kungiyar ta taka muhimmiyyar rawa ta a zo a gani...
Duba da yadda yanayin muhalli yake, zai ba da dama wajen rage fuskantar sauyin yanayi tare da inganta kiwon lafiyarsu, abincinsu da kuma ingancin ruwan shansu. 2- Fashin Baki Kan Abin Da Zai Iya Afkuwa A Wajen Kiwon Su: Ga wanda zai fara wannan kiwo, ana so ya zabi wajen da ya dace da kuma tsarin da zai yi, don guje wa abin da zai iya afkuwa a bangaren sauyin yanayi mai tsanani. 3- Raba Kafa A Yayin Kiwon: Masu iya magana na cewa, ‘Ba a zuba kwai a cikin kwando daya’, wato ma’ana, ana so ka raba kafa ta hanyar yin wata dabara a kan kayanka, don kaucewa yin asara. Kazalika, raba kafa na taimakawa wajen kara bunkasa kiwo...
Alkaluman hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa a watan Afirilun bana, hada-hadar cinikayyar shige da ficen hajoji ta amfani da kudin kasar yuan ta karu da kaso 5.6 bisa dari. Alkaluman da hukumar ta fitar a Juma’ar nan sun nuna cewa, adadin hajojin da kasar Sin ta fitar ya karu da kaso 9.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 2.27, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 314, yayin da adadin hajojin da kasar ta shigo da su daga waje ya karu da kaso 0.8 bisa dari a shekara zuwa kimanin yuan tiriliyan 1.57. Cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, jimillar hajojin da Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar ketare a hada-hadar kudin kasar yuan sun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Minista Tuggar ya bayyana cewa, kasar Cuba ta taka mihimmiyar rawa wajen samar da ‘yancin kai ga wasu kasashen Afrika a lokacin da ake gwagwarmaryar kwato ‘yanci daga ‘yan mulkin mallaka a shekkarun 60s, 70s, 80s da 90s. “Cuba da Nijeriya sun yi aiki tare wajen yaki da ‘yan mulkin mallaka a kasashen Angola, Namibia, Afrika ta Kudu da Zimbabwe” in ji shi, ya kara da cewa, wannan sabon yarjejeniyar za ta karfafa hadin kai a bangarorin kimiyya da fasaha, bincike da kuma samar da ci gaba mai dorewa. A nasa tsokacin, Ministan harkokin waje na Cuba, ya ce, dangantakar da ke tsakanin Cuba da Afrika mai karfi ne, ya kuma gode wa Nijeriya a kan goyon bayan da ta...
A ranar 21 ga watan Mayu, Manchester United za ta kara da Tottenham Hotspur a wasan ƙarshe da za a buga a filin wasa na San Mames da ke birnin Bilbao, a ƙasar Sifaniya. Tottenham kuwa na fatan lashe kofin Turai na farko. Za a jira a gani wacce ƙungiya ce za ta ɗauki kofin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, sai na (Batsari/Safana/Ɗanmusa) Hon. Iliyasu Abubakar. An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa, Xi ya yi nuni da cewa, shekaru 80 da suka gabata, al’ummomin kasar Sin da na kasar Rasha sun bayar da gudummawa mai tarihi da ba za a taba mantawa da ita ba wajen samun nasarar yaki da zaluncin danniya a duniya, tare da kulla kakkarfar alaka da ba za a iya kassarawa ba ta hanyar sadaukar da jini, wadda ta kafa tubulin raya dangantakar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa. Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa...
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici. A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin...
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu. Kazalika, ma’aunin asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kasance cikin daidaito da sama da dalar Amurka tiriliyan 3.2 na tsawon watanni 17 a jere. Wani jami’in hukumar musayar kudaden waje ta kasar Sin ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, tare da nuna juriya da karfi a ci gaban tattalin arziki, wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da...
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi. Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.” Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu. Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin...
Rundunar sojan Ruwan Amurka ta sanar da cewa; Jirgin sama samfurin F-18 wanda kudinsa ya kai dalar Amurka miliyan 67 ya fadi akan jirgin dakon jiragen ruwa na ” USS Harry Truman” a tekun “Red Sea”. Jaridar ” Washington Post” ta buga labarin dake cewa; Jirgin ta fado ne a lokacin da yake kokarin sauka akan doron jirgin ruwan dakon jiragen saman na ” USS Harry Trauman”. Sanarwar ta kuma kara da cewa; Matuka jirgin sun fice daga cikinsa ta hanar lema, kuma an tserato da su daga cikin ruwa ta hanyar jirgi mai saukar angulu. Matukan, kamar yadda sanarwar ta sojojin na Amurka, sun ji rauni. Wani jami’in soja wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya fada wata kafar...
Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau, rukunin farko na tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa na kasar Sin kashi na biyu wadda za ta je yankin Abyei, ya tashi daga birnin Zhengzhou na kasar Sin, da jirgin saman soja domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 12. Bugu da kari, ana shirin tura rukuni na biyu na tawagar a tsakiyar watan Mayu. Kasar Sin ta aike da tawagar wanzar da zaman lafiya da martanin gaggawa ta farko zuwa yankin Abyei a watan Mayun shekarar 2024. Tawagar tana dauke da bangarori da dama da suka hada da bangaren tuki, sadarwa, bincike, da kiwon lafiya, wadanda ke yin sintiri da makamai, da kula da wadanda suka jikkata, da kuma...
Kawamcen jam’iyyun siyasa na kasar Ivory Coast ya bukaci a sake lalen yadda aka tsara yadda ake ristar jam’iyyu a hukumar zaben kasar, ganin yadda ta hana rijistar wasu jam’iyyun saboda dalilai daban daban. Shafin yanar gizo na labarai Afirka news ya bayyana cewa an kafa kawancen ne wanda aka sanyawa suna CAP-CI a farkon wannan shekarar, don tunkarar zaben shugaban kasa wanda za’a gudanar a ranar 25 ga watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Kawancen CAP gamayyar jam’iyyun adawa da dama ne na kasar, in banda Jam’iyyar da Lauranta Bagbo a kafa don tunkarar zaben na watan Octoba. Har’ila yau kawancen na zargin hukumar zaben kasar da rashin adalci a yadda take amincewa da yan takara a...