2025-06-15@21:57:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 123

«Rashin gudanar da Hawan»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...
    Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba da cewa “Mun san cewa kuskure daya tal zai iya cutar da kungiya. Sakamako da kuma makin da kungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horarwa ko kuma dan wasa ya rasa damarsa a cikin kungiya.”Hakan ya faru ga Erin ten Hag – domin daya daga cikin kurakurai hudu da na’urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a...
    Kasashen Iran da kuma Lebanon sun tattauna kan dangantakar dake a tsakaninsu dama halin da ake ciki a yankin. A wata tattaunawa ta wayar tarho da yammacin yau Asabar, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Lebanon din Youssef Raji sun jaddada muhimmancin mutunta juna da hadin gwiwa. Iran da Lebanon suna da dangantaka mai karfi da ta dogara da muradu guda, tare da ci gaba da tattaunawa don karfafa hadin gwiwa a cikin kalubalen da ake fama da shi a yankin. Araghchi ya taya Youssef Raji murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon ministan harkokin wajen Lebanon, tare da yi masa fatan samun nasara a sabuwar gwamnatin Lebanon. Ya jaddada mahimmancin raya dangantakar dake tsakanin...
     Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan. Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da...
    A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu. Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu...
    Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu.   Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen.   Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
    Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
    Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya raba fiye da Naira Miliyan 75 ga masu karamin karfi. Malam Umar Namadi, ya  yaba da tsarin bada tallafin ga al’ummar karamar hukumar ta Miga. A cewarsa, tsarin bada wannan tallafi da kakakin majalisar ya yi ya  dace da kudirorin gwamnatin jihar 12. Yana mai nuni da cewar, a kowacce Karamar Hukuma  za a kaddamar da irin wannan tallafi domin bunkasa tattalin arzikin...
    Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya.   Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar Isra’ila Inbar Lipman Garden, cewa ya yi   A wannan rana mai girma muna tuna Yahudawa maza da mata da yara miliyan shida da aka kashe a cikin Holocaust tare da miliyoyin wasu da ke shan wahala a ƙarƙashin mulkin Nazi.   Muna girmama abubuwan tunawa da su ba wai kawai nuna rashin jin dadi ba a a har ma da sake tabbatar da aniyarmu...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
    Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.