Gwamnatin HKI ta kai farmaki kan tawaga masu rajin kare hakkin bil’adama dauke da kayakin agaji a cikin jirgin ruwa dauke da kayakin agaji zuwa zirin Gaza wacce ta hana shigar abinci cikinsa kimani watanni biyu da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar gwamnatin tsibirin Malta na cewa HKI ta kai hari kan jirgin agajin ne tare da amfani da jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga Nesa, a ruwayen kasa da kasa.

Labarin ya kara da cewa jirgin agajin ya tashi daga tsibirin Malta da nufin isa Gaza, saboda isar da kayakin agajin da suke dauke da su zuwa Gaza, wacce aka killace. Yahudawan saun kai hari da misalign karfe 12.23 a lokacin Malta a daren Jumma’a.

Labarin ya kara da cewa ba wanda ya mutu ko ya ji rauni daga cikin wadanda suke cikin jirgin. Kungiyoyin agaji na kasa da kasa ne suka shirya wannan tafiya mai hatsari don tallafawa mutanen Gaza, sannan akwai fitattun mutane a duniya wadanda suke cikin jirgin agajin.

Kungiyoyin sun bukaci a ya All..wadai da HKI, saboda kai wannan harin, sannan a yi allawadai da ita saboda killace yankin gaza da kuma kashe falasdinawa fararen hula maza da mata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona da iri kan Gaza da kuma al’amuran yanki da na kasa da kasa, inda ya bayyana irin girman bala’in jin kai da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a karkashin gwamnatin Amurka da ke mara baya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Likitoci A Amurka A  Amurka Sun Bukaci A Kawo Karshen Abinda Ke Faruwa A Gaza
  • Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
  • Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon
  • Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan
  • Sojoji sun ceto fasinjoji 99 daga hatsarin kwale-kwale a Ribas
  • Rikicin Boko Haram Da ISWAP: An Kashe Masunta 18, Mutane  Da Yawa Sun Bace
  • ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa na Bayelsa
  • An Bukaci Masu Yiwa Kasa Hidima Su Yi Amfani Da Kafofin Sadarwa Na Zamani Don Inganta Hadin Kan Kasa.
  • Katafaren Jirgin Daukar Jiragen Yaki Na Kasar Amurka Harry Truman Zai Fice Daga Tekun Maliya