HausaTv:
2025-07-30@22:00:47 GMT

Ukraine: Tawagogin Rasha da Amurka sun kammala tattaunawa a Saudiyya

Published: 25th, March 2025 GMT

Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin.

Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.

Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya.

Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin “mai amfani.

Yayin da a cewar Rasha “Akwai abubuwa da yawa da za a yi,” in ji Dmitry Peskov.

Yanzu haka dai Washington da kyiv suna kokarin ganin a kalla, a dakatar da kai hare-hare na wucin gadi a wuraren makamashin Ukraine, wadanda suka lalace sosai.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza.

A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki.

Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin Hamas sun fahimci bukatar neman cimma muradun al’ummar Gaza da ake zalunta ta hanyar da ta dace, kuma ba sa bukatar shiga tsakani na bangarori na uku dangane da hakan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya yi la’akari da katsalandan din Iran a cikin shawarwarin da suka dace da cewa ba shi da tushe balle makama, yana mai jaddada cewa irin wadannan zarge-zarge wani nau’i ne na neman tauyaye hakki da gujewa hakkin da ya rataya a wuyar mutum da kokarin Amurka na gujewa duk wani mugun aiki da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aikita kan al’ummar Falasdinu, da suka hada da kisan fararen hula 60,000 da ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da mata da kananan yara da kuma killace Zirin Gaza tsawon watanni. Da hana shigar agajin jin kai da kuma kashe fararen hula da ke fama da yunwa da kishirwa a tarkon kisa a wuraren da ake kira cibiyoyin rarraba kayan agaji da wata cibiyar Amurka ta kafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ