Falasdinawa Kimani 80,000 Ne Suke Halattar Salla A Masallacin Al-Aksa A Cikin Watan Ramadan
Published: 5th, March 2025 GMT
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin.
Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi.
Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin kansu, don fuskantar yahudawan Sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasarsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin.
A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, baje kolin CAEXPO ya bayyana yadda Sin da kungiyar ASEAN suka himmatu wajen bunkasa bude kofa bisa matsayin koli, da kare tsarin cinikayya cikin ’yanci da kasancewar mabambantan sassa.
Kafar CGTN ta gabatar da kuri’ar ne da harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da yaren Rasha, inda kuma mutane 6,260 suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’ao’i 24. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp