2025-09-19@05:22:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3688

«Allah Ya ba»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A nasa jawabin, Air Marshal, AVM JA Usman, ya yaba wa hafsan hafsoshin sojin saman bisa jajircewarsa da kuma sadaukarwa wajen ciyar da harkokin sojin sama da sauran ma’aikata gaba. ya yi nuni da cewa, taron ya sabunta ƙudirin hukumar na yin amfani da fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra, ta fara bincike kan kisan wasu mutum huɗu da ’yan bindiga suka yi lokacin da suke zaman makoki. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa masu makokin wuta ne a ranar Alhamis a garin Ogidi, da ke Ƙaramar Hukumar Idemili. Hilda Baci ta kafa tarihin dafa shinkafa buhu 200 a tukunya guda Abba ya tarbi tagwayen da aka raba da juna bayan yi musu tiyata a Saudiyya Harin ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu tare da jikkata aƙalla mutum 15. Kakakin rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce suna zargin harin ya shafi rikicin ƙungiyoyin asiri ne. Ya ƙara da cewa jami’an tsaro da suka isa wajen sun gano harsasai 16, kuma za su yi amfani...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...
    Shugaban rikon kwaryar Siriya ya bayyana cewa; Babu sabani na dindindin da Iran Shugaban rikon kwarya na Siriya Abu Mohammed al-Jolani ya yi magana kan alakar Siriya da sauran kasashe, inda ya mai da hankali kan Rasha, Iran da Masar. Ya kuma yi jawabi game da zaben Siriya da ayyana kundin tsarin mulkin kasar da kuma abubuwan da suka faru a lardin Suweida na kasar. Shugaban rikon kwaryar ya fada a jiya Juma’a cewa: Kasarsa ta yi saurin sake gina huldar dake tsakaninta da kasa da kasa, kana ta samu goyon baya daga galibin kasashe musamman na yankin. Ya yi nuni da cewa, ba za a so a kasance cikin halin damuwa da wata kasa ba, kuma kwallon tana cikin...
    Jami’in kungiyar Hamas yayi tsokaci kan yunkurin kashe tawagar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Doha Jami’in kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas, Osama Hamdan ya ce: Yunkurin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi na kashe tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar wani hari ne kai tsaye kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tsagaita wuta. Ya kara da cewa a wata hira da aka yi da shi a gidan telebijin, “yunkurin kashe tawagar Hamas hari ne kai tsaye kan shirin shugaba Trump, idan har Isra’ilawa sun amince da Shirin na Trump, to su saurari martanin Hamas, maimakon mayar da martani ta hanyar jefa bam a birnin Doha da wurin taron jami’an kungiyar.” Hamdan ya yi...
    Wike ya goyi bayan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a wani mataki da ya samu matsayin ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Duk da yake har yanzu shi mamba ne na PDP, Wike ya kasance yana bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar yayin da yake kuma yin aiki don sake zaɓen Tinubu, wani matsayin da yawancin mambobin PDP ba sa jin daɗinsa. Kafin yanzu, jam’iyyar ta shiga cikin wata babbar matsala kan matsayin sakatare jam’iyyar na ƙasa, tsakanin Samuel Anyanwu, wanda Wike yake goyo baya, da Sunday Ude-Okoye, wanda yake samun goyon bayan Gwamnan Jihar Inugu, Peter Mbah. Mafi yawancin shugabannin jam’iyyar sun yi tunanin cewa idan har Anyanwu ya dawo a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa zai...
    Wani mahaifi, Mande Achagh, ya ce matsalar ta fi yin ƙamari a gundumarsa ta Agagbe, a ƙaramar hukumar Gwer West inda yawancin waɗanda basu da matsuguni suka samu mafaka, a wurare na musamman, makarantu, da kuma wasu gundumomi na al’umma. “Matsalar tafi matuƙar lalacewa a Gwer ta Yamma abin kuma ya shafi makarantu sosai. Ina fatan gwamnati zata kalli lamarin domin ta ɗauki mataki, wajen samarwa mawaɗanda suka rasa matsuguni wuraren zama ta haka ‘ya’yanmu za su iya koma harkar karatu ta amfani da azuzuwansu. “Irin matsalar da su yaran namu suke fuskanta dangane da karatunsu ba abinda za ayi wa riƙon sakainar kashi bane. Abin yana matauƙara ɓata mani rai, saboda wasu wuraren yara suna karatu ne a ƙarƙashin...
    A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
    Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta raba kayan tallafi ga al’ummar Jalingo-Kamo da ambaliyar ruwa ta shafa a Karamar Hukumar Kaltungo, inda iftila”in ya shafi gidaje kimanin 90. Rabon kayan ya biyo bayan umarnin Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya amince da bayar da kayan abinci da na masarufi domin rage raɗaɗin da jama’ar da abin ya shafa suke ciki. NAFDAC ta kama jabun maganin maleriya na ₦1.2bn a Legas Harkar tsaro a gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa — Sanata Lamiɗo Yayin rabon kayan a fadar Hakimin Jalingo-Kamo, Sakataren Hukumar SEMA, Alhaji Abdullahi Haruna Abdullahi ya ce sun gudanar da cikakken bincike da ƙirga waɗanda abin ya shafa kafin rabon. Abdullahi ya bayyana lamarin...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara.   Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya ce: “Ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare hakki da tsaron al’umma, kuma ba za su taba tasirantuwa da kage-kagen yanayi ba, kuma za su yi aiki da karfi da azama wajen tabbatar da muradun al’ummar Iran.” Wannan dai ya zo ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Alhamis, inda ministan harkokin wajen kasar Abbas...
    Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta. Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta...
    Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a. Majiyoyi a asibitocin Gaza sun bayyana cewa: Shahidai 27 ne a kai zuwa asibitin Al-Shifa, shahidi daya zuwa asibitin Al-Ma’amoudiya, shahidai uku zuwa asibitin shahidan Al-Aqsa, da shahidai biyar zuwa asibitin Nasser. Wani Falasdine ya yi shahada kana wasu kuma suka jikkata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin birnin Gaza. Share 0...
    An kammala taron baje kolin zuba jari na duniya na Sin karo na 25 (CIFIT) a jiya Alhamis 11 a birnin Xiamen. A yayin taro na wannan karo, an kulla yarjejeniyoyin ayyukan zuba jari guda 1,154, inda jimillar kudin dake kunshe a ciki ta kai kudin Sin Yuan biliyan 644 (kwatankwacin sama da dala biliyan 90.5 ). An kuma fitar da rahotanni masu inganci guda 21. Taron mai taken “Hadin kai da Sin don zuba jari ta yadda za a samu bunkasa nan gaba,” ya gudana ne a fadin filin baje koli da ya kai murabba’in kilomita 12. An gudanar da ayyukan habaka zuba jari sama da dari, kuma tawagogin kasashe da yankuna fiye da 120 sun halarta, tare da...
    Bugu da kari, kafa wurin kare muhalli na kasa da kuma tsara ayyukan kamun kifi a tekun tsibirin Huangyan na da matukar muhimmanci ga ci gaban masana’antar kamun kifi a yankin.   Matakin da Sin ke dauka a wannan karo ya nuna iyakoki da manufofin da aka tsara a karkashin doka, ya kuma fayyace iyakokin ayyukan da suka kamata a yi a tekun tsibirin Huangyan, kana ya bullo da shiri mai ma’ana domin rigakafin barkewar rikice-rikice. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Direban ya yi nasarar tserewa, amma sun harbi motar, inda Zakari Benjamin da Samaila suka samu raunuka a ƙafafu,” in ji shi. ‘Yansanda daga Kontagora sun isa wajen da abin ya faru, sannan suka kai waɗanda suka ji rauni asibiti. Abiodun ya ƙara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa wajen, amma ‘yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji. Ya kuma shawarci direbobi da su guji yin tafiya cikin dare. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindiga sun kai wa wata mota hari a kan hanyar Tegina zuwa Kontagora a Jihar Neja, inda suka jikkata mutum biyu. Harin ya faru ne a Tudun-Fulani bayan direban motar ya ƙi tsayawa lokacin da ’yan bindigar suka buƙaci ya tsaya. ’Yan Najeriya sun kusa fara shan wutar sa’o’i 24 babu ɗaukewa — Minista Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 Rashin tsayawarsa ya sa maharan suka buɗe wa motar wuta, inda suka jikkata fasinjoji biyu da ke zaune a kujerar gaba. Wannan lamarin ya faru ne bayan sa’o’i da ’yan bindigar suka sace wasu makiyaya a garin Usalle da daren ranar Laraba. Rahotanni sun nuna cewar ’yan bindigar sun tura makiyayan bakin hanya sannan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da miƙa ƙudirin doka ga Majalisar Dokokin Jihar domin haramta auran jinsi da kuma wasu aiyukan batsa a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 31 da aka gudanar a ofishin gwamnati na birnin Kwankwasiyya. A wata sanarwa da kakakinsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci tauye darajar addinin Musulunci da al’adun Kano ba. ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Fashi 3 A Kano, Sun Ƙwato Motar Sata Akwai Tara Mai Tsauri Ga Duk Wanda Ya Sare Bishiya Ba Bisa Ƙa’ida Ba – Gwamnatin Kano Ya bayyana cewa ƙudirin ya fi karkata kan hana auran jinsi ɗaya,...
    Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fara samun wutar lantarki ta tsawon sa’o’i 24 ba tare da ɗaukewa ba. Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya ƙaddamar da sabbin ɗakunan horo da ɗakin kwana a Cibiyar Horas da Ma’aikata ta Ƙasa (NAPTIN). Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya Adelabu, ya ce gwamnati ta samu nasarar samar da wutar lantarki da rarraba ta a matakin da ba a taɓa samu ba a tarihin ƙasar. Ya bayyana cewa bunƙasa wutar lantarki shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa, domin tana tallafa wa makarantu, asibitoci, masana’antu da kasuwanci. Ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi...
    Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Ƙwarewa a Nijeriya (NARD) ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, bayan gwamnatin tarayya ta kasa cika mafi ƙarancin bukatun da ƙungiyar ta gabatar cikin wa’adin sa’o’i 24 da ta sanya. Wannan mataki ya zo ne bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (E-NEC) ta yanar gizo a ranar Laraba, 10 ga Satumba, 2025. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dakta Osundara Tope Zenith, ya tabbatar da hakan, inda ya ce yajin aikin ya zama dole bayan shiru daga bangaren gwamnati. Ƙungiyar ta jaddada cewa rashin biyan Kudaden Tallafin Koyan Aiki (MRTF) ga wasu asibitoci, tare da rashin biyan alawus na watanni biyar daga karin kaso 25% da 35%, da sauran hakkoki da aka dakatar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sau da dama wadanda ke dauke da nau’in jini na AA na bayyana cewa sun fi kowa lafiya.   Suna bayyana cewa basa rashin lafiya kamar yadda masu sauran na’ukan jini ke yi. NAJERIYA A YAU: Rayukan Da Aka Rasa Sakamakon Ambaliyan Wannan Shekarar DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan ko da gaske ne masu nau’in jini na AA sun fi sauran masu nau’ukan jini lafiya. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamnatin jihar ta sha alwashin bayyana sakacin aikin da Kwamishinan ya yi da zarar ta kammala bincike.   Don haka, an umurci  babban jami’i a ma’aikatar da ya ci gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatar har zuwa lokacin da za a fitar da wata sabuwar sanarwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa makiya suna son cusa gaba a tsakanin kasashen musulmi don su sami damar sace arzikin makamashin da sunke da shi da kuma jawo hankalin kwararrun da kasashen musulmi suke da shi don amfanin kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo shugaban kasar yana fadar haka a safiyar yau Alhamis, a birnin Ardabil da ke kusa da ke iyaka da kasar Azarbaijan daga arewacin kasar. Masoud Pezeshkian ya je landin ne don kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da ayyukan raya kasa wadanda aka kammala a yankin har guda 72. Shugaban ya kara da cewa, da wadannan kasashe basu da kome ba zasu zo su nemi wani Abu a wajemmu...
    A cewarsa, kudaden fansa da ake yawan ji ana biya yawanci iyalan wadanda abin ya shafa ko al’ummarsu ne ke tarawa.   Ya kuma bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan bindiga sun karɓi sama da Naira biliyan 2.5 a shekarar 2025 kadai, adadin da ya ce babu wata gwamnati da za ta iya ɗauka.   Masanin tsaron ya ce matsalar tsaro a Najeriya ta fi ƙarfin dabarun soja kaɗai, inda ya danganta ta da cin hanci da rashawa wanda ya kira “babban mai ba da damar ayyukan ta’addanci.”   Ya yi gargadin cewa ya zama dole a guji yin zarge-zargen da ba su da tushe kan shugabannin da ke kan karagar mulki, yana mai tunatar da cewa irin wadannan maganganu...
    Kasar yamen itace kasar larabawa daya tilo a kasashen musulmi ta duniya da ta mike ta kalubalanci yakin kare dangi da HKI take ci gaba da yi kan yankin falasdinu, da Israila ta kira da yunkurin samar da fadaddiyar Isra’ila. Wani babban jami’in soji na kasar yaman ya fadi cewa za su ladabatar da isra’ila kan wannan hari da ta kai, Isra’ila ta kai hari kan wuraren farar hula, inda mutane da dama suka yi shahada wasu kuma suka jikkata, kuma duk wannan sadaukarwa ba zai hana ci gaba da goyon bayan alummr gaza ba, da kuma ladabtar da Isra’ila. Wasu majiyar labarai ciki har da kamfanin dillancin labarai na reuters da ma tashar talabijin din isra’ila sun sanar cewa...
    Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tayi Allah wadai da harin ta’addanci da hki takai kan ginin ma’aikatar sadarwa guda biyu a kasar Yaman da ya kai ga shahadar wasu yan jaridar  guda biyu. Har ila yau tayi tir da hari da isra’ila takai kan muhimman wurare a kasar yamen da yankunan farafen hula ,da haka yayi sanadiyar shahadar wasu mutane kuma ya shafi wasu fararen hula na daban, don haka tayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya data dauki matakin gaggawa na dakatar da  laifukan yaki da HKI take tafkawa. Ta ce gwamnatin Isra’ila tana ci gaba da kai hare-hare a kasashen yankin, tare da ci gaba da kisan Karen dangi a Gaza, da hakan ya sabama dan...
    ‘Yan fashin sun raunata mutum ɗaya a cikin ‘yan gidan suka kai harin. ‘Yansanda sun ce an bi diddigin waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da tsauraran bincike. ‘Yansanda sun kuma yi gargaɗin cewa za su ci gaba da aiki tare da al’umma da ƙungiyoyi tdon hana aikata laifuka da kuma tabbatar da tsaron al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugabannin kasashen Afirka sun kammala taron kwanaki 3 kan sauyin yanayi na Afirka a babban birnin kasar Habasha a jiya Laraba tare da amincewa da sanarwar Addis Ababa, inda suka yi alkawarin mayar da nahiyar ta zama cibiyar samar da makamashi mai safta da kuma hanyoyin magance sauyin yanayi a yayin da suke neman kudade na gaske. Shugaban kasar Habasha Taye Atske Selassie, wanda ya rufe taron, ya ce taron ya nuna cewa Afirka ba ta shiga cikin rikicin da ba ta haifar da shi ba. ” Mun himmatu wajen samar da wata nahiya mai wadata,” in ji shi. “Zalunci ne cewa sama da ‘yan Afirka miliyan 600 har yanzu suna rayuwa ba tare da samun wutar lantarki ba. Dole...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa.   Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar. Domin sauke shirin, latsa nan
    A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar. Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan. Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da...
    Zanga-zangar matasa a Nepal, da aka ƙirƙira a matsayin “Gen Z Revolution,” ta ɓarke ne da nufin ƙalubalantar rashawa da takunkumin amfani da kafofin sada zumunta, sai dai ta rikiɗe zuwa tarzoma mai muni. Rahotanni sun bayyana cewa, an fara zanga‑zangar ne sakamakon hana amfani da manyan kafafen sada zumunta guda 26, ciki har da Facebook, X da YouTube, lamarin da ya fusata matasa sosai. An dai soma zanga‑zangar cikin lumana, amma gwamnatin ta ƙasar ta yi ƙoƙarin daƙile muryar matasan, wanda ya sanya masu zanga‑zangar da dama suka riƙa taruwa a Maitighar Mandala — suka mamaye hanyar shiga Majalisar Ƙasa. An ƙona matar tsohon firaministan Nepal Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, na daga cikin wadanda...
    Haka zalika, Ministan Ilimi, Dakta Olatunji Alausa , shi ma ya jinjinawa rawar da Gwamna Sani ya taka wajen sauƙaƙa bikin kaddamar da Cibiyar Horar da Sana’o’i da Kwarewa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gudanar, yana mai cewa yanzu haka ana sake fasalin makarantun fasaha na ƙasa baki ɗaya domin su mai da hankali kacokan kan darussa masu amfani da tasiri.   Shettima ya bukaci mambobin NCS da su hada kai bayan wani tsari guda na juyin-juya halin Nijeriya, yana mai gargadin cewa “ba za mu iya gina ma’aikata da za su yi shiri a nan gaba kan tushen rarraba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya....
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata. Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan ne a cikin gida kafin su kunna wutar. An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi An garzaya da ita asibitin kula da waɗanda ibtila’in ƙuna ya afkawa da ke Kirtipur cikin mummunan yanayi, amma daga ƙarshe ta ce ga garinku nan sakamakon munanan raunuka da ta samu. Rasuwarta ta zo ne a daidai lokacin...
    Shaidu sun ce yawancin ‘yan kasuwar sun gudu cikin daji, domin tsira da rayukansu. Maharan sun kashe sojoji biyar da ‘yan kasuwa kusan 10. Al’ummar sun roƙi gwamnati a matakan ƙananan hukumomin, jiha da tarayya su tallafa musu wajen tsaro, ilimi, lafiya, da samar da hanyoyi. Kakakin sojojin, Kyaftin David Adewusi, ya ce bai san da labarin harin ba amma zai yi bayani daga baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jiragen yakin HKI sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a yau Laraba, inji tashar talabijin ta Al-Masirah na gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa yahudawan sun kai hare-haren ne a tsakanin wasu duwatsu a cikin kasar, da kuma kan cibiyar kungiyar Ansarullah da ke tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar, da kuma ma’aikatar tsaron kasar. Wadanda suka ganewa idanunsu sun bayyanawa kamfanin dillancin labaran reuters kan cewa yahudawan sun kai hare-haren kan wani barikin soja ne a yau Laraba. Kafin haka dai sojojin Yemen sun kai kaiwa HKI hare-hare a gewayen birnin Qudus da kuma tashar jiragen saman da Ramona da ke kudancin kasar kusa da birnin Ummu Rashrash ko Ilaat kamar yadda yahudawan suke kiransa. Gwamnatin kasar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a birnin Alkahira. Ya nuna irin hakurin da JMI ta nuna bayan hare-haren da aka kai mata kan cibiyoyin Nukliyar kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau a shafinsa na X kan cewa, Iran ta amince da takaitaccen aiki da hukumar IAEA ne saboda dole ne ya zamanto ana kula da ayyukan nukliyar kasar ko da takaitacce ne. Sannan ya ce kasar tana son ci gaba da raya yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015. Ya ce, Iran ta amince da wannan takaitaccen yarjeniya ne bayan ta...
    Duk kasar da take son kawo wa al’ummarta ci gaba ta wayewar zamanin da muke ciki wajibi ne ta mayar da hankali a kan gwada basirar ilimin kirkiro da sabbin fasahohi na ci gaba wadda hatta sauran al’ummomi za su amfana, amma ba tayar da husuma da neman zubar da jini ko mai karfi ya danne mara karfi ba. Gudanar da gasa mai tsafta a ko wane fage na ci gaba halas ne, saboda hakan na samar da karin kuzarin ci gaba, amma ba komawa ga zamanin kauyanci na rayuwa tamkar ta namun daji ba! (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Bisa amincewar majalisar gudanarwar kasar Sin, gwamnatin kasar za ta kafa yankin kare muhallin halittu na Huangyan Dao. Tuni dai aka fitar da sanarwar amincewa da hakan a shafin yanar gizo na gwamnatin tsakiyar kasar Sin, wato www.gov.cn a Larabar nan, bayan da ma’aikatar kare albarkatun kasa ta gabatar da bukatar hakan. Sanarwar amincewa da wannan bukata, ta ce kafa wannan yanki na Huangyan Dao, muhimmin tabbaci ne ga wanzuwar matakan kare muhallin halittu mabanbanta, bisa daidaito da dorewa. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Yayin da aka gano gawar Surajo a ranar Litinin, an gano gawar Fatima washegari, Talata. Sai dai har yanzu ba a gano gawar kanwar Fatima ‘yar shekara uku, Haneefa ba.   A lokacin da lamarin ya faru, Fatima tana goye da kanwarta Haneefa mai shekaru uku a duniya.   Su biyun suna dawowa ne daga gidan kakarsu da ke Magume zuwa gidan su da ke Tudun Jukun.   Malamin Islamiyyar su Fatima, mai suna Malam Daddy ne ya yi musu rakiyar hanya acikin kekensa mai taya Uku (Keke-napep).   Shaidun gani da ido sun ce, abin takaicin ya afku ne a mahadar da ke kusa da Cocin Nasara Baptist da ke kan hanyar Gaskiya babban layi a Tudun Jukun.  ...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya isa kasar tunisiya domin tattaunawa da hukumomin kasar, a ci gaba da ziyarar da yake yi a yammacin Afrika, bayan da ya bar kasar masar inda ya gana da directan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  kuma suka cimma matsaya tsakaninsu, An tsara cewa babban jami’in diplomasiyar na iran zai gana da  ministan harkokin wajen kasar inda za su tattauna game da dangantar dake tsakanin kasashensu, da ma na kasa da kasa, A wani sako da ya aike da shi a shafin sa na X Araqchi ya nuna jin dadinsa sosai da kuma jinjinawa ga gwamnatin kasar masar game da rawar da ta taka a bangaren diplomasiya...
    Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba da fifiko kan hadin kai da karfafa jam’iyyar a fadin jihar. Ya ce, “Ina godiya ga daukacin shugabanni da ‘yan jam’iyyar NNPP na Jihar Kuros Riba, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode muku da kuka karɓe mu, muna matukar farin ciki da shugabancin jam’iyyar a jihar, ina kara baku kwarin guiwa da ku yi aiki tukuru don ganin an samu...
    “Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim.   Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba.   “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Onuh ta ce, “Ba zai yi wu ba, mu bar ayyukanmu, da yawa daga cikinmu sun yanke hutun da suke kai, muka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.   “An jefa ‘yan’uwanmu cikin hatsari, wannan ba abun wasa ba ne, don haka mun dakatar da taron kuma mun umarci Ministan ya bayyana a gaban wannan kwamitin cikin sa’o’i 48.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na addini na fitar da wani kaso na kudaden Khumusi don haka. A cikin cikakken labarin, a baya-bayan nan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da izini na addini na ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Falastinu da ake zalunta a Gaza. Ga rubutun tambaya da amsar, kamar yadda gidan yanar gizon KHAMENEI.IR ya...
    Martanin farko da gwamnatin Siriya ta fitar game da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a Homs, Latakia da Palmyra Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta yi kakkausar suka tare da Allah wadai kan hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu wurare a yankunan Homs, Latakia da Palmyra, lamarin da ya saba wa dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Siriya da kuma ‘yan kasashen ketare ta tabbatar da cewa: Wadannan hare-haren suna nuni ne a fili karara na keta hurumin Jamhuriyar Larabawa ta Siriya, barazana kai tsaye ga tsaronta da zaman lafiyar yankin, kuma wani bangare ne na ci gaba da kai hare-hare da Isra’ila ke ci...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi. Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar. DSS ta warware tankiyar da ke tsakanin NUPENG da Dangote ’Yan bindiga sanye da hijabi sun sace mutane 11 a Zamfara Ya ce an ceto ɗan Masar ɗin ne a ranar Talata da safe — kwana ɗaya kacal bayan sace shi — ba tare da an biya kuɗin fansa ba. Osifeso ya ce an sace mutumin ne a yankin Alomaja, kusa da garin Idi-Ayunre, wani yanki...
    “Da samun rahoton, babban jami’in ‘yansanda na yankin, ya jagoranci tawagar jami’an ‘yansanda kai tsaye zuwa wurin.   “Da suka hango jami’anmu, sai suka ajiye kayan suka tsere cikin daji. Binciken wurin ya haifar da gano makaman nan: bindigogi AK-49 guda huɗu, bindigogi AK-47 guda uku, bindiga G3 guda ɗaya, bindiga ƙarama (Sub-Machine Gun) guda ɗaya, mujallu harsasai guda goma sha ɗaya, harsasai 7.62mm guda 4,046, harsasai 5.5mm guda goma sha ɗaya, harsasai 38mm guda 132, da harsashi guda 75.”   CP Mohammed ya ƙara da cewa, a wani samame da aka yi ranar 6 ga Satumba, 2025, bisa bayanan sirri, an kama wani mutum mai suna John Paul daga Abuja a tashar motar Akwanga-Wamba yayin da yake kan hanyarsa...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar. An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da...
    Ministan harokokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gana da tokwaransa na kasar Masar da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi a karon farko tun bayan yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka kaiwa Iran a cikin watan yunin da ya gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa, Aragchi ya kai ziyarar aiki na kwana guda birnin Alkahira a yau Talata ce don tattauna batun shirin Nukliyar kasar Iran da shugaban hukumar IAEA Rafael Grossi a birnin Al-Khahira. Labarin ya kara da cewa ministan ya ce Iran ta amince ta bude sabon shafi a huldarta da hukumar IAEA bisa wani sabon tsari wanda a cikin iran zata tabbatar da amincin shirinta...
    Yayin da ake gab da yin bikin ranar malamai ta kasar Sin karo na 41 nan ba da jimawa ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da martanin wasika ga wakilan malamai na musamman a duk fadin kasar, inda ya bayyana fatansa tare da mika gaisuwar ranar ga malamai da ma’aikata a bangaren ilmi a fadin kasar. A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru 20 da fara aiwatar da shirin “malamai na musamman”, da yawa daga cikin malamai na musamman sun dukufa wajen ba da ilmi a yankunan karkara, tare da nuna kishi da jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa za su ci gaba da tabbatar da aniyarsu kan koyarwa tare da bayar da sabbin gudumawa...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya buƙaci jami’an tsaro da su riƙa ɗaukar duk wani infoma da ke bayar da bayani ga ’yan bindiga a matsayin abu ɗaya da babu wani bambanci a tsakaninsu. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ƙananan hukumomin Wurno da Rabah a ranar Litinin da ta gabata, domin jajanta wa al’umma bisa hare-haren da ’yan bindiga ke kai musu. TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur Dalilin da muka yi watsi da buƙatar dawowar Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen daƙile matsalar ’yan bindiga a faɗin jihar, inda ya buƙaci mazauna ƙauyuka su riƙa tona asirin duk wanda suka sani yana...
    Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna da takwaran aikinsa na kasar masar badar albadelatty ta wayar tarho inda suka tattauna game da batutuwan da suka shafi yankin da kuma irin ci gaban da aka samu, kuma sun mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi Gaza da kuma shirin nukiliyar Iran na zaman  lafiya. Iran dai na neman isar da sakon diflomasiyya ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun saka tsakaninta da kasashen yammacin duniya dangane da shirinta na nukiliya. A halin da ake ciki, Masar ta dauki  kanta a matsayin babbar mai shiga tsakani a rikicin Gaza, inda ta daidaita alakar ta da kasashen Larabawa da ke makwabtaka da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya sun shiga taraddadin abin da ka iya biyo bayana kudurin Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (NPENG) na tsunduma yajin aiki.   Hakan dai ya biyo bayan tashi da aka yi daga zaman da Gwamnatin Tarayya ta kira don sasanta kungiyar, mai samun goyon bayan sauran kungiyoyin kwadago, da rukunin kamfanonin Dangote, ba tare da cimma wata matsaya ba. NAJERIYA A YAU: Yadda Ilimi Ke Ƙara Tsada Yayin Komawar Yara Makaranta DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Ministan Kwadago Muhammadu Dingyadi ne dai ya kira taron, wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da wakilan kungiyoyin NUPENG da NLC da TUC da na Dangote...
    El-Rufa’i ya jaddada cewa manufarsa ita ce ganin an tabbatar da gaskiya da bin doka a ƴansandan Nijeriya, domin tabbatar da jami’an suna aiki da gaskiya da biyayya ga ƙa’ida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina. Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce: “A Zamfara an kashe ‘yan ta’adda 30 a hare-haren sama da kasa, yayin da masu tada kayar baya 76 da suka hada da mata da kananan yara suka mika wuya ga jami’an tsaro.   “Rundunar ‘yansanda ta bayar da rahoton kama mutane 1,950 da ke da alaka da munanan laifuka, garkuwa da mutane, da kuma fashi. An kubutar da jimillar mutane 141 da aka yi garkuwa da su.   Ya ce hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama sama da kilo 66,000 na miyagun ƙwayoyi.   A ɓangaren Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC), ya ce hukumar ta yi nasarar gurfanar da ƙorafe-ƙorafe 588 ga kotu a cikin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Baghaei ya bayyana cewa dangantakar Iran da hukumar IAEA zai sauya saboda hare-haren da HKI ta kaiwa cibiyoyin makamashi nukliya na kasar iran a cikin watan yunin da ya gabata. Tashar talabijan ta Presstv a nan tehran ta nakalto Baghaei yana fadar haka a yau litinin ya kuma kara da cewa, ma’amalar kasar Iran da hukumar makamashin Nukliya ta IAEA zai sauya gwagwadon yadda al-amura suka sauya bayan yakin kwanaki 12 da HKI da kuma Amurka. Ya ce har’ila yau mu’amalar zata kasance bisa rahoton da hukumar ta IAEA ta aikawa iran da kuma wasu abubuwan da shugaban hukumar Rafael groosy ya ke riyawa a cikinsa. Da farko iran zata mayar masu da...
    Wasu mazauna unguwar Oworonshoki da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas, sun datse wani sashe na gadar Third Mainland a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da suka gudanar don nuna adawa da rushe musu gidaje. Datse hanyar da suka yi ya haddasa cunkoson masu ababen hawa da fasinjoji, lamarin da ya tilasta wa ’yan sanda tarar hanzarin lamarin, inda suka riƙa harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zangar-zangar. MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su kamo waɗanda suka kai hari a Bama Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2023 aka soma rusau ɗin, lamarin da ya raba wasu mazauna unguwanni kamar Oke-Eri, Odunfa Lane, Ogo-Oluwa, Precious Seed, Coker da kuma...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa kungiyar BRICS zata ci gaba da ayyukanta duk tare da matsalolin da take fuskanta. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron kungiyar ta BRICS ta hotunan yanar gizo da aka gudanar a yau litinin. Ya kuma kara jaddada cewa kungiyar da sannu zata wuce wadan nan matsalolin da suke gabatan a halin yanzu, sannan ta ci gaba girma da daukaka. Yace a cikin wuta ne ake gane zinari na gaskiya, don haka matsalolin da suke gabar kungiyar BRICS ne zasu fayyace irin karfin da kungiyar take da shi na fuskantar matsaloli, sannan ta ci gaba girma har zuwa lokacinda zata cimma manufar kafata. Shugaban...
    A yau Litinin, wasu rahotanni na cewa, yayin wani taron manema labaru na musamman kan zuba jari ga sassan ketare da aka gudanar a taron tattauna harkokin cinikayya da zuba jari na kasa da kasa na Sin karo na 25, cewa a shekarar 2024 adadin jarin da kasar Sin ta zuba kai tsaye a kasashen da suka shiga shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kai dalar Amurka biliyan 50.99, adadin da ya karu da kashi 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023. A dai yau din, ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, da hukumar kididdiga ta kasar, da hukumar kula da musayar kudin waje ta kasar, sun fitar da sanarwar “kididdiga ta shekarar 2024 kan...
      Ya bayyana karya ka’idojin da aka shimfiɗa kan amso basussukan a matsayin “babban abin damuwa da fargaba kan ɗorewar tattalin arzikin kasar,” yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar samar da “sabbin tsaruka masu ƙarfi, da za su daidaita hanyoyin karɓar rance na gaskiya, da kuma ƙuduri na bai ɗaya don tabbatar da cewa, duk kuɗin da aka karɓo ya dace da buƙatar shirin inganta zamantakewar ‘yar Nijeriya”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki.   Kwamishinan ya ƙara da cewa jagorancin Gwamnan na bai wa haɗin kan al’umma muhimmanci a matsayin ginshikin shugabanci na dimokuraɗiyya.   “Wannan ƙoƙarin wayar da kai yana nuna hangen nesa na Gwamna na gudanar da mulki mai maida hankali kan bukatun jama’a, inda kowace murya ke da muhimmanci, kuma kowane ɗan ƙasa yana da rawar da zai taka wajen gina makomar Jihar Kaduna.   “...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar tsaron DSS  a Najeriya ta aike da wasika ga dandalin sada zumunta  na X, wanda ake kira Twitter a da, inda a ciki ta ke bukatar ya sauke shafin dan gwagwarmaya din nan, Omoyele Sowore ko kuma ya fuskanci mataki mai tsanani . A wasikar da hukumar ta DSS ta wallafa a shafinta na X a safiyar wannan Lahadi, ta zargi Sowore da amfani da dandalin sada zumuntar wajen caccaka da kuma yin kalaman raini ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu. DSS ta yi ikirarin cewa magoya bayan Tinubu ba su ji daɗin rashin mutuncin da Sowore ya ke yi wa shugaban ba, saboda haka har sun fara zanga-zangaar rashin amincewa da hakan. Lamarin da jawo sabanin siyasa. DSS...
    Kwamitin ya kuma jaddada buƙatar wayar da kan jama’a da kamfen ɗin mutunta kai, da haɗa ɗabi’a mai kyau a cikin kundin karatu, da ɗaukar iyaye da ke taimaka wa ‘ya’yansu wajen magudi a matsayin masu laifi. Kwamitin ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da lalata ingancin tsarin ilimi a Nijeriya, abin da zai karya harsashin ci gaban ɗan Adam da tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana kan hana yaduwar makamin nukiliya kan kowacce kasa . Rahotan ya bayyana cewa Araqchi ya bayyana a shafinsa na x cewa batun samuwa ko fadada shirin makamin nukiliya ba shi ne a gabansu ba, lamarin shi ne waye ya bada dama a samu ci gaban ilimi ko da ma na shirin nukiliya na zaman lafiya ne, Ya jaddada cewa saboda haka wannan ba’a bin mamaki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada yin kira ga al’ummar Musulmi cewa: Wajibi ne kasashen musulmi su yanke alakarsu da ‘yan sahayoniyya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Dole ne kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci da siyasa da gwamnatin ‘yan sahayoniyya azzaluma tare da mayar da ita saniyar ware. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Dole ne a fuskanci bala’o’in da muguwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta haifar a Gaza. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi tsokaci kan mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza inda ya ce: Dole ne kasashen da suke gudanar da zanga-zangar a yau musamman kasashen musulmi su yanke duk wata huldar kasuwanci...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Jami’an kasar suna kiyaye shawarwarin Jagoran juyin juya halin Musulunci Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran. Shugaba Pezeshkian ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a shafin sada zumunta na X cewa: Jami’an zartaswa na kasar suna kiyaye shawarwari da umarnin Jagoran juyin juya halin Musulunci yayin ganawarsa a jiya (Lahadi) da wakilan gwamnati. Ya kara da cewa: Da yardar Allah za a shawo kan matsaloli tare da hadin kan kasa da gwiwar al’umma da taimakon al’umma da kuma saukakawa Jagoran juyin juya halin Musulunci. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new...
    Rundunar sojin Yeme ta sanar da kai hare-hare guda 8 da jirage sama marasa matuka ciki kan muhimman wurare a Isra’ila Dakarun sojin Yemen sun sanar da yammacin jiya cewa, sun kai wasu manya-manyan farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen saman yaki  marasa matuka ciki guda takwas a kan wasu wurare da dama a yankunan Falasdinawa da aka mamaye. An kai hare-haren ne kan filin jirgin saman Ramon da muhimman wurare da na sojoji da suka hada da Negev, Umm al-Rashrash, Ashkelon, Ashdod, da Jaffa. Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta da ‘yan gwagwarmayarsu masoya, da kuma mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba yunwa da makiya yahudawan sahayoniyya suke aikatawa kan ‘yan...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da ke sa ilimi ƙara tsada yayin da yara ke komawa makaranta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Jimilar kudin asusun ajiya na kasar Sin a ketare ya kai dala triliyan 3.3222 zuwa karshen watan Agusta, inda ya karu da dala biliyan 29.9 ko kaso 0.91, idan aka kwatanta da na karshen watan Yuli. Hukumar kula da musayar kudi ta kasar Sin ta alakanta karuwar da tasirin sauyin kudi da sauyin farashin kadarori. Ta kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da habaka yadda ya kamata, cike da juriya da kuzari, da samar da goyon bayan mai karfi ga asusun ajiyar kasar na ketare. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 11 suka jikkata a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai ƙauyen Wake da ke gundumar Agunu, a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna. Hari  ya faru ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiyar ranar Lahadi, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye garin, inda suka yi ta harbe-harbe. Harin Borno: Dole ’yan Najeriya su haɗa kai su fuskanci Boko Haram — Atiku Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna  Har ila yau, sun yi garkuwa da wasu mazauna garin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadinsu ba. Waɗanda suka rasu a harin sun haɗa da: Elisha Paul, Japhet Bitrus, Obadiah Joshua, Luka Augustine,...
    Ministan yakin HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sun yi kokarin kashe jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae a yakin kwanaki 12 amma bayanan da suke da shi ya kasa kaiwa ga manufarsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko wanda HKI take tabbatar da cewa ta yi kokarin mai matsayi mafi girma a kasar Iran, wanda kuma ya kasa kaiwa na sarara. Kazt ya bayyana haka wa tasoshin talabijin ta Chennel 13, Kan da kuma Channel 12, kan cewa sun yo kokari har sau 2 amma bayayan da ke hannummu sun kasa tabbatar da abunda muke nema. Yace da mun sami da mun kasheshi tuni. Bayanan da gwamnatin...
    Ali Akbar Vilayati mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aya. Khaminae ya bayyana cewa, yenci da kuma zaman lafiya da tsaron JMI yana da matukar muhimmanci ga kasar Iran. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Wilayati yana fadar haka a lokacin da yake ganawa da Ammar Hakin shugaban Jam’iyyar Hikma na kasar Iraki wanda yake ziyarar aiki a nan Iran a yau Lahadi. Wilayati ya kara da cewa kasashen Iraki da Iran suna da dangantaka mai muhimmanci tsakaninsu wanda ya hada da na addini da al-adu ga kuma makobtaka. Yace Iran tana jin dadin ganin Iraki tana samun ci gaba da kuma zaman lafiya mai dorewa a karkashin jagorancin malaman addini...
    Na dauki fim sana’a, kuma sana’ar ce. Dan wallahi sana’a ce me kyau ma, ta ba ni gida, ta ba ni mota, na ci, na koshi. Yanzu idan zan shekara na ce ba zan fita ba, a cikin gidana ne, kuma darajar Kannywood. Ina finafinai na a haka na samu gidana, na gina gidan kuma nake zaune cikinsa.   Ko kina da ubangida, a cikin masana’antar Kannywood? Ai ni a masana’antar duk wani sa’a na, ko wanda ya girmen ubangidana ne, ni ba butulu ba ce da zan ce ban da iyayen gida.   Ana rade-radin akwai yaranki a cikin masana’antar Kannywood, mene ne gaskiyar maganar? ‘Ya ta guda daya ce take Kannywood, saboda da kanta ta ce “Umma ina...
    Kazalika, an amince da amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar karo na 12, wanda Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Katsina. Da yake karin haske ga manema labarai bayan taron, kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin gida, Dakta Nasiru Mu’azu Danmusa ya ce, an sanar da matakin ne sakamakon mawuyacin halin da jihar ke ciki, wanda ya kawo babban kalubale ga ababen hawa na yau da kullum wajen shiga wasu yankunan, musamman na karkara da marasa galihu. “Gwamnati ta bayyana matsayinta a fili: tsaro shi ne fifiko na farko, na biyu da na uku na wannan gwamnati shi ne, mun kudiri aniyar magance rashin tsaro baki-daya.” in ji Dakta Danmusa. Baya ga...
    A jawabin da ya yi wa shugabannin sashen sintiri, jami’an ‘yansandan motoci, da sauran jami’an da ke aiki a hedikwatar rundunar, CP ya ce halayen jami’an sintiri a fili suke bayyana hoton da al’umma ke da shi game da rundunar ‘yansanda. Adeh ta bayyana cewa CP ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda jami’ai ke gudanar da ayyuka a halin yanzu, yana mai jaddada cewa kula da zirga-zirga na daga cikin manyan alamomin nuna ci gaban gari. Bayan ya yi yawon duba wurare da dama a birnin a lokutan cunkoso, CP ya gano muhimman wurare kusan 30 da ke da matsalar zirga-zirga, ciki har da Wuse, Area 1 Roundabout, Jikwoyi, Karu, Kurudu, AYA, Apo Resettlement, Gudu, Galadima, Dawaki, da Kubwa....
    Ƙungiyar masu dakon Man Fetur da Gas (NUPENG) ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin kasa baki daya daga ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025, domin nuna adawa da abin da ta kira tsauraran matakan kin amincewa da kungiyar da Kamfanin matatar Dangote ke yi. NUPENG ta zargi kamfanin da daukar direbobin da za su yi aiki da sabbin motocin CNG da aka shigo da su bisa sharadin cewa kada su shiga kowace kungiya a bangaren man fetur da iskar gas. kungiyar ta ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki na Nijeriya, dokar aiki ta ƙasa, da kuma yarjejeniyar kasa da kasa ta ILO kan yancin kafa ƙungiya. Bayanin hakan ya fito ne bayan wani taro da...
    ’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka jami’ai takwas na Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) da ke aiki a kamfanin siminti na BUA da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East ta Jihar Edo. An kai harin na kwanton ɓauna ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Juma’a, 5 ga Agusta, 2025, lokacin da jami’an suka fita raka wasu ma’aikatan kamfanin ’yan ƙasar China guda biyar bayan kammala aikin gadi a ƙofar kamfanin. Wani babban jami’in rundunar a jihar ne ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce ’yan bindigar sun kuma jikkata jami’ai huɗu waɗanda ke karɓar magani a asibiti a halin yanzu.
      Zulum, wanda ya yi matukar takaici da harin, ya gana da shugabannin al’umma tare da jajantawa iyalan wadanda suka rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamandan Sojojin Iran ya jaddada cewa: Dole ne a ko da yaushe Iran ta kasance a shirye don yin yaki Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya jaddada wajibcin kasancewa cikin shiri a ko da yaushe domin yaki, yana mai cewa: A yau sun fahimci yaki da gaba da kuma makircin makiya daidai da yadda suke a baya. Babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya ziyarci rundunonin sojoji a yankunan Isfahan, Tabriz, da Hamadan. A yayin da yake yin nazari kan shirye-shiryen wadannan runduna tare da rakiyar kwamandoji, mayaka, da matukan jirgin sama, ya lura da tsayin daka da al’ummar Iran suka yi wajen tunkarar wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar na tsawon...
    Shugaban hukumar shari’a ta kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ga mulkin kama karya ba Shugaban hukumar shari’a ta Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kaddamar da yaki kan wata kasa ba, kuma ba za ta taba yin hakan ba, to amma ba za ta taba mika wuya ga tsarin mulkin kama karya ba, yana mai cewa: Iran a koyaushe tana taka-tsantsan kan yunkuri da makirce-makircen makiya. A yayin ganawarsa da shugaban kungiyar Hikma ta kasar Iraki Sayyid Ammar al-Hakim, Hujjatul-Islam Gholamhossein Mohseni Ejei a birnin Tehran ya yi karin haske kan irin karfin dangantakar da ke tsakanin Iran da Iraki, yana mai jaddada cewa: Abubuwan...
    Shugaban kasar Tunisiya ya bayyana cewa: Afirka na bukatar sabuwar hanya don tunkarar son ran ‘yan mulkin mallaka Shugaban kasar Tunusiya Qa’is Saeed ya bayyana a ranar Alhamis cewa: Tunisiya tana alfahari da hadin kan kasashen Afirka, kuma ta tsaya tsayin daka kan burin kafa kungiyar tarayyar Afirka mai inganci, duk kuwa da kalubalen da nahiyar ke fuskanta, kamar tashe-tashen hankula, fadace-fadace, laifuffukan safarar bil adama, da rashin samar da muhimman abubuwan rayuwa. A jawabin da ya gabatar a wajen bude taron baje kolin kasuwanci a kasar Aljeriya karo na 4, Saeed ya ce: “Nahiyar Afirka na da dimbin arziki, amma a lokaci guda tana fuskantar talauci da ke sanya matasanta shiga cikin hanyoyin safarar mutane.” Ya ci gaba da...
    Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...