2025-09-19@05:24:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3688

«Allah Ya ba»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Taron koli na Shanghai wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi la’akari da karfafa dangantaka da kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) daya daga cikin manufofin ziyararsa a kasar China da halartar wannan taro. Ya ce, taron kolin na Shanghai wata dama ce mai matukar muhimmanci da kuma dacewa don inganta huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya da sauran kasashe. Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya bayar da safiyar Lahadi a filin jirgin sama na Mehrabad na Tehran kafin ya tashi zuwa kasar China don halartar taron kolin Shanghai: Kasashe mambobin kungiyar Shanghai sun kai kimanin...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada ci gaba da gwagwarmaya soji kan makiya ‘yan mamayar Isra’ila Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Tafarkin al’ummar Yemen na goyon bayan al’ummar Falastinu yana ci gaba kuma tabbatacce kuma yana kara ruruwa. A cikin jawabinsa Sayyed al-Houthi ya ce: ‘Yan kasar Yemen suna fuskantar makiya a dukkan fagage: ta fuskar siyasa, soja, tattalin arziki da kuma ta kafofin watsa labarai, ba za su yi rauni ba sakamakon wuce gona da iri da ake yi kan su. Ya kara da cewa al’ummar kasar Yemen suna yin jawabi da ya hau kansu wajen taimakawa wa al’ummar Falastinu, yana mai bayyana cewa; Suna tare da...
      A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin aiki tare don aiwatar da muhimman ayyukan da suka sa a gaba a karkashin tsarin dandalin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Yu ya ce, kasar Sin ta tafka asarar rayukan sojoji da fararen hula sama da miliyan 35 da kuma asarar tattalin arzikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 600 a lokacin yakin duniya na biyu. Ya yi nuni da cewa, tsayin dakan da kasar Sin ta yi ya yi mummunar wargaza mulkin danniya, tare da ba da gudummawa mai tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A cewar majiyar, kwale-kwalen zai iya daukar fasinjoji 16 ne kacal, amma a zagaye na Uku cunkoson matafiyar ya yi yawa inda wasu mata biyu suka tilasta wa kansu afkawa cikin jirgin inda suka zama fasinjoji zuwa 18, ana kyautata zaton cewa, wannan ne ya yi sanadin kifewar kwale-kwalen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a shafinsa na X , inda yake zargin shuwagabannin kasashen turai da hana tsaida yaki a Ukraine. Dmitriev ya kara da cewa Brussels na zangon kasa ga shirin tsaida yakin tare da dorawa shugaban kasar Ukraine gabatar da bukatun ba zasu taba yiyuwa Rasha ta amince da sub a. Ya kara da cewa shuwagabannin kasashen Turai suna tsawaita yakin har zuwa lokacinda Al-amura zata sake komawa...
    Hadakar ta wuce batun tattalin arziki kadai, domin a bangaren tsaro ma, Rasha ta yi amfani da lalacewar alaka tsakanin kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da kasashen yamma, inda ta samu kutsawa cikinsu.   Ganin yadda yankin ke fama da matsalolin tsaro, sai Rasha ta aika musu da sojojin haya na Wagner domin taimakon kasashen da makamai da horo.   Amma ganin yadda har yanzu kasashen ke ci gaba da fuskantar hare-hare, shin za a iya cewa alaka da Rasha ta yi musu rana?   Sababbin kawayen Moscow Tun a 2021 Rasha ke tura dubban sojoji da makaman da suka kai miliyoyin Dala zuwa Mali da Burkina Faso da Nijar. Tana haka ne domin taimakon kasashen wajen yaki...
    Cibiyar CDC Na Afirka Da WHO Suna Aiki Tare Don Kawo Karshen Cholera Cibiyar Africa Centres for Disease Control and Prevention (Africa CDC) da kuma hukumar lafiya ta Dunita (WHO) sun hada kai don ganin an kawo karshen cutar colera a nahiyar ta Afirk, tare da hada kai da kasashen Nahiyar. Kamfanin yana labarai ta interner Afriva News ya bayyana a ranar Jumma’a kan cewa, shirin wanda yake cikin shirye-shiryen kiwon lafiya na cibiyar Afrika CDC na shekara ta 2025-2026. Sannan manufar shirin itace rage cutar ta Colera da kasha 90  a wannan shekarar, sannan kawo karshen cutar kwata-kwata a kashe 20 na nahiyar nan da shekaru 2030. Cutar colera dai tana kama mutane ne ne saboda shan ruwa marasa...
    Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta dauki danwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu. Bayan da cinikin Eze ya fada, yanzu kuma kungiyar ta Arsenal ta sake mayar da hankalinta wajen sayan dan wasan baya daga kungiyar kwallon kafa ta Bayer Liberkusen, wato Piero Hincapie.   Chelsea Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai hakura da karin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da danwasan RB Leipzig Dabi Simons. Sai dai komai zai dogara ne da yawan ‘yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrikue George, wadanda...
    Ko Mbeumo zai dawo wa United da karsashinta? Dan wasan dan kasar Kamaru Bryna Mbeumo ya zama abin tattaunawa kuma mafi tsada a ‘yanwasan Afirka lokacin da ya koma Manchester United kan fani miliyan 65 daga kungiyar kwallon kafa ta Brentford. Dan kwallon mai shekara 25 ya ci kwallo 20 a gasar da aka kammala da kuma bayarwa a ci bakwai. Manchester United na tsaka da sake gina kungiyar karkashin mai horarwa Ruben Amorim bayan gama gasar a mataki na 15, wanda shi ne mafi muni a tarihin kungiyar na Premier League. Mbeumo zai fuskanci matsi nan take domin ya nuna kwarewarsa tare da Matheus Cunha da Benjamin Sesko wadanda duka kungiyar ta sayo a wannan kakar domin kara karfin...
    Gaskiya dai inda matsalar take shi ne, rashin wayewa da wasu mazan suke da shi, mafi yawa kuma mazan da suke da rashin ilimi su ke da wannan dabi’ar da take ba, dauwamammiya ba. Hakan gaskiya kwata-kwata bai dace ba, saboda an fi so namiji ya auri mai ilimi, wacce za ta tarbiyyantar da ‘ya’ya kan hanya ta gaskiya, da tarbiyya gurin rayuwa ta yau da kullum. Amma idan aka ce mace ba tada wani wayewa to, ba ita kadai za ta zauna cikin wannan rashin wayewar ba, har sai ya kai ga yaran da aka haifa suma su zama cikin duhun kai, su kasa mu’amala da al’umma. Saboda duk mutum wanda yake da rashin wayewa yana tare da tsatstsauran/baudadden...
    A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin. Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin cika shekaru 70 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara mai zuwa, wajen cimma nasarar gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, da kara bayar da gudummawa don wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, da bunkasa ci gaba da walwalar sassan kasa da kasa. A dai yau din, shugaba Xi ya gana da firaministan Cambodia Hun...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma a samu wannan harshen ya ci gaba da yaduwa kamar wake dan arba’in. An taba yin wani shugaban kasa da ya ayyana nazartar wasu darussa a matsayin bata lokaci domin bai ma san a ina za su yi aiki ba. Duk kuwa da kasancewar duk kasar da ya ratsa a Arewacin kasar domin yakin neman zabe, da harshen Hausa yake magana. Abin da nake nufi...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Ba za su ƙyale kowa ya lalata dangantakar abokantaka da ke tsakanin Iran da Armeniya ba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin ganawarsa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin tsaron kasar Armeniya a yau Asabar, ya jaddada cewa: Dole ne su tabbatar da cewa babu wani karfin kasashen waje da zai iya wargaza dangantakar abokantaka tsakanin Iran da Armeniya. Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa, damuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da abubuwan da ke faruwa a yankin Caucasus na baya-bayan nan, musamman kasancewar dakarun kasashen waje a wannan yanki mai matukar muhimmanci, an kawar da su sosai bisa la’akari da fayyace da kuma tabbacin da jami’an kasar Armeniya suka bayar. Ya ce, “Dole ne su...
    Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau. A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da...
    Watan Mayu 1956,aka gabatar da kudurin niyyar yin doka a majalisar Kudu maso gabashin Nijeriya, suka gabatar da kudurin zai bada dama ta a amince da Sarakunan gargajiya, wanda ta haka ne aka samu damar kafa majalisar Sarakunan Kudu maso gabashin Nijeriya, duk kuwa a lokacin da akwai turjiyar da aka samu daga masu fafutukar tafiyar da lamurra yadda suka dace, saboda sun ki goyon bayan a sa su masu Sarautun gargajiya a harkokin yadda ake tafiyar da gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    Har ila yau, wannan ilhama ta tsotsar nonon uwa da ake haifar jarirai da ita, ana kiranta da ‘Sucking refled’, a turancin likita. Kazalika, ilhamar tana fara aiki ne gadan-gadan bayan haihuwa a duk lokacin da kan nonon uwa ya taba saman bakin jariri, wato hanka kenan.   Haka abin yake, idan aka sa wani abu makamancin kan nono; kamar kan yatsa ko kuma fasfaya (pacifier), haka za su rika tsotsa babu ji babu gani, saboda haka aka shirya wa kwakwalwarsu cewa; da zarar kan nono ya dunguri hanka, sai su kama tsotsa kai tsaye.   Don haka, su ma ba aikin kansu ba ne, haka kawai za su ji suna yi ba tare da wani kokari nasu ba, abu...
    Ɗan wasan ɗan shekaru 22 ya zura ƙwallaye 10 ne kawai a wasanni 52 da ya buga a United bara, kuma zuwan Sesko ya ka5ra rage masa damar zama a cikin ƙungiyar. Sha’awar Napoli kan Højlund ta ƙaru ne bayan Romelu Lukaku ya samu rauni a cinyarsa wanda zai sa ya daɗe a jinya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ‘Kun kuduri aniyar kiyaye manyan ka’idojin bin doka domin tabbatar da cewa kowa, har da masu mulki, suna karkashin doka kuma ana iya daukar mataki a kansu. Idan muka yi haka, to mun magance tushen matsalar mulki a wannan kasa,’ in ji shi. Sarkin Musulmi ya jaddada cewa adalci shi ne tubalin zaman lafiyar al’umma, kuma dole doka kullum ta kasance mai nufin cimma adalci a matsayin babbar manufarta. Ya shawarci mahalarta taron da su yi amfani da wannan taro wajen tattauna muhimman batutuwan da suke tsara makomar Nijeriya.” “Ya ce, ‘Ina fatan wannan taro zai ba ku damar tattauna batutuwan da suka shafi makomar al’ummarmu. Abubuwa uku ne manya: Ci gaba da kokari wajen gyaran dokoki domin a hankali...
    Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati. Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar. Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi. Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar...
    “A yayin aikin ceto, wanda aka sace din ya sami raunin harbin bindiga a kafarsa ta hagu bayan ‘yan ta’addan sun bude wuta lokacin da suke kokarin tserewa,” in ji sanarwar.   An garzaya da wanda aka ceto zuwa asibiti, kuma a halin yanzu yana samun sauki.   Kwamishinan ‘Yansanda, Bello M. Sani, ya yaba wa jarumtar jami’an da ‘yan sa-kai bisa saurin daukar mataki, tare da sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da yaki da miyagun laifuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin Jihar Kebbi.   “Wannan aikin ceto ya nuna jajircewarmu wajen kawar da miyagun laifuka a jihar. Ba za mu gajiya ba wajen tabbatar da tsaron kowace al’umma,” in ji Sani.  ...
    Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.”   Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.  ...
    A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas. Hotuna: Bassey Willie            
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya ce ’yan Najeriya sun riga sun yanke shawara kan zaɓen shekarar 2027 da ke tafe. Yayin da yake jawabi a Abuja ranar Alhamis a taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar NNPP, Kwankwaso ya ce: “A yau, yawancin ’yan Najeriya na kokarin yadda za su samu abinci. Wasu sun rasa matsugunansu saboda rashin tsaro. Wasu kuma suna asibiti ba tare da kulawa ta gari ba—ko kuma ba za su iya zuwa ba saboda babu kuɗi a hannunsu. “Mutanen wannan kasa sun yanke shawara kan abin da za su yi a 2027. Shi ya sa muke farin ciki da kanmu—saboda muna tare da jama’a. Kuma jama’a sun san muna tare da su. Ba...
    Bisa wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa, hakan ya nuna cewa, wannan shi ne karo na farko da Asusun Anita na Nijeriya ya samu karuwa tun daga watan Disambar shekarar 2021.   Kazalika, rahoton ya sanar da cewa, a watan Agusta Asusun ya ci gaba da karuwa wanda daga watan aka samu kimanin dala biliyan 1.46 zuwa yau daga dala biliyan 39.54 a ranar daya 19 ga watan Agustar shekarar 2025, suka karu zuwa i dala biliyan 41.00.   Wannan ya nuna yadda karuwar Asusun ta kai zuwa kaso 3.69 a kasa da makwanni uku, da suka gabata.   Bugu da karu, Asusun ya samu wannan karuwar ce, saboda yawan shigowar kudaden musaya na waje cikin kasar da...
    “Wannan mummunan aikin yana nuna gazawar harkokin tsoro da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a karkashin wannan gwamnati ta APC. Kazalika, yana zama manuniya kan tabarbarewar rashin tsaro a kasarmu, wanda ya sa har babban jami’in tsaro na kasa ya yi kira ga ‘yan kasa su koyi kare kansu,” in ji Abdullahi.   Jam’iyyar ta kuma caccaki Shugaba Tinubu kan burus da abubuwan da suka fi muhimmanci, ta zarge shi da mayar da hankali kan al’amuran da suka shafi kasa da kasa mai makon magance rikicin da al’ummar kasar nan ke fuskanta. “Abin takaici ne cewa maimakon fuskantar wadannan mummunan lamuran da wahalar da suka jawo, shugaban kasa Tinubu na ci gaba da tafiya kasashen waje, yana holewa a kasashen ketare,...
    Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja. Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar. Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro. Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi Ya ruwaito...
    Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada bukatar kara azamar inganta da’a a harkokin jam’iyya, da dorewa bisa turbar aiwatar da ka’idojin gudanar da kudurorin nan takwas, na shugabancin jam’iyyar kwaminis game da inganta da’a a harkokin jam’iyyar.   Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya yi tsokacin ne cikin wani umarni da ya bayar, ga wani taron tattaunawa don kara gina jam’iyyar kwaminis a yau Jumma’a a nan birnin Beijing. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shaidu sun ce jirgin cike yake da mata, maza, da yara, kafin ya kife a tsakiyar ruwa. Wasu daga cikin fasinjojin sun yi nasarar yin iyo inda suka tsira, amma har yanzu ba a gano da dama ba. Al’umma sun daɗe suna zargin irin waɗannan hatsari na faruwa ne saboda ɗauke fasinjoji fiye da ƙima, rashin saka rigar iyo, amfani da jiragen ruwa marasa inganci, da kuma rashin bin ƙa’idojin tsaro. Duk da wannan, gwamnati ba ta ɗauki matakan tsaro ba. A halin yanzu, magidanta a Shagari da ƙauyuka maƙwabta na cikin tashin hankali suna jiran labari game da ‘yan uwansu da suka ɓace, yayin da ake ci gaba da zaman ɗarɗar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta bada sanarwan cewa mutun daya dan kasa yayi shahada a yau Jumma’a saboda makami masu linzami wadanda jiragen yakin HKI suka cilla a kan motarsa a kauyen Sair cikin lardin Nabadiyya. Tashar talabijin ta Al-mayaddeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa, sojojin yahudawan sun jefa boma-bomai har guda hudu a kan garin Kafar Kila a kudancin kasar ta Lebanon. Labarin ya kara da cewa a garin kafar kila, sojojin yahudawan sun kai hare hare da dama a yau Jumma’a bayan wadanda muka bayyana amma basu kai ga kashe ko raunata wani ba. A jiya Alhamis ma jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hare hare a wurare da dama daga...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ta kafa kwamitin bincike mai ƙarfi na ƙwararrun jami’an tsaro tare da haɗin gwiwar rundunar ‘sojan Najeriya, domin gano abin da ya jawo aka kashe wani jami’in soja da wani sifeton ’yan sanda ya yi a jihar kwanan nan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), CSP Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin Kwamishinan ’yan sandan, Sani-Omolori Aliyu a hedikwatar rundunar da ke Bauchi a ranar Juma’a. Na bar APC saboda Tinubu bai cika alƙawarin da ya yi ba — Marafa An kama wani mutum da laifin kashe mahaifiyarsa kan zargin maita Wakil ya ce, an ɗora wa kwamitin alhakin tattarawa da...
    Kasar Sin ta gabatar da ‘yancin samun ci gaba a matsayin hakkin dan Adam mafi muhimmanci. Ta hanyar dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), ta zuba jari mai yawa a fannin samar da ababen more rayuwa, da cinikayya, da fasahohi a fadin nahiyar Afirka. Ayyuka irin su hanyar dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti, manyan tituna, tashoshin ruwa da wutar lantarki, gadojin kan hanyar ruwa da masana’antu, duk wadannan an tanade su ne don su zama hanyar rage talauci da tallafawa al’umma. Ta hanyar inganta yanayin rayuwa da samar da damarmakin tattalin arziki, kasar Sin ta yi nuni da cewa, tana kara karfafa martabar jama’ar Afirka ta hanyar samar musu da ci gaba.   ’Yancin Cin Gashin...
    Osuman ya koka kan yadda a kowace rana ake kashe rayukan mutane a yankin, ya kara da cewa, yara, mata, maza, tsofaffi duk sun fada cikin matsalolin ambaliyar ruwa, ta’addancin ‘yan bindiga dadi, ayyukan ‘yan ta’adda da sauran annobobi.   Ya bukaci shugabannin arewa da mazauna yankin da su farka, su hada kawunansu kana su dukufa da yin addu’o’in neman zaman lafiya a yankin.   Da yake magana da kafar BBC bayan taron, mai ba da shawara ga ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, kungiyar ta yi nazari da bitar matsalolin da suke addabar arewa tare da cimma matsayar cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa.   “Matsalolin nan ga su nan a zahirance, kuma dole ne a tursasa gwamnati ta...
    Da aka tuntubi Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed mai ritaya, ya tabbatar da faruwar al’amarin, amma ya ce; jami’an tsaro sun shawo kan lamarin.   Haka zalika, mazauna Ndanaku da ke Karamar Hukumar Patigi a Jihar Kwara, sun kauracewa wurin sakamakon hare-haren ‘yan bindiga. Kazilika, harin na zuwa ne makwanni kadan bayan faruwar makamancin haka a garin Babanla da ke Karamar Hukumar Ifelodun.   Kwamandan ‘yan banga, Gina Gana; wanda shi ma yana daya daga cikin wadanda suka tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa; an kai hare-hare guda biyu ne kwanaki uku da suka gabata, wanda ya tayar wa da kowa hankali a garin.   Har wa yau, a makon day a gabata ne Gwamna...
    Kungiyar Marafa ta kuma zargi gwamnatin Tinubu da watsi da tsarinsa na siyasa da kuma rashin tallafawa al’ummar da ke fama da matsalolin tsaro. Daga ƙarshe, ta bayyana cewa Marafa da dukkan magoya bayansa a kananan hukumomi da mazabu 147 na Zamfara sun fice daga APC, kuma nan gaba za su bayyana sabon matsayar siyasar da za su bi.     —   Wannan sigar za ta fi ja hankalin masu karatu a yanar gizo. Kana so in ƙara ƙaramin taken ƙasa (sub-headline) da ke ƙara jan hankali, irin na jaridu, misali: “Tsohon Sanatan Ya Ce Zamfara Ta Fi Kowa Fama da Sace-Sace Amma Gwamnati T a Yi Watsi da Ita”?   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Duk da yawan wadanda aka gano suna dauke da cutar, jami’an kiwon lafiya sun bayyana irin ci gaban da ake samu. Daraktan kula da lafiyar al’umma a ma’aikatar lafiya ta tarayya, Dakta Godwin Ntadom, ya bayyana cewa; Nijeriya ta samu sanarwar bullar cutar tarin fuka mafi yawa a 2024, inda ta gano sama da mutum 400,000 da ke dauke da cutar, kwatankwacin kashi 79 cikin 100 na masu jinyar.   Haka nan, akwai yara da dama wadanda ke dauke da cutar ta TB, amma ba a gano ba. Kazalika, yaran da aka gano suna dauke da cutar, yawansu ya karu daga 8,293 a 2018 zuwa 43,000 a 2024, in ji shi.   Duk da haka, Ntadom ya bayyana cewa; tarin...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a 2023, Peter Obi, ya soki gwamnatin tarayya kan ƙarin kuɗin fasfo da aka sanar cikin makon nan. Ya bayyana cewa wannan ƙarin ya nuna rashin la’akari da halin da talakawa ke ciki a yau. A cewar Obi, sabon farashin fasfo na – ₦100,000 mai shafuka 32 da ₦200,000 mai shafuka 64 – ya fi sabon albashin ƙasa na ₦70,000, abin da ya ce bai dace ba da halin da ma’aikata ke ciki. Ƴansandan Libya Sun Kama Ƴan Nijeriya Biyu Kan Zargin Fashi Hukumar Shige Da Fice Ta Ƙara Kuɗin Fasfo Zuwa N100,000, N200,000 Ya zargi gwamnati da ƙara ƙaƙabawa jama’a ƙarin nauyi maimakon sauƙaƙa musu, musamman a lokacin da tattalin arziƙin...
    Yana mai cewa: “Da yawa yanzu an manta zaurance ko ba a yi, saboda yanayin yadda zamani yake. Amma a da, musamman ma idan ka je wajen da ka ga sun iya Hausa kuma su ba Hausawa ba ne, za ka iya juya harshe ta amfani da zaurance wajen canza yaren ba tare da wanda ka ke tare da shi ya fahimci me kake faa ba.”   Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a (CAS), Dakta Sunusi Yakubu Ahmed, ya bayyana jin dadinsa matuka bisa zabar kwalejin don gudanar da wannan taron.   Dakta Sunusi ya ce: “Tun lokacin da na ga an yi irin wannan taron a Jami’ar Northwest, na bukaci nima ina da burin...
    Masu shirya taron sun dauki lokacin ana shirye-shiryen garin taron ta yi armashi da kuma nasara musamman saboda gayyato baki da aka yi daga makwabciyar kasar wato jamhuriyar Nijar.   Kasancewar masarautar Daura na da alaka da aka al’adun gargajiya an shirya kasaitaiccen bikin wanda ya burge mahalarta taron musamman baki.   Masu shirya taron sun kara da cewa dalilin da ya sa suka zabi masarautar Daura domin shirya wannan taron shine saboda kasancewar Daura tushen Hausa da al’adu hausawa. Haka kuma an shirya wani tattaki daga Katsina domin zuwa Daura karkashin hukumar raya al’adu ta jihar Katsina inda aka shafe kwana biyu ana tafiya akan dawakai zuwa garin na Daura duk a cikin shirye-shiryen bikin ranar Hausa ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.   Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
    Har ila yau, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta bayyana cewa; an fara bincike kan hatsarin da jirgin kasan daga Abuja zuwa Kaduna ya yi a garin Asham da ke Jihar Kaduna.   Hukumar ta ce, binciken zai gudana ne karkashin kulawar hukumomin da abin ya shafa tare da sa ido daga ma’aikatar sufuri ta tarayya, domin kokarin gano musabbabin faruwar al’amarin.   A cikin sanarwar da NRC ta fitar a yammacin ranar Talata, ta bayyana cewa; jimillar mutum 618 ne suke cikin jirgin a lokacin da ya sauka daga kan hanyarsa.   Kazalika, hukumar ta bayyana cewa; daga cikin fasinjojin, mutum akalla 14 ne suka samu raunuka daban-daban, sannan kuma an garzaya da su asibiti. Sauran fasinjojin kuma,...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dangantaka tsakanin Iran da China na dauke da dabarun manufofi masu kyau Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Kasar Iran na da sha’awar gudanar da hadin gwiwa mai ma’ana da kasar China, musamman a fannin raya dabarun kiyaye hanya, yana mai bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a matsayin kyaukyawar dabara. Shugaba Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Alhamis don daidaita yin nazari kan fannoni daban-daban na dangantaka da hadin gwiwa, da kuma bayyana ajandar ziyarar shugaban kasar China. Taron ya samu halartar manyan jami’ai da shugabannin hukumomin zartarwa da abin ya shafa. A yayin wannan taro, an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi...
    Jami’in kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: A shirye suke su ci gaba da yaki na dogon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila Jami’in kungiyar Ansarullah ta Mabiya Huthi ta kasar Yemen Mohammed al-Bukhaiti ya bayyana cewa: A shirye al’ummar Yemen su ci gaba da yaki na tsawon lokaci da gwamnatin mamayar Isra’ila, kuma suna farin ciki da arangama kai tsaye da haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa, za a ci gaba da daukar matakan soji na goyon bayan Gaza muddin gwamnatin ta ci gaba da yakin da take yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa harin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan birnin Sana’a ba zai shafi goyon bayan da al’ummar Yemen ke yi ga...
    Yanzu haka a nan kasar Sin ana ta shirye-shiryen gudanar da babban bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yaki da mamayar sojojin Japan, da nasarar yakin kin tafarkin murdiya, wanda shi ma wani lokaci ne da zai dada tabbatarwa duniya zahirin abubuwan da suka wakana, tare da karyata sassan dake kokarin lullube gaskiya, da kaucewa daukar alhakin ta’asar da aka aikawa al’ummar Sin a yayin mamayar birnin Nanjing. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp ShareTweetSendShare Previous Post Manyan Jami’ai A Ma’aikatar Tsaro Ta...
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci.   Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
    An kafa ta a cikin 1955 kuma tana da hedikwata a Tokyo, IAPH kungiya ce ta duniya mai dauke da tashoshin jiragen ruwa fiye da 190, kuma tana gudanar da kasuwanci a cikin ƙasashe 89.   Mambobin kungiyar IAPH suna kula da sama da kashi 60 cikin 100 na cinikin teku da kwantena na duniya. Kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin tekun duniya, tare da yin aiki kafada da kafada da Hukumar Kula da Teku ta Duniya, Hukumar Kwastam ta Duniya, da tsarin Majalisar Dinkin Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    A yau Alhamis aka bude bikin nune-nune na masana’antar manyan bayanai ta Big Data, a birnin Guiyang na lardin Guizhou dake kudu maso yammacin kasar Sin. Taken bikin na bana shi ne “Karfafa masana’antu ta hanyar bayanai, ingiza ci gaba ta hanyar basira” wanda ya kunshi rumfuna 6 da suka hada da na amfani da kirkirarriyar basira wajen yanke shawara da kayayyakin more rayuwa da hidimomi da manhajoji da bude ido da kirkire-kirkire, dukkansu masu amfani da fasahohi na zamani, wanda ya hada kamfanoni 375 na cikin gida da ketare. Yayin da Sin ke tsaka da zurfafa aiwatar da shirin “AI Plus” mai ingiza amfani da fasahar AI a bangarori daban-daban, taron ya nuna sabbin nasarorin da aka samu wajen...
    Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce daga watan Junairu zuwa Yulin bana, darajar abubuwan da Sin ta shigo da su kasar daga kasashe masu karancin ci gaba na Afrika, ta kai dala biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 kan na bara.   Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, inda ta ce wani rahoto da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, karkashin jagorancin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ya zama wani muhimmin karfi mai ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar. Ta ce cinikayya tsakanin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun  DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi. A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki  wadanda ake sarrafasu daga nesa. Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa...
    3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka. Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci. Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na...
    ’Yan Majalisar Dattawan kasar Mexico sun yi naushe-naushe a ranar Laraba lokacin da muhawara ta yi zafi a zauren majalisar. Rahotanni sun ce an fara ba hammatar iska ne bayan shugabannin ’yan adawa a majalisar sun bukaci sojojin Amurka su shiga kasar su taya su yaki da dillalan miyagun kwayoyi. Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare Shugaban marasa rinjaye a makalisar, Alejandro Moreno, shi ne dai ya je wajen yin jawabi a fusace bayan kammala zaman majalisar, inda ya tunkari shugaban majalisar, Gerardo Fernandez Norona, saboda hana shi damar yin Magana. A cikin wani bidiyo a kafafen sada zumunta dai, an ga...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Ofone Modupe Alasin, a karamar hukumar Efon-Alaaye da ke jihar. Kakakin rundunar a jihar, SP Sunday Abutu ne ya tabbatar da kisan matar, inda ya ce an kama mijinta yayin da ake ci gaba da bincike. ’Yan sanda sun ceto yara 3 da aka sace a Kaduna Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai Binciken farko-farko dai ya nuna mijin ne ya lakada wa matar tasa duka saboda ta ki zuwa gonarsu a kan lokaci. Wani makwabcin gonar ya ce ya jiyo marigayiyar tana ihun neman taimako, amma duk da haka mijin nata ya ci gaba da nada mata na jaki. Kazalika,...
    Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna  ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr dake kudancin kasar Iran. A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na X, Ulyanov ya rubuta cewa: Iran ta sake tabbatar da cewa, ko da bayan hare-haren da sojoji suka kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarta na zaman lafiya da ke gudana karkashin hukumar ta IAEA ba bisa ka’ida ba, abin kunya ne, a matsayinta ta mamba ta hukumar...
    Jami’ar kasa da kasa a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ta ce: Kananan Yara masu fama da yunwa a Gaza suna mutuwa sannu a hankali Inger Ashing, shugabar kungiyar Save the Children, ta tabbatar da cewa: “Yaran Gaza da ke fama da yunwa sun kai ga mataki mai tsanani,” inda ta bayyana dalla-dalla kan mutuwarsu a hankali, kuma sun kai ga matakin da ba su iya yin kuka. Inger Ashing ta fadawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba cewa: Yunwar da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a Gaza a makon da ya gabata, ba wai kawai “kalmomi ne na fasaha ba,” ta kara da cewa: “Lokacin da babu isasshen abinci, yara suna fama da rashin abinci mai...
    Rahoton yahudawan sahayoniyya ya tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa dakile hare-haren dakarun Yemen Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Jerusalem Post ta bayyana a cikin wani rahoto na baya-bayan nan cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fama da babbar matsala ta soji da tsaro, bayan da ta kasa dakatar da hare-haren da Yemen ke kai mata hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki tun daga ranar 19 ga Oktoban shekara ta 2023. Jami’an gwamnatin mamayar Isra’ila sun bayyana bangaren Yemen a matsayin “wanda ya fi kowa hauka a yankin,” suna masu gargadin cewa shiga fafatawar da suke yi da su zai haifar da mummunan sakamako ga haramtacciyar kasar Isra’ila, ganin yadda suke ganin dakarun Yemen...
    Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ta ceto wasu yara guda uku da aka sace tare da kama mutum uku da ake zargi da sace su. A ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, wani mutum ya kai rahoton cewa an sace ’ya’yansa uku. An kashe mutum 3 a faɗan ƙungiyoyin asiri a Legas ’Yan bindigar da suka sace ma’aurata a Katsina na neman N600m Yaran sun haɗa da Aslam Umar Lukman mai shekaru 14, Suleiman Umar Tanko mai shekaru 12 da Aliyu Umar Tanko mai shekaru 10. Waɗanda suka sace yaran sun nemi a ba su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa. ’Yan sanda sun yi amfani da dabaru inda suka cafke shugaban ƙungiyar, Richard Philip. Yayin bincike, ya...
    Bayan samum rahotom faruwar lamarin, jami’an tsaro suka bazu cikin dazuka domin ceto waɗanda suka sace. Kwamishinan ’yansandan jihar, Monday Agbonika, ya jagoranci aikin a kan titin Benin zuwa Akure. Ya ce sun yi amfani da sabbin fasahohi ciki har da jirage marasa matuƙa, wanda ya taimaka wajen samun nasara. Agbonika ya yaba wa jami’an ’yansanda, sa-kai, da mafarauta bisa haɗin kai, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa shi ne mabuɗin magance manyan laifuka. Ya tabbatar wa jama’a cewa za su ci gaba da aiki har sai an ceto sauran mutanen da aka sace kuma an kama maharan. “Mun ƙuduri aniyar kawar da miyagun laifuka daga titunanmu da al’ummominmu, kuma za mu yi amfani da dukkanin kayan aiki na fasaha...
    An kai shi asibiti, inda aka kula da shi sannan aka sallame shi domin halartar jana’izar iyalan nasa. Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA), Bello Garba, ya ce ba su samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba, amma sun shirya gudanar da bincike kan lamarin. An binne mamatan bisa tanadin addinin Musulunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan bindigar da suka sace wani mutum, matarsa da ’yarsu a Jihar Katsina, na neman Naira miliyan 600 a matsayin kuɗin fansa. Wanda aka sace sun haɗa da Anas Ahmadu mai shekara 33, matarsa Halimat, da kuma ’yarsu Jidda. Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-Rufai NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi An sace su ne a gidajensu da ke Filin Canada Quarters a Sabuwar Unguwa, cikin garin Katsina da safiyar ranar Talata. A yayin kai harin, wani ɗan sa-kai mai shekara 25 mai suna Abdullahi Muhammad, ya rasu lokacin da yake ƙoƙarin ceto su. Wani ɗan uwan ma’auratan ya shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutane da dama ba sa sanin suna dauke da ciwon suga ballantana su san hanyoyin magance shi kafin ya yi tsanani. Sau da yawa ciwon sai ya kai wani matakin da zai yi wa mutum illa sannan yake sanin yana dauke da shi. NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan matakan da ciwon suga ke bi kafin ya yi tsanani da kuma hanyoyin magance shi. Domin sauke shirin, latsa nan
      Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a.   Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya...
      Ya kuma jaddada cewa, ya kamata kasar Sin ta himmatu wajen shigo da ayyukan hidimomi masu matukar inganci, da yin amfani da ingantaccen tsarin bude kofa ga waje don inganta masana’antun gudanar da hidimomi na cikin gida, da hanzarta bude kofar hukumomi a fannin hada-hadar gudanar da hidimomi.   Li ya ce, za a yi kokarin samar da kyakkyawan yanayi na shigo da ayyukan hidimomi, da kyautata tsarin kula da manyan iyakokin kasa, da karfafa yadda ake kula da bayanai na iyakokin kasar cikin tsari. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Wannan na zuwa ne bayan samun labarin kama wata mai suna Maryam Hussain Abdullahi a Saudiyya da zargin fataucin miyagun ƙwayoyi a daidai lokacin da take aikin Umara.   Da yake bayyana yadda aka bankaɗo harƙallar ta hanyar, wadda ke jefa mutanen da ba su ji, ba su gani ba cikin masifa, ya ce ‘yan uwan wadanda aka kama ne a Saudiyya ne suka kawo ƙorafi ga hukumar NDLEA cewa an kama ’yan uwan su a Saudiyya, inda cikin gaggawa hukumar ta ƙaddamar da bincike.   “’Yan Nijeriya da aka kama a Saudiyya su ne: Maryam Hussain Abdullahi da Abdullahi Bahijja Aminu da Abulhamid Sadiq waɗanda suka hau jirgin Ethiopian Airline mai lamba ET940, wanda ya bar Kano a ranar...
    Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a kan babban titin da ke shiga garin tare da rike hotunan shahidan Hizbullah, da kuma wasu hotuna wadanda suke kiran jakadan da suna “Dabba” ya sa Barrack ya fasa ziyarar. Tom Barrack yana daga cikin jami’an gwamnatin Amurka suke son tilastawa shuwagabannin gwamnatin kasar Lebanon, sun kwance damar kungiyar Hizbullah na kasar da karfi. Hizbullah wacce ta dauki shekaru tana hana HKI shiga kasar kasar....
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci rashen rundunar Qudus tare da hadin kai da hukumar leken asiri na JMI da kuma yansandan kasa FRAJA sun sami nasar aiki tare a garuruwan Iranshahr, Khash, da kuma Saravan na yankin sistan baluchestan, inda suka halaka yan ta’adda har 13 sannan suka kama wasu da ransu suna kuma gudanar da bincike a kansu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa daga wadannan garuruwa uku ne yankin Sistan Baluchestan ne mafi yawan yanta’adda wadanda suke samun tallafin kasashen waje suke amfani da su don kawo hare-hare cikin lardin wadanda suka kai ga shahadar Jami’an tsaro da dama da kuma wasu fararen hula. Jami’an tsaron sun kai sumamayen ne a safiyar yau...
    Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a kan babban titin da ke shiga garin tare da rike hotunan shahidan Hizbullah, da kuma wasu hotuna wadanda suke kiran jakadan da suna “Dabba” ya sa Barrack ya fasa ziyarar. Tom Barrack yana daga cikin jami’an gwamnatin Amurka suke son tilastawa shuwagabannin gwamnatin kasar Lebanon, sun kwance damar kungiyar Hizbullah na kasar da karfi. Hizbullah wacce ta dauki shekaru tana hana HKI shiga kasar kasar....
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD (OHCHR) ta bayyana cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 982 a yankin yamma da kogin Jordan tun cikin watan Octb. Shekara ta 2023. Wannan banda wasu 42,000 da suka tilastawa barin gidajensu daga yankin. Banda haka sun rusa gidajen shaguna da sauran abinda Falasdinawa suka mallaka. Banda haka yahudawan da suke yankin suna kai farmaki kan Falasdinawa a yankin, inda suke kashe wasu Har’ila yau kungiyar red cross ta bayyana cewa ta sha jinyar wasu Falasdinawa a yankin Yamma da kogin Jordan wadanda suka sha hayaki mai guba wanda sojojin HKI suke jefa masu a yankin, Labaran sun kara da cewa a yau laraba sojojin yahudawan sun kai hare haren kan Falasdinawa a Nablus...
    Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa.   Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu.   Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje.   Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari  ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
    ’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari  ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU Maharan sun shiga yankin ne ta ɓangaren Katsina ɗauke da bindigogi, inda suka dinga harbi a sama. Sun harbe wani mutum mai suna Aminu Shehu har lahira, sannan suka yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Shehu Dakin. Majiyoyi, sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da wayar Alhaji Shehu wajen kiran iyalansa,...
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa. Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don...
    Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar tun shekara ta 2023 da ta gabata Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar a ranar Talata, tun bayan barkewar yaki a kasar a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023. Kamfanin dillancin labaran Sudan ya bayar da rahoton cewa, “Gwamnatin bege” karkashin jagorancin fira ministan kasar Kamil Idris, “ta tattauna, a zamanta na farko na hukuma a birnin Khartoum bayan kafuwarta, game da tsare-tsaren ma’aikatun na wannan shekara, inda suka mai da hankali kan ayyukan jama’a da rayuwar jama’a, tsaro na ‘yan kasa, sake gina kasa, da tabbatar da dawowar ‘yan kasar da suka yi gudun hijira bisa radin kansu....
    Gwamna Uba Sani ya umarci jami’an tsaro da su kamo waɗanda suka aikata laifin tare da wanzar da zaman lafiya. Jami’ai sun ce jihar ta samu zaman lafiya sosai cikin shekaru biyu da suka gabata sakamakon Kaduna Peace Model, wanda ya rage rikice-rikice tare da sake ba da damar zuwa gonaki da kasuwanni a wuraren da aka daɗe ana fama da rikici. Sai dai sun yi gargaɗin cewa rashin tsaro daga jihohin maƙwabta na yawan zuwa cikin Kaduna, don haka ana buƙatar gwamnatoci na jihohi su haɗa kai domin kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa NRC ta dakatar da jigilar jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja Rahotanni sun ce an kai harin ne wajen misalin ƙarfe 3:00 na daren Litinin inda maharan suka sace magidancin mai suna Malam Anas tare da matarsa mai suna Halimatu ​​da ’yarsa. Bayanai sun kuma nuna wani dan bangar da yayi ƙoƙarin kai musu ɗauki ya rasa...
    A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Ci Gaban Da Harshe Da Al’adun Hausa Suka Samu A Shekaru 10 DAGA LARABA: Yadda wasu tsare-tsaren ba da tazarar haihuwa ke yin illa ga mata Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a ranar 9 ga watan Agusta yayin da suke kiwon shanu. ‘Yansanda sun ce sun ƙwato makamai da harsasai daga hannun ‘yan bindigar, tare da alƙawarin ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya kaddamar da shirin dashen bishiyoyi na shekarar 2025 a Damaturu babban birnin jihar. Gwamna Buni ya kuma yi gargadi game da sare itatuwa ba gaira ba dalili, yana mai jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta amince da ayyukan da za su sanadin kwararowar hamada da lalata muhalli ba. Da yake jawabi a wurin bikin mai taken: “Shirin Buni na dakile kwararowar hamada” Gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da kwararowar hamada, da raya gurbatacciyar kasa, da dakile illolin sauyin yanayi. Ya yi nuni da cewa, tun daga shekarar 2020, gwamnatin jihar Yobe ta dasa miliyoyin itatuwa iri-iri a fadin jihar domin dakile kwararowar hamada daga kudancin Jihar. Daga kanmu,...
    A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi. A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban. A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a watan Satumban bara a Beijing, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakarsu. Firaminista Li ya ce yana fatan...
    Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
      A nasa bangaren Volodin ya ce, a karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, dangantakar Rasha da Sin ta ci gaba da zurfafa cikin nasara. Majalisar dokokin Rasha ta himmatu wajen aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomin dokokin kasashen biyu, da kuma himmatuwa wajen samun karin sakamako mai kyau a dangantakar kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an kawo jami’an tsaro a yankin don tsaron fasinjojin. Kamfanin jiragen kasa na kasa wato ‘The Nigerian Railway Corporation (NRC) bai bada wani bayani kan al-amarin ba har zuwa lokacin bada wannan labarin. Saukan jirgin daga layin dogon dai bai jiwa wani rauni ba, kuma babu wanda ya rasa ransa. A cikin watan mayun shekara ta 2024 da ya gabata ma, an sami...
    Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci.   A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko da su guji siyasantar da al’amuran tsaro, yana mai cewa: “Wannan ƙalubale na gama gari ne, ba wai na shugabanni kaɗai ba. Domin haka nake kira ga al’umma da shugabanni su daina siyasantar da tsaro.”   Ribadu ya ƙara da cewa, gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, za ta ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin magance barazanar tsaro tare da kawo...
    Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.   “Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari, duk wanda ya samu rauni za a kula da shi cikin gaggawa, yayin da ake ba da tallafin gaggawa na psycho-socio da tallafin likita ga wadanda abin ya shafa,” in ji Maiyaki.   Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na sanya ido sosai kan lamarin tare...
    Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar Viktor Gyokeres da Eberechi Eze, baya ga waɗanda ta ke da su kamar Gabriel Martinelli, Leandro Trossard, Ethan Nwaneri da Max Dowman don rage giɓin Saka da Odegaard. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta sake duba matsayar ta, inda suka ce kasuwar ce tushen rayuwarsu da iyalansu, kuma rushe ta zai kara jefa su cikin talauci da rashin aikin yi. Haka kuma, sun yi barazanar kai ƙarar gwamnati kotu idan aka ƙi biyan su diyya, domin a cewarsu, an tauye musu haƙƙin kasuwanci da kuma dukiyar da suka shafe shekaru suna tarawa. Sai dai gwamnatin Legas ta ce irin waɗannan ayyuka na rusau na daga cikin shirinta na zamanantar da manyan kasuwanni, don su dace da tsarin birane na zamani da kuma kare muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sauka daga kan titi. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tarogon jirgin kasan sun mirgina a yayin da fasinjoji suka shiga tashin hankali.
    A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin bikin Ranar Hausa ta Duniya. Ga kadan daga cikin hotunan yadda kasaitaccen bikin ke gudana.                      
    shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai yafe jinkirin yin Allah wadai da bala’in Gaza ba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: “Al’umma ta tuna cewa bala’in Gaza bai shafi musulmi kadai ba, wannan lamari ne na gwaji na lamiri na dukkanin bil’adama, don haka suna kira ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da addini ko yanayin kasa ba, da su tsaya a bangaren bil’adama, adalci da mutunci, wato a bangaren dama na tarihi.” Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron baje kolin na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, inda ya yi jawabi ga...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tun bayan barkewar yakin da Iran, babu wata hulda da ta hada ta da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya jaddada cewa: “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a shawarwari,” yana mai bayanin cewa: “Tun bayan barkewar yaki da Iran, kasar Iran ta daina yin mu’amala da Amurkawa, amma tana ci gaba da hulda da Turawa ko da a lokacin da ake tsaka da yakin.” A wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung ta Jamus dangane da shawarar da Turai ta gabatar na tsawaita wa’adin aiki da hanyar da za a bi wajen ganin an dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen...