2025-05-02@05:34:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1552

«Allah Ya ba»:

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: An dage zaman tattaunawan Iran da Amurka ne bisa shawarar kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi nuni da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Oman ne ya sanar da sauyin lokacin zaman tattaunawan ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayanin cewa, dage shawarwarin ya zo ne bisa shawarar ministan harkokin wajen kasar, kuma za a sanar da wata sabuwar rana daga baya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da manema labarai cewa: An canja ranar da za a gudanar da zaman shawarwarin ba na kai tsaye ba na gaba tsakanin Iran da Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a...
    Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya. Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijira falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi Allah wadai da matsayin Amurka na goyon bayan haramtacciyar kasar Isra’ila kan haramta hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da ayyukan ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA”, tana daukan wanan a matsayin Amurkia na ci gaba da nuna son kai da goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya da kuma rashin mutunta dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar jin kai. A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar jiya Alhamis, kungiyar Hamas ta yi nuni da cewa: Shigar da Amurka...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    Haka kuma, kasar Sin ta yi nuni da cewa, matakan kasar Amurka kan harajin kwastam sun kawo illa ga cinikayyar duniya, da moriyar kasashe masu tasowa, amma kasar Sin a nata bangaren kokari take yi wajen tabbatar da bunkasar cinikayya ta duniya, da kuma tsayawa tare da kasashe masu tasowa. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Faɗin ginin, wanda ya haura sukwaya mita 13,000, ya ƙunshi babban ginin tashar da ababen da ke tattare da shi, kuma zai kasance tashar da ta fi kowace girma a layin dogon da ake kira Kaka Reluwe.   Kaka Reluwe na nufin hanyar dogo daga KAduna zuwa KAno.   Kamfanin CCECC ya ce idan an gama aikin, zai taimaka gaya wajen haɓaka harkokin sufuri kuma ya kawo matuƙar sauƙi ga miliyoyin matafiya a ɓangaren Kano na hanyar jirgin.   Shi dai wannan layin dogo na Kaka Reluwe, hanya ce mai tsawon kilomita 204. Ta tashi daga Kaduna, ta bi ta Zariya, zuwa Kano.   Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya ƙaddamar da ita a ranar 15 ga Yuli, 2021, sannan...
    Gwamnan ya kara da bayyana biyan Biliyan 16 na basussukan fansho, da kuma sauya mafi karancin fansho daga ₦5,000 zuwa ₦20,000, da kuma fitar da Naira miliyan 100 domin tallafawa ayyukan ’yan fansho.   A wani mataki makamancin haka, gwamnan ya sanar da kafa sabbin ma’aikatu 4 da hukumomi 2 da za su zaburar da samar da ayyukan yi da kirkire-kirkiren fasaha a jihar.   Wadannan sun hada da ma’aikatun raya gidaje, tsaron cikin gida, daskararrun ma’adanai, da wutar lantarki da makamashi mara illa, sannan kuma ya kafa hukumomar bunkasa ICT ta jihar Kano da hukumar kula da kanana da matsakaitan masana’antu.   Gwamna Yusuf ya kuma ba da sanarwar umarnin fara aiwatar da shirin mafi karancin albashi na ₦71,000...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa. Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko  Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar....
    Zargin sabani tsakanin Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba, ya karu a yau Alhamis bayan da mataimakin gwamnan ya kaurace wa bikin Ranar Ma’aikata a birnin Minna, babban birnin jihar. LEADERSHIP ta ruwaito cewa Kwamred Garba, wanda shi ne tsohon shugaban reshen jihar na ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), bai taɓa kin halartar bikin Ranar Ma’aikata ba tun bayan da ya zama mataimakin gwamna. Sabanin shekarar da ta gabata, Kwamred Garba bai bayyana a wannan shekarar ba duk da cewa Gwamna Bago da Sanata mai wakiltar mazabar Neja ta Gabas, Sani Musa, sun halarta, lamarin da ya ƙara zafafa zargin rikici tsakaninsa da gwamnan. Wasu majiyoyi sun ce yana wajen gari, yayin da wasu ke...
    Babu tabbacin ko ya rasu sakamakon rashin lafiya ko kuwa an kashe shi. An ce ‘yan bindigar sun fara neman Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa, amma iyalansa sun iya haɗa Naira miliyan 11 ne kacal. Sun kuma buƙaci sabon babur da kayan abinci, duk a matsayin kuɗin fansa. Bayan da matar da ta tsere ta shaida wa jama’a abin da ya faru a ranar Litinin, sai aka yi masa sallar jana’iza a ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Rundunar ‘yansandan Jihar Zamfara, ta bakin kakakinta DSP Yazid Abubakar, ta ce har yanzu ba ta samu labarin tabbacin mutuwar limamin da iyalansa daga hukumomi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kai wannan mataki ne bayan lashe Copa del Rey a wasan ƙarshe da Real Madrid a filin wasa na La Cartuja a Seville. Yamal ya fara buga wasa a Barcelona a shekara ta 2023, inda ya fara a gasar La Liga a wasan da suka buga da Betis, yana da shekaru 15 da watanni tara a lokacin. Tun daga wannan rana, ya ci gaba da kafa tarihi a ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Amma shugaban EFCC ya ce hakan ba gaskiya ba ne. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sakataren Majalisar koli ta tsaron kasar Iran wanda ya halarci taron kungiyar “Brics” a kasar Brazil ya bayyana cewa; Makaman Nukiliya ba su cikin akidar tsaron kasar Iran. Ali Akbar Amhadiniyan ya kuma kara da cewa; Iran ba za ta amince da kin aiki da hakkokinta na cin moriyar fasahar makamashin Nukiliya a fagagen zaman lafiya ba. Da yake Magana akan Falasdinu kuwa, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya ce: “Amfani da karfi domin kai wa ga sulhu” da “Diflomasiyya ta dole” akidun siyasa ne masu hatsarin gaske, yana mai kara da cewa; ta hanyar shimfida adalci ne ake kai wa ga sulhu,haka nan kuma yin furuci da hakokin da suke halartattu. Akan barazanar da wasu kasashe suke...
      Cikin adadin, masu bayyana ra’ayoyi daga kasashen Saudiyya da Serbia, suna cikin mafiya bayyana matukar baiken matakin na Amurka, da karin kaso 28.5 bisa dari. Yayin da a daya bangaren al’ummun Malaysia, da Isra’ila, da Australia, da Singapore, da Philippines, da Najeriya, da Portugal, da Pakistan, da Afirka ta kudu, kasonsu na nuna baiken matakan kara harajin na Amurka ya karu da sama da kaso 20 bisa dari. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin jihar ta ce, matakin na daya daga cikin kokarin gwamnati mai ci na inganta ayyukanta domin samar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar jihar Sokoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ko da yaushe Sin tana himmatuwa wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, tare da kira da a warware rikici ta hanyar tattaunawa. A sa’i daya kuma, aniyarta ta kiyaye ikon mulkin kasa, da hakki da moriyarta a tekun kudancin Sin ba za ta sauya ba. Ita kasar Philippines kuma za ta dandana kudarta bisa ga yadda ta aiwatar da mummunan mataki kan batun zirin tekun Taiwan, da nufin biyan bukatun Amurka game da dabarunta a yankunan tekun Indiya da na fasifik. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    A ganin gwamnatin Amurka, manufar ramuwar haraji za ta taimaka wajen farfado da masana’antu a kasar da kara samar da guraben aikin yi, amma yadda ta daidaita matsalolin tattalin arzikinta ba ta hanyar da ta dace ba, da kuma gazawa wajen bin ka’idojin tattalin arziki, ya haifar da damuwa a zukatan al’umma da kuma tsoro a kasuwanni, lamarin da ya sa Amurka ta kara shiga mawuyacin hali.   Cikin kwanaki 100 da suka shude, wasu kasashen duniya sun ki mika wuya ga cin zalin Amurka ta fuskar manufar ramuwar haraji. Misali, kasar Sin ta fara mayar da martani, a kokarin kiyaye halastattun hakkokinta da tsarin tattalin arziki da cinikayya da ma na adalci a duniya. Kana kuma kungiyar tarayyar Turai...
    Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewarsa, wajibi ne shirin ya mayar da hankali kan burin cimma zamanantarwa irin ta gurguzu da nufin gina babbar kasa da samun ci gaba wajen farfado da ita. Shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar, wanda shi ne daftarin dake zaman jigon jagorantar ci gaba na matsakaici da dogon zango a bangaren tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin, yana zayyana baki dayan burikan kasar da manyan ayyuka da manufofin da ake aiwatarwa a dukkan bangarori cikin shekaru 5. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
    Sun ce suna tafiya daga Yola zuwa Lafia ne lokacin da wasu mutane da ake zargin ‘yan fashi ko masu garkuwa da mutane ne suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka tsere zuwa daji don tsira rayukansu. Sojojin sun taimaka wajen gyara tayar motar sannan suka tabbatar da cewa fasinjojin sun ci gaba da tafiyarsu cikin tsaro. Shugaban Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa saurin ɗaukar mataki da kuma tsayin daka kan aiki. Ya kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai a kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Rahotannin da suke fitowa daga kasar Yemen na cewa katafaren jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki malakar klasarAmurka wato USS Harry Truman zai fice daga tekun red sea da nan kusa saboda makaman kasar Yemen da suka fada mata. Tashar talabijin ta Almasirah ta kasar Yemen ta nakalto wani jami’in ma’aikatar tsaron kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa, saboda yawan hare haren da sojojin Yemen suka kaiwa jirgin, wadanda suka hada da amfani da makamai masu linzami samfurin Crusse da kuma Balistic, har ila yau da jiragen yaki masu kunan bakin waken da suka fada a kansa. A yanzun ya zama dole jirgin ya fice daga tekun. Tun cikin watan Maris da ya gabata ne gwamnatin...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    Haka kuma wasu hukumomin gwamnati sun taimaka, ciki har da Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice, Hukumar Tsaro ta DSS, Hukumar Lafiya ta Tashar Jirgin Sama da Rundunar ‘Yansanda. Mutane biyu daga cikin waɗanda aka dawo da su na fama da matsananciyar rashin lafiya, kuma an garzaya da su asibitin New Ikeja don a duba lafiyarsu. Bayan an yi musu rijista da ɗaukar bayanan yatsunsu, an mayar da su cibiyar mazauna ‘yan gudun hijira da ke Igando, a Jihar Legas, inda za su samu taimako don ci gaba da rayuwa. NEMA ta ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarinta na tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali a ƙasashen waje da kuma taimaka musu...
    A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
    Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki. Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”...
    Wani bon kirar hannu da aka dasa akan hanyar dake hada Rann da Gamboru a jihar Borno ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 6. Daga cikin wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar tashin bom din sun hada mata da kananan yara kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta sanar. Kungiyar nan mai suna; gwamnatin musulunci a yammacin Afirka ce ta sanar da daukar alhakin kai hari na ranar Litinin din da ta gabata. Bugu da kari sauran wadanda su ka rasa rayukan nasu manoma ne da suke cikin motar a-kori-kura da ta taka nakiya. Baya ga wadanda su ka rasa rayukansu, wasu mutanen su 3 sun jikkata,kuma tuni an dauke su zuwa asibiti domin yi musu magani. Wani dan sintiri da yake...
    Shugaban tawagar baƙin, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya ce sun zo Yobe domin nazarin halin tsaro da tattara bayanai da za su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.   A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.   Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...
    Hukumar Fensho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta shirya fara aikin tantance ‘yan fansho da ke cikin tsarin. Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Fansho, inda shugabannin kungiyar ‘Yan Fansho ta Najeriya reshen Jigawa suka halarta. A cewarsa, an shirya fara aikin tantancewar ne daga ranar Litinin, 5 ga Mayu, 2025. Alhaji Dagaceri ya bayyana cewa, an shirya hakan ne da nufin sabunta tsarin biyan fansho tare da tabbatar da ingancin bayanai. Ya ce, aikin tantancewar zai gyara wasu ‘yan kura-kurai da suka kunno kai a cikin shekaru uku da suka gabata, da kuma tabbatar da ingantattun bayanai a jadawalin...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin wuta da zai iya janyo tashin gobara da zai iya kona yankin gaba daya. A jawabin da ya gabatar yayin taron kolin majalisar shawarar Musulunci ta Iran a yau Talata, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Firai ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya mai laifi ne mai zubar da jinin fararen hula, saboda neman hana mutuwarsa a fagen siyasa, kuma yanzu yana yin barazana ga al’ummar Iran...
    Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila’ tana aiwatar da kisan kiyashi kan Falasdinawa ana gani kai tsaye a tauraron dan Adam Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a yau Talata ta yi Allah wadai da shirun da duniya ta yi game da yadda gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya take aiwatar da kisan kiyashi a zirin Gaza, kai tsaye duniya na gani ta hanyar tauraron dan Adama. A yayin gabatar da rahoton shekara-shekara na kungiyar ta Amnesty kan kare hakkin bil’adama a duniya Agnes Callamard, sakatariyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce tun ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, duniya ke kallon yadda ake aiwatar...
    Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma dokar ta kunshi hukunta masu laifin daurin shekaru 25 a gidan yari. Jaridar ta The Guardian ta ruwaito cewa: Masu fasakwaurin mutane da aka yanke wa hukunci sun zama rukuni na biyu mafi girma a gidajen yarin Girka, bayan masu safarar miyagun kwayoyi. Jaridar ta bayyana cewa ‘yan Sudan su ne rukuni na hudu mafi girma na masu neman mafaka a kasar Girka, inda suka...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na farko a fannin tattalin arziki a Jami’ar Maiduguri a shekarar 1996, ta kara inganta iliminta da samun digiri na biyu a fannin Gudanar da Kasuwanci (MBA) daga Jami’ar Bayero, Kano a shekarar 2011.“ Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa Aisha Mujaddadi ta samu  gogewa na tsawon shekaru 19 a fannin aikin shawarwari na ci gaban kasa da kasa, inda ta yi aiki a kan muhimman...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka.   A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet   Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda tsawonsu ya dara na bene mai hawa biyar, inda kuma aka tanadar wa da yankin, ababen more rayuwa.   kananan hukumomi ne, suka gina wadannan matsugunnan, musamman donin a dakile barazanar kwararowa alumma daga kauye, zuwa cikin birane.   A gwajin da aka yi na yankunan da su habaka sosai a China, ana buga misali da Hero Bay kan yadda gwamnati ke bai wa alumma...
    Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta, ya taɓa buga wasa a duka ƙungiyoyin. Yana fatan ya zama kocin farko da zai jagoranci Arsenal ta lashe kofin Zakarun Turai. Wannan ya sa magoya bayan Arsenal ke fatan ganin ƙungiyarsu ta yi abin mamaki a wasan da za a fara da misalin ƙarfe 8 na dare agogon Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Kalli yadda aka karɓi ’yan Najeriya guda 203 da aka dawo da su daga ƙasar Libya. (Hoto: Onyekachukwu Obi).
    Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda. An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su. ‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike. Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Sanata Ali Ndume, mai wakiltar yankin Borno ta Kudu, ya bayyana cewa hare-haren na ƙara ƙamari a yankin abun takaici ne. Ya ce ya samu rahoto tsakanin Hawul da Garkida inda aka ce an kashe ’yan sa-kai sama da 10 a ranar Litinin. A cewarsa, sama da mutane 100 aka kashe cikin wata guda a hare-hare da aka kai Sabon Gari, Izge, Kirawa, Pulka, Damboa, Chibok, Askira Uba da wasu garuruwa da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD a kasashen Turai yana fadar haka a gaban alkalai a kotun ta ICJ a jiya litinin. Ya ce  HKI tana kisa ta sama da makamai, sannan tana kisa ta kasa da yunwa banda haka tana ci gaba da korar  Falasdinawa daga yankin yamma da kogin Jordan tun fiye da watanni 3 da sua habata. Kutun ta bude wannan zaman ne bisa bukatar MDD ta shekara...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
    Shugaban  kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye. Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take  ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar. Shugaban kungiyar...
    Wata majiya kuma ta bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu na iya fin haka, duba da yawan mata da yara da lamarin ya rutsa da su. A lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin soji da ‘yansanda ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki” DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A kan wannan sauyi da dalilansa ne shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari. Domin sauke shirin, latsa nan
      Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai. Gwamnan ya kuma amince da nadin mambobin tawagar Amirul Hajjin. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, mambobin sun hada da Dr. Yusuf Abdurrahman, Babban Limamin Masarautar Hadejia da Alhaji Lawan Ya’u Roni, Talban Kazaure. Sauran su ne Dr. Mahmoud Yunusa, Sa’in Dutse da kuma Alhaji Adamu Dauda Zakar, Durbin Hadejia. Sanarwar ta bayyana cewa an yi wadannan...
    Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan kasuwa na duniya da su shiga harkokin tattalin arziki da zuba hannun jari a Iran. A yayin bikin bude baje koli karo na bakwai na baje kolin kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa kasashen ketare (Iran Expo 2025) a safiyar yau Litinin, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi maraba da baki na kasashen waje da suka halarci wannan baje kolin, yana mai cewa, “Ko...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba. Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka,...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin da ta gabata, Araqchi ya bayyana ci gaba da killace yankin Gaza da rashin abinci da magunguna, tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, a matsayin wani laifi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin dan Adam. Ya dauki Amurka da sauran masu goyon bayan ‘yan sahayoniyya a matsayin masu hannu a kisan kiyashi da laifukan yaki...
    Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya. A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato. Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi ’yan uku a garin Kaurar Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo ta jihar. Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi A yayin da mai jego da angon karni da ’yan uwa suke tsaka da murna, wannan karuwar haihuwa ta kara jawo musu sha-tara ta arziki, inda matar gwamnan...
    “Saboda haka, Litinin 28 ga Afrilu, 2025, za ta kasance 30 ga Shawwal 1446AH, yayin da ranar Talata 29 ga Afrilu, 2025 za ta zama farkon watan Zulki’ida 1446AH.”   Sanarwar ta ci gaba da cewa, Sarkin Musulmi na mika sakon fatan alheri ga al’ummar Musulmi, ya kuma bukace su da su ci gaba da yi wa kasa addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso...
    Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani gidan yarin da aka kebewa yan Afrika, kuma yawansu ya kai 115, amma har yanzun ba’a san yawan wadanda suka rasa rayukansu a gidan yari. Labarin ya  kara da cewa har yanzun ma’aikatan agaji suna aikin ceto a wurin, sannan hotunan da suka fara bayyana sun nuna gawaki da dama. Amma Al-Masirah ta bayyana cewa akalla mutane 68 sun rasa rayukansu.
    Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa  a makon da ya gabata. Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da yankin sun dade suna takurawa Abbas kan ya nada mataimaki da kuma wasu mataimaka sabuda rawar da gwamnatinsa zata taka bayan yakin gaza. A yau ne majalisar zartarwa ta amince da nada Hussein Al Sheikh a matsayin mataimakin shugaban majalisar da kuma mataimakin shugaban kasa a lokaci guda. Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Falasdinawan WAFA, ya bayyana cewa gwamnatin Abbas ce da hakkin sa hannu...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar. A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta...
    A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.   “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.   “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.   “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fagen siyasar Najeriya na ci gaba da jijjiga sakamakon sauya sheƙar da ’yan siyasa daga ɓangarori daban-daban suke yi. A baya-bayan nan tsallakawar da wasu jiga-jigan jam’iyyun adawa suka yi zuwa Jam’iyyar APC mai mulki ta jawo ɗiga ayar tambaya a kan dalilansu da kuma makomar hamayya a zaɓen 2027. Hakan dai yana faruwa ne a daidai lokacin da wasu ’yan ƙasar suke kokawa bisa yadda ake gudanar da mulki da kuma yadda wasu manyan ’yan siyasa suke fadi-tashin kafa wata inuwa da suka ce za ta ciro wa talaka kitse a wuta ta hanyar kawar da gwamnatin APC. NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin magani DAGA LARABA:...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin lamarin ya kai matakin da akwai wuraren da mutane ba sa iya zuwa da daddare saboda tsoron mummunan abin da ke iya samun su. An kashe sojoji 12 a barikin Nijar An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba Wasu na ganin yadda ake gudanar da siyasar jihar da kuma yadda rashin aikin yi su ne ummulahaba’isin wannan matsalar musammam a tsakanin matasa....
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne a kawar da ta’addanci ta hanyar hadin kan kasashen yanki Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta’addancin da aka kai a birnin Pahalgam na kasar Indiya, tare da nuna alhini da juyayinsa ga gwamnati da al’ummar kasar Indiya, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin domin yakar ta’addanci da kuma tsayawa tsayin daka kan wannan barazana ta bai daya. Pezeshkian ya zanta ta wayar tarho a yammacin jiya Asabar da fira ministan kasar Indiya Narendra Modi, inda suka tattauna kan sabbin al’amuran da suke faruwa a yankin na Indiya, da kuma alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Indiya.
    Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka. Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran,...
    A ganawarsa da wata jami’ar Amurka, al-Julani ya yi alkawarin ba zai cutar da tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila ba! Barbara Leaf, tsohuwar mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin gabas ta tsakiya, ta tabbatar da cewa shugaban rikon kwarya a Siriya, Mohammed al-Julani (al-Shara’a), “ya bayyana fahimtar matsalolin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila,” a cewarta. Hakan ya zo ne a wata ganawa tsakanin Leaf da al-Julani a birnin Damascus, jim kadan kafin ta bar mukaminta. Leaf ta bayyana taron a matsayin “mai kyau kuma mai amfani.” Har ila yau Leaf ta yaba da “hanzari da kuma dabarar da Shara’a ke bi wajen tunkarar al’amurran yankin,” tana mai cewa “yana neman kulla kyakkyawar alaka da bangarorin yankin.”
    Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna Umar Namadi ya yi jinjina ga marubucin littafin bisa rubuta cikakken tarihi da zai amfani al’umma, musamman matasa masu tasowa. Malam Umar Namadi ya kuma yi alkawarin umurtar ma’aikatar ilimi ta jihar da ta sayi kwafin littafin domin amfanin ɗalibai a makarantun gwamnati. Gwamna Umar Namadi ya kuma sayi kwafi bakwai na littafin a madadin iyalinsa kan kudi naira miliyan daya, yayin da...
    A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga gida ta NOUN inda na karanci ‘Education Administration and Planning’.   Jammaje ya ci gaba da cewa a yawace yawacen da na yi na tafi kasashe irinsu Afirika Ta Kudu da kasar Kenya inda a wancan lokacin sai na lura cewa mutanen wadannan kasashen biyu suna yi wa duk wani dan Nijeriya wani kallo na daban sakamakon abin da suka ga ana nunawa a wasu...
    A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun kai daukin gaggawar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan sansanin ‘yan hijira da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu da kuma yanke wutar lantarki a garin Atbarah, a jihar “Nahrun-Nil” ta arewa. Hukumar dake samar da wutar lantarki ta Sudan ta tabbatar da yankewar samar da wuta a wannan yankin saboda harin da mayakan na rundunar daukin gaggawa su ka...
    Francis, wanda aka zaba a matsayin gwarzon Shekarar na TIME a 2013, ya zama Fafaroma na farko na da ya fiton daga yankin Latin Amurka lokacin da ya karbi ragamar cibiyar addinin. A cikin wa’adinsa, Francis ya ya yi suna wajen tawali’u da kiran zaman lafiya yayin da duniya ke fuskantar manyan kalubale, da suka hada da gami da cutar Korona da rikicin Gaza.   Yayin da duniya ke juyayin rasuwar Francis tare da tunawa da tarihin rayuwarsa, yanzu kuma an fara shirin mika jagoranci a fadar Batican wadda aka fi sani da interregnum, wato ana nufin wani lokaci da babu Paparoma akan kujerar mulki (wanda ake kira sede baccante, ko “kujerun da ba kowa ba”).   Akwai abin da...
    Mayakan Boko Haram sun halaka mutum goma sha biyu da jikkata karin biyu bayan wani hari da suka kai kan kauyen Bokko Ghide a Karamar Hukumar Goza ta Jihar Borno. Wakilinmu ya ruwaito cewa cikin wadanda aka kashe akwai ’yan sa-kai biyu da wasu mutum 10 da suka fita debo itacen girki. Sulhu da ’yan bindigar Katsina: Gaba aka ci ko baya? Abubuwan da suka faru yayin jana’izar Fafaroma Francis Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce mayakan sun yi wa ’yan sa-kan kwanton bauna a kan hanyar Kirawa da ke gudunmar Pulka. “Sun fita neman itace ne a jeji a ranar Asabar, yayin da yaran [mayakan Boko Haram] suka yi musu kwanton...
      Duk da haka, Mai Maciji ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun gudu lokacin da matasan gari suka afka musu. Sun kona wani shago a kasuwar, amma wutar ba ta bazu zuwa sauran shaguna ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar a birnin Mascat na kasar Omman. Ya ce bangarorin biyu a shirye suke su ci gaba da tattaunawa, ya kuma kara da cewa tawagra tattaunawa a wannan karon sun dan kara yawa, don akwai bukatar kwararrun a bangaren siyasa, sannan a zama mau zuwa a ranar Asabar mai zuwa zai hada kwararru a fanni makamashin nukliya. Ministan ya kammala da cewa idan Amurka da gaske...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bayyanawa firai ministocin kasashen Indiya da Pakistan a maganar da yayi da su ta wayar tarho a jiya Asabar, kan cewa mu hada kai gaba daya don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiya yana fadawa shuwagabannin kasashen biyu, kan cewa akwai bukatar hada kai tsakanin kasashen biyu da sauran kasashen yankin don yi ki da ayyukan ta’adanci. Shugaban ya kara jaddada yin allawadai da hare-heren da aka kai cikin kasar Indiya a makon da ya gabata. Ya kuma jajantawa Narendra Mudi firai ministan kasar kasar ta India. Harin dai yan bindiga a garin Pahalga na yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar Indiya suka kai,...
    Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada hannu wajen bayar da karin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya.   Shugaba Aliyev ya ce, “Muna ganin kasar Sin jagora ce ga kasashe masu tasowa na duniya, kuma tana taka rawar gani a wajen hada kan kasa da kasa, musamman ma wajen yayata ruhin Bangdun, ciki har da martaba ikon mulki da cikakkun yankunan kasa na sauran kasashe, da rashin...
    Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, ‌kasar Sin‌ za ta ‌kara bude kofarta domin ‌maraba da jarin waje na duniya‌. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai albarka.   Lokaci zai tabbatar da cewa, kasar Sin ta taba zama kyakkyawan wurin saka jari da ya dace, kuma tana kasancewa haka ma a yanzu, kana babu makawa a nan gaba za ta ci gaba da zama hakan ga ‘yan kasuwa na kasashen waje. (Mai fassara: Bilkisu Xin)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...
    Daruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar wani abu mai karfi a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke kudancin kasar Iran Wata babbar fashewa, wacce ba a taba jin irin ta ba, ta afku da yammacin ranar Asabar a yankin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke Bandar Abbas, a kudancin kasar Iran, wanda ya yi sanadiyyar jikkata daruruwan mutane a rahotonnin da ake da su a hannu har zuwa yanzu. A cikin wani sabon rahoton da aka samu kan adadin mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tashar jiragen ruwa ta Shahid Raja’e, kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ya ce: Adadin wadanda suka jikkata ya kai 516 ya zuwa yanzu. Fashewar ta yi karfi...
    ‘Yan gudun hijira a Sudan sun yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su ceto yara da tsofaffi daga mummunan kangin da suka shiga An gwabza kazamin fada a kusa da birnin El Fasher da ke arewacin Darfur tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka yi ruwan bama-bamai kan birnin da na manyan bindigogi, inda suka kashe fararen hula akalla 35. Sojojin Sudan sun samu nasarar dakile wadansu daga cikin wadannan hare-hare, amma duk da haka sun janyo hasarar rayukan bil’adama da na dukiya. Sannan  sojojin Sundan sun kuma kwace iko da birnin Bara da ke Arewacin Kordofan, kofar Nyala a Kudancin Darfur. Dakarun kai daukin gaggawa sun yi wa birnin kawanya...
    Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira idan aka ga wani abu da ba a gamsu da shi ba; 08034805544, 07032490813 da kuma 09053872244 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar Tajikistan Sirojiddin Muhriddin. Ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi harajin kwastam yayin da suka hadu a birnin Almaty domin halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen tsakiyar Asiya da kasar Sin karo na shida. Wang, ya nanata cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da dukkan bangarori domin tabbatar da gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci,...
      Kazalika, ya ce, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa tare da IMF wato asusun ba da lamuni na duniya, da kuma ba shi goyon baya wajen taka muhimmiyar rawa a kan kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya cikin kwanciyar hankali.   Bugu da kari, Pan ya jaddada bukatar gaggauta zurfafa sauye-sauyen asusun na IMF a bangaren kaso, yana mai bayyana gyare-gyaren da suka kamata a yi a bangaren rabon kason a matsayin wani muhimmin bangare na sake fasalin tsarin shugabancin IMF. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Zulum ya bayyana wasu matsaloli da ke kawo tsaiko, ciki har da ƙarancin sojoji a yankunan Timbuktu Triangle, Tumbus, tsaunin Mandara, da kan iyakar Nijeriya da ƙasashen Sahel. Ya roƙi Ministan Tsaro da ya turo ƙarin manyan makamai da motocin yaƙi na zamani zuwa Borno domin taimaka wa sojoji. A nasa jawabin, Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura ƙarin kayan aiki da jami’an soja don magance matsalar tsaro a Borno da Arewa Maso Gabas. Ya ce shugaban ƙasa ya umarce su da su tabbatar da samar da duk abin da ake buƙata domin murƙushe ‘yan ta’adda a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara  bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo. A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7....
    Shugaban rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed Al-sharaa ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta samar da hulda da HKI a dai-dai lokacinda ya dace. Jaridar Middle East Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Ahmed Sharaa yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaba Donal Trump Har’ila yau shugaba Al-sharaa ya fadawa wani dan majalisar dokokin kasar Amurka kan cewa gwamnatinsa zata samar da huldar jakadanci da HKI a lokacinda ya dace, sannan a bangaren kasar Siriya kuma tana bukatar da farko a dagewa kasar takunkuman da aka dora mata, sannan yana son a yi maganar yankunan kasar Siriya wadanda HKI ta mamaye bayan juyin mulkin da aka yi a kasar. Dan majalisar dokokin kasar ta Amurka...
    Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a kan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila inda a wannan satin ake saran Liberpool za ta zama zakara a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork  ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Al-shaibani ya na cewa takunkuman suna hana ruwa guda a cikin al-amura da dama a kasarsa, kuma suna hana kafuwar gwamnatinsa su kamar yadda ya dace. Ministan ya ce dage takunkuman ya zama wajibi don samun ci gaban kasar don kuma rage matsin lamban da mutanen kasar suke ciki.  Kasashen yamma musamman Amurka da tarayyar Turai da kuma MDD...
    A cewar kungiyar ta OPEC, wannan ya ya faru ne duk da raguwar yawan man da Nijeriya ta samar a watan da ya gabata, musamman idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata.   Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da raguwar, yawan Man da kasar nan ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce na kasashen Algeria da Dimoliradiyyar Kongo.   Kazalika, kungiyar ta bayyana cewa, ta hanyar ci gaba da karfin da ta samu a watan Fabrairu, kasar nan, dara kasar Algeria, inda ta samar da ganga 909,000 a kowace rana, da kuma jamuriyar Kongo da ta samar da ganga 263,000 a kowace rana.   Kungiyar...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gargaɗi sabbin masu yin hidimar ƙasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da su guji shiga ƙungiyoyin sirri, da ayyukan siyasa, da kuma nuna kiyayyar addini a duk tsawon lokacin hidimarsu. A cikin jawabin gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Abdulkadir Mamman Nasir, ya gabatar a yayin shirin gabatar da ƴan hidimar na rukunin A, na tsari na ɗaya, Gwamna Radda ya bayyana cewa wannan horon na farko wani muhimmin mataki ne a tafiyar hidimar ƙasa da mambobin NYSC ke yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Minista Ya Nemi A Mayar Da  NYSC Shekaru 2 Ya kara da cewa suna buƙatar...
    “Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho.   Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta.   Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta.   Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...
    Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu. Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar. Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan. Haka shi ma Malam Usman Auwal,  ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar...
    Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama.  Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da asubahin yau Asabar akan wani gidan da yake a sansanin ‘yan hijira da “Mukhayyam-Shati’i.” da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai 3 da jikkata wasu da dama. Majiyar Falasdinawa ta kuma ambaci cewa, da asubahin yau Asabar sojojin HKI sun tarwatsa wasu gidaje a yankunan da suke gabashin birnin Kudus.  Dama a jiya Juma’a jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata makaranta da take...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona.   A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira miliyan 15, da Yalwa naira miliyan 2.7, da dai sauransu.   Ba da jimawa ba, wani shugaban ‘yan fashin dajin nan, Dogo Gide, ya bukaci a biya naira miliyan 100 daga wasu al’ummomi 23 da ke karamar hukumar Tsafe, lamarin da ya sa jama’a suka kauracewa gidajensu.   Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Kunchin-Kalgo da aka nemi naira miliyan 20 daga wajensu,...