Jagora: Tunanin JMI Ta Yi ‘Biyayya Ga Amurka’ Ba Zai Taba Yiyuwa Ba.
Published: 24th, August 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Sayyid Aliyul Khaminae, yace mafarkin da gwamnatin Amurka take yi na JMI ta yi biyayya a gareta, abu ne wanda ba zai taba faruwa ba. Ya kuma yi gargadi ga mutanen kasar su yi hattara da kokarin raba kansu.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Imam Khaminae yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a jawabin da ya gabatar a wani taro a cikin Hussainiyyar Imam Khomani (q) dake nan Tehran.
Labarin ya kara da cewa Jagoran ya gabatar da jawabin ne, a ranar shahadar Limami na 8 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), wato Imam Aliyu dan Musa Arridah (a).
Labarin ya kara da cewa, makiyan JMI sun tabbatar da cewa ba zasu taba samun nasara a kan JMI ta yaki ba, musamman ganin abinda ya faru da su a yakin mai tsarki na kwanaki 12 a cikin watan Yunin da ya gabata. Har’ila yau tare da hadin kan mutanen kasar, da kuma hadin kai da aiki tare tsakanin sojojin kasar an sami nasara a kansu Don haka yace a halin yanzu sun koma kan rarraba kan mutanen kasar, don haka dole ne mutane su sa hankali su kuma yi hattara da wannan makircin.
A wani wuri a jawabinsa yana cewa, gwamnatocin Amurka a shekaru kimani 45 da suka gabata sun nuna adawa da JMI, amma tare da boye manufofinsu na wannan adawar, wani lokacin su ce, take hakkin bilk’adana, ko hakkin mata, ko goyon bayan ayyukan ta’addanci da sauransu. Amma shugaban kasar Amurka mai ci ya fito fili ya bayyana cewa Amurka tana son Iran tayi mata ‘biyayya’.
Jagoiran yace ya zama dole ga masana da masu rubutu su tabbatar da cewa hadin kan da kasar Iran take da shi a cikin yakin da ya gabata da kuma bayansa ya dore.
Imam Khaminae ya bayyana cewa Amurka da HKI sun so ganin bayan JMI a yakin da ya gabata, amma suka gamu da maida martani mai tsanani wanda basu zata hakan zai faruba, saboda shirin da suka yiwa hakan. Tare da rundunoninsu na cikin Iran da wajenta.
Jagoran ya ce a halin yanzu, HKI ce kasar da kowa a duniya yafi ki, saboda haka ne kasashen yamma musamman Faransa da Burtaniya suna canza muryarsu zuwa soka, kadai amma kome a kasa yana tafiya kamar yadda yake a da, Yace irin abinda yake faruwa a gaza bai taba faruwa a tarihin bil’adama ba.
Daga karshe yace Iran a shirye take ta dauki matakan da suka dace kan HKI, ba yin tir a baka kawai ba, ya yabawa mutanen yamen kan matakan da suke dauka kan HKI kuma shi ne dai dai. Sannan ya yi addu’a, kan cewa All..ya taimaki JMI a kan makiyanta, da kuma dukkan wadanda suke gwagwarmaya neman gaskiya a duniya, ya kuma basu sa’ar tumbuke HKI cutar cancer da aka dasa a yankin. Da kuma fatar farkawar musulmi da hadin kansu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masu Makoki A Mashad Sun Yi Cincirindo A Hubbaren Imam Reza (a) Da Ke Mashad August 24, 2025 Aragchi: Batun ‘Isra’ila Babba” Mafarki ne Kuma Barazana Ce Ga Zaman Lafiya A Duniya August 24, 2025 Dakarun IRGC A Inan Iran Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Gwamnatin Iran August 24, 2025 Juyayin Shahadar Jagoran Shiriya Na Iyalan Gidan Manzon Allah Imam Ali Arridha {a.s} A Mash’had Sun Kai 3,500,000 August 24, 2025 Ma’aikatar Shari’a Ta Sojojin Kasar Iran Ta Ce; Dakarun ‘IRGC’ Barkono Ne A Idanun Makiya August 24, 2025 Makami Mai Linzamin Iran Kirar Qasim Basir Mafarkin Ban Tsoro Ne Ga Tsarin Tsaron Makiya August 24, 2025 Al’ummar Birnin Chicago Na Amurka Sun Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa August 24, 2025 Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Ta Bayyana Kakaba Yauwa A Gaza Da Laifin Yaki August 24, 2025 Ministan Tsaron Iran: Ba Mu Yi Amfani Da Manyann Makamanmu A Yaki Da Isra’ila Ba August 24, 2025 Holland: Karin ministoci 8 sun yi murabus saboda kin daukar matakai kan Isra’ila August 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da ya gabata
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta.
Mohammad Islami shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na Iran ta fadi a bayan taron da hukumar ta IAEA dake gudanarwa a Vienna yanzu haka cewa yana neman hukumar ta IAEA ta goyi bayan kudurin da ta fitar kuma ta yi Tir da harin wuce gona iri da hki ta kai kan tashoshin nukiliyarta.
Wakilai guda 180 a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ne suka hallara abirnin viyana daga ranar 15-19 domin gudanar da taron kasa da kasa karo na 69 da hukumar ta duniya ke shiriya a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austeria
Yace mun bayyana cewa alummar Iran basu da rauni wajen fuskantar duk wata barazana, kuma basu da niyyar mika wuya, ,ya kara da cewa ilimin nukiliyar Iran na asalai ne kuma ba zaa iya share shi ta hanyar tayar da bama bamai ba.
.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Kungiyar Human Rights Watch; Isra’ila Ta Kashe ‘Yan Jarida Fiye Da 30 A Kasar Yemen Ne Da Gangan September 16, 2025 Kungiyar Kare Hakkokin Bil’Adama Ta Siriya Ta Bankado Karin Fararen Hula Da Aka Kashe A Rikicin Suweida September 16, 2025 Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya September 16, 2025 An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A HKI September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci