An kama matashi kan zargin kashe matar ɗan uwansa mai juna biyu
Published: 24th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, ta kama wani matashi mai shekara 29, Sylvester Enemo, bisa zargin kashe matar ɗan uwansa, Misis Esther Enemo, wacce ke ɗauke da juna biyu a Ilorin.
An samu gawar Esther mai shekara 39 a yankin Temidire Zone 4, a bayan gidanta cikin daji, an yayyanka jikinta.
An haramta bukukuwan aure a Taraba NDLEA ta kama matashi da wiwi ta miliyan 10 a KanoAn gano wasu sassan jikinta a cikin wani buhu da aka jefar a ƙarƙashin gada, sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba a ga kanta ba.
Shaidu sun ce an ga Sylvester da safiyar ranar Alhamis ya fita daga gidan da leda baƙa kuma da jini a jikinta.
Maƙwabta, sun ce marigayiya tana gida ita kaɗai a daren kafin a kashe ta, kuma an ga lokacin da ta yi cefane kafin ta koma gida, lamarin da ya nuna kamar tana jiran wani.
Kisan ya tayar da hankalin al’umma, inda ake zargin yana da alaƙa da tsafi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an CID sun kama wanda ake zargi bayan samun rahoton faruwar lamarin.
Ta kuma bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Ojo Adekimi, ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da tabbatar da adalci.
An kai gawar marigayiyar ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin (UITH), kafin kammala bincike.
Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a da su kwantar da hankali tare da guje wa yaɗa jita-jita da ka iya tayar da fitina a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɗan Uwa Kwara zargi
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai October 30, 2025
Manyan Labarai Sheikh Gumi Ya Yabi Tinubu Kan Afuwar Da Ya Yi Wa Maryam Sanda October 30, 2025
Manyan Labarai Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC October 30, 2025