Aminiya:
2025-12-09@04:49:05 GMT

Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS

Published: 15th, April 2025 GMT

Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu.

EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya

Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan.

Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu.

A wani jawabi da ya yi manema labarai tun a watan da ya gabata, shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa sun sauya tsarin ne saboda “daidaita shi da irin na sauran ƙasashen duniya.”

Ya ce karo na ƙarshe da Nijeriya ta sauya tsarin ƙididdigar shi ne a shekarar 2009, inda ake ƙididdige farashin kayan da aka fi amfani da su a wannan tsakanin.

Hakan na nufin yanzu za a riƙa kwatanta farashin kayayyakin da aka ƙididdige daga shekarar 2024, maimakon 2009 da aka riƙa amfani da ita a baya.

A sabbin alƙaluman da NBS ta fitar, ta alaƙanta hauhawar farashin da tashin kayayyaki irinsu citta, garin rogo, shinkafa, zuma, dankali, barkono da sauransu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Hukumar NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hauhawar Farashi Maris Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.

Yayin da yake bayyana dalilin sauya sheƙar, Amaewhule ya ce sun bar PDP ne saboda rikice-rikicen cikin jam’iyyar.

Bugu da ƙari, a wani mataki da ake ganin na ƙoƙarin kaucewa gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 daga Gwamna Siminalayi Fubara ne, Kakakin ya sanar da dage zaman majalisa har zuwa watan Janairu 2026.

Ayyukan majalisar a kwanakin baya-bayan nan sun nuna cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba tsakanin bangaren zartarwa da majalisar jihar.

A watan Maris 2025, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamna da majalisa wanda kusan ya jawo rugujewar tafiyar da mulki a jihar.

Shugaban ƙasa ya kuma tsige Gwamna Fubara, mataimakinsa da kuma dakatar da majalisar jihar.

Sai dai an dawo da gwamnan da ’yan majalisar a jihar bayan an ɗage dokar ta-bacin a watan Satumba, tare da fatan cewa zaman lafiya ya dawo tsakanin bangarorin biyu.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC