Femi Falana SAN Ya Yi Kiran A Inganta Harkar Shari’a A Najeriya
Published: 10th, April 2025 GMT
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a.
Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano suka shirya, wanda aka gudanar a otal din Bristol Kano.
Falana ya yabawa jihar Kano bisa amincewa da dokar hukumar kula da laifuka ta FIDRA a shekarar 2019 tare da zama jiha ta farko da ta soke tuhumar da jami’an ‘yan sanda ke yi na aikata laifuka.
Ya kuma jaddada bukatar masu gabatar da kara su samar da na’urori na zamani da horarwa masu inganci don bunkasa ayyukansu.
Falana ya kuma jaddada mahimmancin inganta yanayin aiki ga masu gabatar da kara don ba su damar mai da hankali kan ayyukansu.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta bayyana irin kalubalen da talakawa ke fuskanta wajen samun adalci, inda ta bayyana yanayin tattalin arziki da kuma bukatar gwamnati ta shiga tsakani.
Falana ya ba da shawarar cewa a baiwa ofishin kare hakkin jama’a ikon taimakawa talakawa, tare da kasancewa a kowace karamar hukuma.
“Hakan zai baiwa talakawa damar samun adalci da kuma samun lauyoyin da za su gudanar da shari’o’insu, inda ya ba da misali da hukumar ba da agajin lauya ta kasa (Legal Aid Council) wacce ke da ofisoshi a dukkan jihohin kasar nan 36.
Falana ya kuma jaddada mahimmancin kare hakkin wadanda ake tuhuma da kuma karfafa amincewa da tsarin shari’a.
Ya kara da cewa wadanda ake tuhuma suna da ‘yancin neman a ba su lauya, kuma dole ne ‘yan sanda su tuntubi hukumar bayar da agaji ta Legal Aid don samar da lauya. Ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su taka rawa wajen wayar da kan jama’a, game da hakkokinsu a karkashin doka.
Femi Falana SAN ya yi kira ga kafafen yada labarai da su rika wayar da kan jama’a domin su sanar da jama’a hakkinsu a karkashin doka.
Cover /Abdullahi jalaluddeen/Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Shari a kare hakkin
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya.
Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu.
NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makarantaShirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya.
Domin sauke cikakken shirin, latsa nan