Gwamnatin Jigawa Za Ta Hada Gwiwa Da Jami’ar Azman Don Inganta Ilimi A Jihar
Published: 13th, March 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa za ta kulla haɗin gwiwa mai muhimmanci da Jami’ar Azman domin faɗaɗa damar ilimi da inganta ci gaban al’ummar jihar.
An bayyana hakan ne lokacin da shugabannin Jami’ar Azman, karkashin jagorancin Shugabar Jami’ar, Farfesa Fatima Batul Mukhtar, suka kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi a Fadar Gwamnati da ke Dutse.
Wannan haɗin gwiwa yana da nufin tallafawa sabbin hanyoyin koyarwa, da daukar nauyin dalibai a wasu shirye-shirye na musamman, da kuma inganta basirar matasa a muhimman fannoni kamar lissafi da kwamfuta, da kimiyyar bayanai, da sarrafa harkokin jiragen sama, da sauransu.
Yayin da take jawabi, Shugabar Jami’ar ta nuna godiya ga jajircewar gwamnatin jihar wajen bunkasa ilimi, tare da jaddada aniyar jami’ar wajen samar da inganci da kirkire-kirkire.
Ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta hada kai da jami’ar wajen shirye-shiryen horar da matasa da ba su takardun shaidar ƙwarewa, musamman a bangaren shirye-shiryen kwamfuta, tare da manyan kamfanoni irin su Cisco, Huawei, da Oracle Academy.
“Mai Girma Gwamna, Jami’ar Azman ta riga ta samu ci gaba a shirye-shiryen kwamfuta, domin mun yi rijista da Cisco, Huawei, da Oracle Academy, kuma muna da malamai da ke da takardar shaidar koyarwa daga Huawei. Saboda haka, muna rokon ku da ku duba yiwuwar yin haɗin gwiwa da mu a shirye-shiryen takardun shaidar ƙwarewa a bangaren shirye-shiryen kwamfuta.”
Shugabar Jami’ar ta kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa jajircewarta a fannin ilimi, musamman ware kaso 32 bisa dari na kasafin kudin 2024 ga bangaren ilimi da kuma ƙarin naira biliyan uku da aka ƙara wa Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Jigawa.
A nasa martanin, Gwamna Namadi ya nuna matuƙar godiya ga ƙoƙarin Jami’ar Azman tare da yabawa shugabancin Farfesa Fatima Batul Mukhtar.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin shirye-shiryen musamman da jami’ar ke bayarwa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana da shirin daukar nauyin wasu dalibanta domin su yi karantu a bangarorin da babu a sauran makarantu a jihar.
“Sabbin kwasa-kwasan da kuka kirkiro suna da kyau, kuma hakan zai jawo hankalin dalibai da malamai zuwa jami’ar.
Wannan na daga cikin dalilan da suka sa na ga babbar dama a wannan jami’a. Kwasa-kwasan da kuka ambata suna da matukar muhimmanci, musamman a yankunan da basu dawannan taarin karatu.”
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jami ar Azman Jigawa gwamnatin jihar shirye shiryen Jami ar Azman shirye shirye
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su.
Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse.
Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban Kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama, Alhaji Sani Sale Zaburan ya bayyana bukatar ganin jami’an ma’aikatar da ke kula da kananan hukumomi a shiyya shiyya suna gudanar da ayyukan su ba tare da jingina da shugabannin kananan hukumomi ba a ko da yaushe amma Kuma su na yiwa kananan hukumomin jagoranci wajen gudanar da sha’anin mulki da harkokin Kudi kamar yadda ya kamata.
Daya daga cikin ‘yan kwamatin Malam Ibrahim Sabo Ahmad Roni ya duba kundin bayanan sha’anin mulki yayin da Oditoci su ka duba kundin bayanan harkokin Kudi tare da yabawa da kuma bada shawarwari da za su inganta ayyukan ma’aikatar.
Da ya ke mayar da jawabi, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa wanda Babban Sakatare na maikatar ya wakilce shi, Alhaji Muhammad Yusha’u ya ce ma’aikatar ce ke uwa da makarbiya wajen yiwa kananan hukumomi jagoranci a sha’anin mulki da harkokin Kudi da zamantakewa domin kawo cigaba a yankunan karkara.
Kazalika, a daya bangaren kuma, karamin Kwamatin da Babban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa ya kafa bisa jagorancin wakilin mazabar Kiyawa Alhaji Yahaya Muhammad Andaza domin duba aikin gyaran gidajen kananan hukumomin jihar 27 da ke kan titin Bypass a Dutse ya mika rahoton sa ga babban kwamatin.
Alhaji Yahaya Muhammad Andaza Wanda sakataren Kwamatin Alhaji Yusha’u Muhammad ya wakilta, ya ce karamin Kwamatin ya duba gidajen Inda ya dauki samfur din yanayin da su ke ciki.
Ya ce daga cikin gidajen akwai wadda ke funskatar matsaloli kamar na tsagewar bango da sanya darduma da kujeru da kayan amfani a dakin girki marasa inganci yayin da ba a mayar da na’urar sanyaya daki a wasu gidajen ba.
Yusha’u wanda shi ne mataimakin Akawun majalisar, ya lura cewa akwai rashin kyawun flasta a wasu gidajen yayin da kan dakin wasu ke yayyo sai Kuma rashin fankar sama da karayyayun kujeru da rashin hada wasu gidajen da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rashin kyawun kofofi da magudanin ruwa da ke kawo barazanar ambaliyar ruwa ga wasu gidajen.
A nasa jawabin, shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar Dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari ya ja hankalin shugabannin kananan hukumomin jihar da su dauki nauyin cikakkiyar kulawa ga gidajen bisa la’akari da dinbin kudaden da aka kashe wajen gyara gidajen.
Usman Mohammed Zaria