Adadin Mata Mamallaka Sana’o’i Na Ta Karuwa A Kasar Sin
Published: 8th, March 2025 GMT
Yanzu haka adadin matan kasar Sin mamallaka sana’o’i na ta karuwa sannu a hankali, inda ya zuwa yanzu mata ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da ci gaba mai inganci a kasar.
Wasu alkaluma daga hukumar lura da hada hadar kasuwanni ta kasar sun nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, adadin kamfanoni da matan kasar Sin suka zuba jari sun haura miliyan 23, adadin da ya kai kaso 41.
Alkaluman sun nuna adadin hada-hadar kamfanoni masu jarin matan kasar Sin na ta karuwa, da kimanin kaso 9.8 bisa dari a duk shekara tun daga shekarar 2012, a gabar da karin mata ke kafawa, da zuba jari a kamfanoni daban daban. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu.
Irin wadannan mata a wasu lokutan basa tsira da rayukansu, a wasu lokutan kuma ko sun tsira, sukan shiga halin ciwon damuwa wanda ke daidaita musu rayuwa, a wasu lokutan ma har sai sun ji kamar su dauki rayuwar su.
NAJERIYA A YAU: Matsayar Doka Kan Taron Da Jam’iyyar PDP Ta Gudanar DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka SaceShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin halin da irin wadannan mata ke shiga da kuma hanyoyin da zasu bi don dawo da martaba a rayuwarsu.
Domin sauke shirin, latsa nan