Iran Ta Yi Tir Da Kakkausar Murya Kan Barazanar Soji Da Isra’ila Ke Yi Mata
Published: 28th, February 2025 GMT
Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin tsaron kasar a matsayin rashin hankali da wauta.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana a jiya Alhamis yayin da jami’an Isra’ila ke ci gaba da yi wa Iran barazanar daukar matakin soji, kasashen yamma na ci gaba da zargin kasar da kara karfin tsaronta.
M. Baqaei ya yi nuni da cewa, yankin yammacin Asiya na fama da wata mamaya da ta dade wacce kamu ta wuce gona da iri da rashin bin doka da oda.
Don haka ya kara da cewa, wajibi ne kawai Iran ta kara karfin tsaronta.
Kalaman nasa sun zo ne bayan ministan harkokin wajen Isra’ila Gideon Saar ya ce ana bukatar daukar matakin soji don dakatar da shirin nukiliyar Iran.
A cikin shekarun da suka gabata, kasashen Yamma sun soki ayyukan Iran a kan shirin nukiliyarta, jirage marasa matuka, tsaron sararin samaniyarta, da kuma shirye-shiryen makamai masu linzaminta, suna masu neman Tehran ta dakatar da su.
Iran ta sha nanata cewa ci gaban da take samu na soji ne kawai don kara kaimi ga kasar kan barazanar abokan gaba, musamman Isra’ila da Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku
Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya
Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin mamayar Isra’ila.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Wadannan hare-hare wani bangare ne na matakin da ya dace na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kai wa kan zirin Gaza.
Sannan sanarwar ta kara da cewa: Farmakin na farko an kai shi ne yankin Jaffa da aka mamaye da jirage marasa matuka ciki guda biyu. Harin na biyu ya biyo an kai shi ne kan yankin Ashkelon. Sannan harin na uku an kai ne kan wani gungun sojojin mamaya a yankin Negev.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Qolibaf: Barin HKI Ta Yi Abinda Taga Dama Ne Yana Karfafa Mata Giwa July 30, 2025 Yunwa Ta Kashe Karin Falasdinawa 7 A Gaza July 30, 2025 Malta Zata Amince da Samuwar Falasdinu a Cikin Watan Satumba Mai Zuwa July 30, 2025 Amurka Ta Ce HKI Ba Zata Fice Daga Kasar Lebanon Ba Sai An Kwance Damarar Hizbullah July 30, 2025 Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku July 30, 2025 Girgizar Kasa Mai Karfi Ta Kada Yankin Kamtashatka Na Kasar Rasha July 30, 2025 Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Cikin Masallacin Kudus July 30, 2025 Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka July 30, 2025 Shugaban Kasar Ivory Coast Ya Bayyana Shirinsa Na Sake Tsayawa Takarar Shugabanci Karo Na Hudu July 30, 2025 Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu July 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci