Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Janye Bincike Kan Shigo Da Jan Karfe
Published: 27th, February 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye binciken sashe na 232 kan shigo da jan karfe kasarta, inda ta bayyana cewa, zargin da ake yi na cewa kasar Sin na amfani da tallafin gwamnati da karfin samar da hajoji fiye da kima don gurgunta abokan takara kwata-kwata ba ya da tushe.
Kakakin ma’aikatar He Yadong ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a lokacin da yake amsa tambaya kan matakin da Amurka ta dauka na kaddamar da binciken sashe na 232 kan jan karfe da aka shigar da su kasar daga kasashen waje.
Ya kara da cewa, binciken na Amurka wani aiki ne na kashin kai da kariyar cinikayya wanda ta yi bisa fakewa da “tsaron kasa”, kuma matakin zai kara yin illa ga tsarin cinikayyar bangarori daban daban da kuma kawo cikas ga daidaiton tsarin samarwa, da rarraba hajoji tsakanin sassan kasa da kasa.
Kakakin ya ce, idan Amurka ta nace kan sanya karin haraji da sauran matakan takaitawa, Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kiyaye hakkoki da moriyarta. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Amurka: “Afirka Ba Ta Cikin Jerin Fannoni Da Muka Ba Da Fifiko A Kai”
Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu kasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban kasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alakar tarihi tsakanin kasar Laberiya da Amurka. Bugu da kari, Trump ya katse maganar shugaban kasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar—ba domin neman karfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka din damar samun ma’adanan da take bukata, da yiwuwar sanya wadannan kasashen dake nahiyar Afirka amincewa da karbar bakin haure da ake korarsu daga Amurka.
Watakila, shugaba Trump ba ya mai da hankali sosai kan da’a a fannin diflomasiyya, amma idan aka kwatanta da shugabannin kasar Amurka da suka gabace shi, to, a kalla yana bayyana kome a fili ba tare da rufa-rufa ba. Maganarsa da matakan da ya dauka, dukkansu na isar da sako zuwa ga kasashen Afirka cewa: “Ba ku cikin jerin fannonin da Amurka take nunawa fifiko.” “Za mu iya musayar wasu abubuwa, amma kada ku yi tsammanin za ku samu riba ko alfanu sosai.” (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp