NEMA Ta Bada Tallafi Ga Wadanda Gobara Ta Shafa A Kauran Namoda
Published: 10th, February 2025 GMT
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta gabatar da kayan agaji ga gwamnatin jihar Zamfara domin tallafawa wadanda gobara ta shafa a wata makarantar Islamiyya da ke Kaura Namoda.
A lokacin da take mika kayayyakin, Darakta Janar na Hukumar Hajia Zubaida Umar, ta ce matakin ya nuna damuwar gwamnatin tarayya kan halin da wadanda abin ya shafa ke ciki.
Babbar Daraktar wanda shugaban NEMA shiyar Sokoto, Aliyu Shehu Kafindangi ya wakilta, ya ce tallafin ya hada da kayan abinci kamar buhunan shinkafa, da masara, da man girki, da kayayyakin amfani gida.
A baya dai Hajiya Zubaida Umar ta ziyarci wadanda lamarin ya rutsa da su wadanda har yanzu suke ci gaba da karbar magani a asibitin mata da yara na Khadijah da ke Kaura Namoda.
A asibitin, wakilin na shugabar ta NEMA, ya kuma gabatar da kayayyakin jinya ga hukumar lafiya matakin farko domin ci gaba da kula da wadanda abin ya shafa.
Ya kuma jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki da suka hada da wakilan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara ZEMA, da ma’aikatar jin kai ta jihar Zamfara, da kuma karamar hukumar Kaura Namoda zuwa wurin da lamarin ya faru domin jajanta wa makarantar.
Wadanda suka karbi kayayyakin da hukumar ta NEMA ta bayar, a madadin gwamnatin jihar sun hada da babban sakatariyar hukumar ta ZEMA, wadda Daraktan Yaki da iftila’i, Hassan Usman Dauran, da wakilta, da Sarkin Kaura-namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha da kuma kwamishinan ma’aikatar jin kai ta jihar Zamfara, wanda babban sakataren ma’aikatar Mohammed Bashir Maradun ya wakilta.
Haka kuma tawagar ta kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kaura-namoda, Alhaji Sanusi Muhammad Asha a fadarsa.
Tun da farko, Sarkin Kauran Namoda, Alhaji Sanusi Asha, ya yi alkawarin sanya ido kan rabon kayan abincin ga wadanda abin ya shafa da kwamitin bayar da agajin gaggawa da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suka kafa.
Hakazalika, ZEMA da ma’aikatar jin kai ta jihar, sun yabawa hukumar NEMA bisa wannan karimcin.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kauran Namoda jihar Zamfara Kaura Namoda
এছাড়াও পড়ুন:
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.
Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.
Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu KanoShugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.
Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.
Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.
Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.
Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.
Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.
NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.
Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.
Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.
Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.