Netanyahu zai gurfana a kotu kan cin hanci
Published: 10th, February 2025 GMT
Fira Ministan Isra’ila, Banjamin Netanyahu, zai gurfana a kotu kan zargin aikata zamaba da karbar cin hanci da rashawa.
Za a gurfanar da Mista Netanyahu ne daomin ya amsa tambayoyi a shari’ar da aka jima ana zargin sa da aikata manyan laifuka uku na cin hanci da cin amana.
Masu gabatar da kara na zargin sa da aikata laifukan da suka hada da karbar cin hanci da zamba da kuma cin amana.
A kan haka yake fuskantar zargin bayar da cin hanci da kuma cin amanar dukiyar al’umma da aka ba shi.
Ana kuma zargin shi da matarsa da karbar toshiyar baki ta Dalar Amurka 21,000 daga wani furodusa a masana’anatar fina-finan Amurka ta Hollywood, dan kasar Isra’ila mai suna Arnon Milchan, da wani attajirin kasar Australiya, James Packer.
Yana kuma fuskantar zargin kulla yarjejeniyar da mamallakin kamfanin jaridar Yedioh Ahronoth, Arnon Mozes, domin tallata shi, inda shi kuma zai yi dokar da za ta hana bunkasar wata jarida da ke gogayya da Yedioh Ahronoth.
A kan wannan kuma ana zargin Netanyahu da laifin zamba da kuma cin amana.
Tun shekarar 2020 Netanyahu yake fuskantar wadannan zarge-zarge, amma ya musanta aikata ba daidai ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu
Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis.
Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya.
Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry GanaSakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka.
Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe baki ɗaya, inda da yawa ke jinjinawa jagorancinsa da kuma abin da ya bari.
Ana ci gaba da miƙa saƙon ta’aziyyarsu daga ko’ina, a dai-dai lokacin da jama’a ke juyayin rashin Sarkin.
Marigayi Sarkin Gudi ya shahara wajen hikima da jagoranci da jajircewa wajen ci gaban al’ummarsa tare da taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da haɗin kai a tsakanin al’umma, kuma za a riƙa tunawa da abin da ya bari har zuwa tsawan lokaci.
Sallar jana’izar wadda manyan malamai za su jagoranta, za ta samu halartar manyan baƙi, shugabannin gargajiya da sauran al’umma.
Za a binne gawar Sarkin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin na Gadaka.
Al’ummar masarautar dai na cikin alhini, inda da dama ke nuna alhininsu dangane da rashin jagoransu.
Ana sa ran gwamnati da al’ummar Jihar Yobe za su yi wa marigayi Sarkin gaisuwar ban girma, ganin irin rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.