2025-05-09@12:02:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 210
«Kidayar Jama a»:
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai. A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake...

An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo...
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da shawarar yin amfani da fasahar zamani wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan fashi a Nijeriya. Shugaban ya bayar da shawarar ne a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ya jagoranci mambobin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na ƙasa a ziyarar jaje ga...
Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga taron musayar al’adu da cudanyar al’umma da aka shirya domin murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya da jama’ar kasar Sin suka yi a kan zaluncin Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet. A cikin sakon nasa,...
Fira ministan kasar Siriya ya bayyana cewa: Kasar Siriya zata gudanar da tattaunawa ba na kai tsaye ba da haramtacciyar kasar Isra’ila! Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Abu Mohammed al-Julani ya sanar a jiya Laraba cewa: Kasar Siriya zata gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar...
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.” Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da...
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin musayar kudaden waje ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Afrilu, asusun ajiyar kudaden waje na kasar Sin ya kai dalar Amurka biliyan 3281.7, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 41 ko kashi 1.27 bisa dari daga karshen watan Mayu....
A bidiyon da wani mai suna Nawab Sheikh ya fitar na nuna yadda ya hau motarsa, wacce yake tuka ta a kan titunan birnin Murshidabad a cikin ƙasar Indiya, don nishaɗantar da mahaya babur, wanda ya sa bidiyon yake ta yaɗuwa a shafin sada zumunta na Instagram. Babu wani wuri mafi kyawun nuna bajintar kirkira...
“Mun rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke cikin Maiduguri. Yanzu haka saura biyu da ba na hukuma ba. Mun riga mun dawo da kashi 75 na ‘yan sansanin Muna gida, saura kashi 25 za su koma cikin kwanaki masu zuwa.” Kowane iyali sun samu tallafin abinci, kayan gini da kulawar lafiya. Haka kuma,...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Sha Alwashin Mayar Da Martani Cikin Gaggawa Kan Duk Wani Hari Kan Kasarta
Jamhuriayar Musulunci ta Iran ta sha alwashin mayar da martani cikin gaggawa ga duk wani kasadan ‘yan Sahayoniyya da Amurka kan kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya jaddada cewa: Duk wani kasadan harin soji da Amurka ko wakilliyarta gwamnatin ‘yan sahayoniyya suke yi, ko...
Falasdinawa fiye da 50 ne suka yi shahada yayin da wani adadi da dama suka jikkata a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai Gaza a jiya Litinin Rahotonni sun bayyana cewa: Fiye da Falasdinawa 50 ne aka suka yi shahada wasu adadi da dama kuma suka jikkata sakamakon hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ke...
A cikin wata daya kadai sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinawa 152 a yammacin Kogin Jordan. Majiyar Falasdinawa ta ambaci cewa a kudancin garin Khalil ‘yan mamayar sun rushe gidaje 25 da kuma wasu cibiyoyi, da hakan ya sa adadin gidajen da su ka rushe zuwa 152 kamar yadda hukumar Falasdinu ta ambata. Bugu da...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi watsi da zarge-zargen da aka yi ma ta dangane da kasar Yemen. A wani bayani da ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran din ta fitar ta bayyana cewa: Abinda mutanen Yemen suke yi domin taimakawa al’ummar Falasdinu, mataki ne na kashin kansu da su ka dauka cikin ‘yanci...
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya caccaki tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi da cewa maƙaryaci ne da ba shi da “kunya”. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi tare da ilahirin kansiloli 484 da ke fadin jihar a ranar Lahadi da maraice. Kotu za ta rataye matashi kan...
Ministan Tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Za su mayar da martani mai tsanani da karfi kan duk wani ta’addanci da kasarsu za ta fuskanta Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake mayar da martani ga barazanar Amurka, ya tabbatar da cewa Iran za ta mayar da martani mai karfi tare...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bishop Joseph Osifuwa, Bishop na jihar Kwara, ya ce Nijeriya za ta iya magance matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a sassan kasar nan idan har ta dauki matakin magance masu tada kayar baya. Bishop Osifuwa ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen babban taron cocin karo...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yaba da sadaukarwar da ‘yan jarida suka bayar da suke ba da labaran irin wahalhalun da Falasdinawa ke ciki A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter na ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana jin dadinsa ga...
Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara. Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin...

Falasdinawa 40 Ne suka Yi Shahada A Zirin Gaza Sakamakon Ta’addancin Sojojin Mamayar Isra’ila A Jiya Juma’a
Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan...
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya kaddamar da ayarin likitoci su tara domin kula da lafiyar maniyata aikin hajjin na wannan shekaran. Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ne ya bayyana hakan bayan ganawar farko da ayarin da kuma shugabannin hukumar. Ayarin likitocin ƙarƙashin jagorancin Dr. Bello Jamoh, za...
A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki...
Rahotonni sun tabbatar da cewa: Da tsakar daren jiya Litinin wayewar garin yau Talata, sojojin mamayar Isra’ila dauke da motocin soji guda hudu da wasu sojoji masu tafiyar kafa sun kutsa cikin yankunan kasar Siriya daga titin Al-Hurriya, inda suka wuce titin Al-Kassarat, zuwa Talat Jabata Al-Khashab. Majiyar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya ta...
Guo Jiakun ya bayyana cewa, a ranar 26 ga wannan wata, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki sun gabatar da sabbin matakan mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido, lamarin da ya kyautata manufar mayar da kudin haraji tun daga lokacin sayayya da kawo sauki ga baki masu sayayya. (Zainab Zhang) ...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas...
Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci...
Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar...
Sanarwar ta kuma zayyana matakan fadada adadin shaguna masu iya mayar da kudin haraji domin bunkasa samar da kayayyaki da hidimomi masu ruwa da tsaki. Haka kuma, za a kara kafa kantunan sayar da kayayyaki masu mayar da kudin haraji ga baki a manyan wuraren sayayya da gefen tituna da wuraren bude ido da...
Haka zalika, mazauna jihohin da abin ya shafa, sun koka kan wasu abubuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da sauran makamantansu. Masu Sayar Da Ruwa Sun Kara Farashi A Kano A Jihar Kano, wani mazaunin unguwar Hotoro ta Arewa, a Karamar Hukumar Nassarawa, Malam Gambo Muhammad, ya ce; ana sayar da kowacce jarka daya kan...
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri...
Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas...

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa. Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2...
Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya...

Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata...
Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe. A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan,...

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Amnesty International Ta Ce; Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ba Ta Dace Da Bincike Laifukan Sojojinta Ba
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin Mamayar Isra’ila ta tabbatar da cewa ba za a amince da ita ba a duk wani bincike laifukan sojojinta Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta tabbatar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta sake tabbatar da rashin sahihancinta wajen binciken laifukan...
Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu...
Shugaban NDLEA, Brig.-Gen. Mohamed Buba Marwa, ya yaba wa jami’an hukumar bisa ƙoƙarinsu wajen yaki da magungunan da kwayoyi na haram, yana mai kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abu da ke shafar safarar magunguna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi...
Dakarun gwagwarmayar Yemen sun kaddamar da hare-haren daukan fansa kan yankin Jaffa da ke kusa da birnin Tel Aviv na Isra’ila Dakarun gwagwarmayar Yemen sun sanar da aiwatar da wasu matakan soji masu inganci kan yankin Jaffa da aka mamaye, da kuma kan jiragen ruwan Amurka masu dauke da jiragen saman yaki na Truman da...
Gao ya kara da cewa, Sin da kasashen Afirka sun zamo misali na bunkasa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, suna kuma gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil’adama, kana sun nunawa duniya cewa kasashe masu tasowa na da ikon samar da sabon salon wayewar kan bil’adama na kashin kan su, kuma za su...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin...
Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan...
Shugaban ofishin siyasa na Hamas Khalil al-Hayya ya sanar da cewa, kungiyar a shirye take ta shiga cikin tattaunawa don tabbatar da cimma cikakkiyar yarjejeniyar musayar fursunoni, da tsagaita bude wuta a Gaza, da janyewar Isra’ila daga yankin, da kuma kaddamar da yunkurin sake gina yankin. A cikin wani jawabi da kungiyar ta fitar, al-Hayya...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku. Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce...
Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp