2025-11-21@22:35:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9199

«Ingantuwa»:

    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta tabbatar da bada cikakken goyon bayanta ga Kwalejin Aikin Noma ta Gwamnatin Tarayya da ke Kirikasamma. Gwamna Umar Namadi ya bayar da wannan tabbaci ne lokacin da ya karɓi tawagar gudanarwar kwalejin ta farko, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Dr. Muhammad Yusha’u Gwaram, yayin ziyarar girmamawa da suka kai...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga...
    Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci. Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi  Zargi: Majalisar Kano ta dawo...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe...
    Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta wanke Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano da aka dakatar, Alhaji Naziru Yau, daga dukkanin zarge-zargen da aka masa. Wannan ya ba shi damar komawa bakin aikinsa da shugabancin Ƙaramar Hukumar Rano. An kama Faston da ake zargi da yi wa mambobin cocinsa 3 fyade ’Yan bindigar da suka sace masu ibada...
    Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin...
    Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da sace ɗalibai da ma’aikatan makarantar Katolika ta Saint Mary da ke Papiri, da ke Ƙaramar Hukumar Agwara da jihar. Aminiya ta rawaito yadda ’yan bindiga suka kutsa cikin makarantar tsakanin ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na safiyar Juma’a. ’Yan bindiga sun sace dalibai a wata makarantar Neja ’Yan bindigar da...
    ’Yan bindiga sun kai hari makarantar Katolika ta St. Mary da ke cikin yankin Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, sannan suka sace ɗalibai da malaman da ba a kai ga tabbatar da adadinsu ba. Har zuwa yanzu dai babu cikakkun bayanai a kan harin, amma majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa an...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya.   Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da...
    Rundunar ƴansandan jihar Neja ta ce tuni ta aika jami’ai yankin da aka sace wasu ɗalibai da ba a san adadin su ba har yanzu domin kuɓutar da su. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP W. A Abiodun ya fitar, ya ce an aika jami’an tsaro da haɗin gwiwar sojoji da sauran...
    Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u ‘Yan bindigar da suka sace masu ibada 38 a Cocin Christ Apostolic Church (CAC), Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a Jihar Kwara sun nemi kudin fansa na Naira miliyan 100 kan kowane mutum daya da suka sace. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa masu garkuwan sun fara kiran iyalan waɗanda aka...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka...
    Daga Usman Muhammad Zaria Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha. Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar...
    Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa...
    Daga  Khadijah Aliyu  Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu samari bakwai da ke shiga irin ta mata da aikata badala a wani shahararren gurin nishadi da ke kan titin Zoo Road a karamar hukumar Kano Municipal. Yayin tabbatar da faruwar lamarin ga Rediyon Nijeriya, Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
      Kungiyar Haɗin Kan Masu Kiwo na Gargajiya ta Afirka (CORET) tare da haɗin gwiwar ECOWAS sun hada matasan da aka horar da su da manyan abokan holda don bunkasa kiyo da bunkasa yawan madara a jihohin Kaduna da Jigawa.   A yayin zaman karawa juna sani a Kaduna, Koodinetan Aikin na CORET Dr. Umar...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga,...
    Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar da sunayen sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar matasa, wanda hakan ya ƙara yawan ma’aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin. Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta...
    Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi wasiƙa daga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 wanda ya kai Naira tiriliyan 1, irinsa na farko a tarihin jihar. Za a gabatar da kudurin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamban 2025. Wasiƙar, wadda Kakakin Majalisar, Alhaji Jibril...
    Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da sace dalibai ashirin da biyar daga Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu. Lamarin ya faru ne a daren Litinin da misalin ƙarfe 4 na safe a lokacin da ƴan bindiga suka mamaye makarantar, inda suka kashe wani...
    Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban...
    Rahotanni daga birnin Tehran sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadawa masana tattalin arziki cewa Tehran a shirye take na yi duk wata yarjejeniya idan dai za’a tsage gaskiya, kuma iran ta kara karfafa dakarunta wajen kasancewa cikin shirin ko ta kwana musamman ma bayan yakin kwanaki 12 da aka...
    Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.  Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da  kasar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yarjejeniyar Alkahira tsakanin Iran da IAEA ba ta da inganci Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Iran ta sanar da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) cewa: Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar, yana mai nuni da cewa...
    Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale. Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara...
    Hukumar Zakka ta Jihar Zamfara ta sanar da shirye-shiryen aurar da marayu 200 ’yan asalin jihar a wani yunƙuri na tallafa wa marasa galihu. Sakataren hukumar, Malam Habibu Balarabe ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da bikin auren a ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2025, a harabar hukumar...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a...
    Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU....
    Mahukunta a Jahar Kwara sun sanar da rufe makarantu a garuruwan Ifelodun,Ekiti, Irepodun, Isis, da Oke Ero, saboda matsalolin tsaro da ake fuskanta Kwamishinan ilimi na Jahar ta Kwara Lawal Olohungabebe ne ya sanar da daukar wannan matakin saboda abinda ya kira bayar da kariya ga rayuwar daliban da suke fuskantar barazanar masu dauke da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Gwamnatin Jihar Kwara ta bayar da umarnin rufe makarantu a ƙananan hukumomin jihar guda huɗu na saboda ƙaruwar hare-hare a jihar cikin sa’o’i 48 da suka gabata. Aƙalla mutane uku sun mutu a garin Bokungi da ke Ƙaramar Hukumar Edu a ranar Laraba. Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas...
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza....
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya  domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen...
    Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda...
    Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman ma game da rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Addis...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.