2025-09-19@10:43:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9079
«a kudancin kasar»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ali Larijani, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, hanyar yin shawarwari da Amurka tana nan a bude, duk kuwa da takun sakar diflomasiyya da ake yi. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X, Larijani ya jaddada cewa “hanyar tattaunawa da Amurka ba a rufe ta ba,” yana mai jaddada cewa Iran “tana bin shawarwari ne na hankali.” Babban jami’in na Iran ya nanata cewa Washington na gabatar da bukatu da ke kawo cikas ga tsarin shawarwarin tun daga farko. Ya kara da cewa, Amurka ta gabatar da batutuwan da ba za a iya cimma matsaya a kansu ba, kamar rage karfin makamai masu linzami na Iran, inda ya ce wannan da ma wasu...
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dala biliyan 2.5 da gwamnatin kasar Habasha, domin gina daya daga cikin manyan masana’antun takin zamani a duniya a garin Gode. An rattaba hannu kan yarjejeniyar tsakanin rukunin Dangote da kamfanin zuba jari na Habasha (EIH), wanda zai baiwa rukunin Dangote damar rike hannun jarin kashi 60 cikin dari, yayin da EIH zai rike kashi 40 cikin dari. Ana has ashen cewa idan an kammala aikin, zai kasance cikin manyan masana’antun samar da takin zamani guda biyar na duniya, wanda zai rika samar da takin zamani ton miliyan uku a kowace shekara. A cewar EIH, za a kammala aikin a cikin...
Jami’an Iran sun yaba matuka da irin nasarorin da aka samu a yayin halartar shugaban kasar Mas’ud Pezeshkian a taron kungiyar Shanghai (SCO) a kasar China. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Kazem Gharibabadi ya bayyana cewa, Iran ta yi amfani da tsarin diflomasiyya a bangarori daban-daban a yayin taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) na shekara-shekara a kasar Sin. Gharibabadi ya bayyana hakan a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon shafin Twitter a jiya Talata, inda ya yi bayani kan abubuwan da suka shafi taron, wanda shugaba Masoud Pezeshkian, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin ya aiwatar da su. A cewar jami’in diflomasiyyar, halartar babban jami’in gudanarwa na kasar Iran a taron ya...
Rundunar sojin Yaman ta sanar da cewa ta kaddamar ad wasu manyan hare-hare a kan wasu mihimamn wurare na tsaro da tattalin arzikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Tun a ranar Litinin da ta gabata ta sanar da cewa za ta aiwatar da ayyukan soji biyar masu girma a kan wasu muhimman wurare da suka hada da hedikwatar tsaro, tashar wutar lantarki ta Hadera, filin sauka da tashin jiragen sama na Lod da ke Jaffa ko Tel Aviv, da kuma tashar jiragen ruwa ta Ashdod, da kuma tashr jiragen ruwa ta MSC ABY da ke arewacin tekun Bahar Maliya. An gudanar da ayyukan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka da dama da kuma makamai masu linzami. Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya...
Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar rayukan da za su kai sama da miliyan 100, wadanda daga cikinsu sojoji da fararen hula miliyan 35 ne Sin ta yi asara. Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da wannan mummunar akida ta mulkin danniya, yayin da ta shiga cikin sahun sojojin sauran kasashe a yakin duniya na biyu. Kafada da kafada suka yi gumurzu wajen murkushe maharan kasashen Japan, Jamus da...
Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata. A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu. A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma. Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da...
Babban sakataren MDD António Guterres, wanda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwar Shanghai wato SCO da aka gudanar a birnin Tianjin dake kasar Sin, ya bayyana cewa, Sin ta taka rawar gani sosai wajen cimma nasarar yakin duniya na biyu. Kuma gudummawar da Sin ta bayar ita ce mabudin nasarar da kawancen kasashen duniya suka samu a yakin duniya na biyu. Bugu da kari, Guterres ya jaddada ta hanyar nuna batutuwan tarihi cewa, babbar mamayar da Japan ta yi wa Sin ita ce farkon yakin duniya na biyu na gaskiya. Guterres ya yi imanin cewa, tsayin daka da kasar Sin ta yi wajen yin tir da hare-haren Japan, ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru da dama, tare...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar Litinin 8 ga Satumba, 2025 ne gwamnatin jihar Kano za ta kaddamar da sabuwar majalisar Shurah, karkashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf. Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnati dake Kano. Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a 2 ga Satumba, 2025. Xi: Alakar Sin Da Rasha Ta Zama Misali Na Kyakkyawar Dangantakar Manyan Kasashe Sabuwar Ajandar Kasar Sin Ta Inganta Magance Gibin Kudi A Duniya Kafa majalisar Shurah na zuwa ne domin karfafa gudanar da mulki cikin hadin kai, da bayyana gaskiya wajen yanke shawara. Ana sa ran majalisar za ta kasance kamar wata kungiya mai ba da...
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce alakar Sin da Rasha ta zama misali na kyakkyawar dangantaka tsakanin manyan kasashe, wadda ke kunshe da ingantaccen yanayin kawance na makwafta, da cikakken salon tafiya tare bisa manyan tsare-tsare, da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin zantawarsa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Beijing. A nasa tsokacin kuwa, shugaba Putin ya ce shawarar da shugaba Xi ya gabatar game da tsarin shugabancin duniya ta zo a lokacin da ake matukar bukatarta, kuma wajibi ne a yi aiki da ita, kana za ta taka muhimmiyar rawa wajen magance gibin dake akwai a tsarin shugabancin duniya. Ya ce a nata bangare, Rasha a...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hakimin Bagaji Odo a Karamar Hukumar Omala ta Jihar Kogi, David Wada. Rahotanni sun ce basaraken ya faɗa tarkon ’yan bindigar ne a ƙauyen Ojuwo Ugweche da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Litinin, yayin da yake dawowa daga taron sarakunan gargajiya a Abejukolo, hedikwatar ƙaramar hukumar. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Wani mazaunin yankin, Maji Ahiaba, ya bayyana cewa a ’yan kwanakin nan ƙauyen Ojuwo Ugweche na fuskantar hare-haren masu ta’adar garkuwa da mutane, duk da cewa a baya an taɓa tura jami’an tsaro da ’yan sa-kai...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya kuma umarci da a maido da babban daraktan yada labarai, Mista Ayo Adewuyi ya kammala wa’adinsa na ragowar shekaru uku, wanda zai kare a shekarar 2027. Shugaba Tinubu ne ya nada Adewuyi a shekarar 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. Gwamnatin Kano za ta sake yi wa zawarawa da ’yan mata auren gata Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace wa wani Usman...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin. Wannan ajanda, ta nuna hanyar da za a bi, tare da ba da jagoranci ga aiwatar da ayyukan gina tsarin mulkin duniya mai adalci da dacewa, a karkashin yanayin duniya mai fuskantar manyan sauye-sauye, da kuma jagorancin cike gibin kudi na samar da ci gaba da bunkasa. Sabuwar ajandar mulkin duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta yi magana kai tsaye kan wasu muhimman abubuwa guda uku a tsarin jagorancin duniya, wato rashin daidaiton iko, da rarrabuwar ra’ayoyi, da kuma rashin daukar matakai. Ajandar, wadda ta fitar da wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar wa auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Zabarmawa Sun Bayyana Dalilin Bai wa Gwamnan Kebbi Sarautar Garkuwa Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni tana shiryawa. Tun bayan hawansa mulki...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Idan ba a haɗa kai ba, munanan manufofin Amurka za su haɗa har da kasar China Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: Idan kasashe ba su hada kai ba, Amurka za ta aiwatar da munanan manufofinta na fadada ayyukan da take amfani da su a yau, ta hanyar jefa bama-bamai, da kisan gilla, da kakaba takunkumi kan al’ummomi, da zasu hada har da kasar China ma. A yayin ziyararsa a kasar China, shugaban kasar Iran ya yi hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, inda ya jaddada bukatar tunkarar siyasar bangare guda ta Amurka. Yana mai cewa: Idan ana son a kaucewa siyasar bangare guda ta Amurka, dole ne a aiwatar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yammacin Turai sun fara amfani da takunkumi kan kasar Iran bisa umarnin ‘yan sahayoniyya da Amurka Dangane da matakin da kungiyar gungun Turai ta dauka na son sake dawo da takunkumin da ya shude kan kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Kasashe uku na Turai ne suka fara aiwatar da shirin sanya takunkumi bisa umarnin ‘yan sahayoniyya da Amurka. Baqa’ ya fara taron manema labarai na mako-mako da jajantawa al’ummar Yemen da Falastinawa, yana mai cewa: “A yayin da ake gudanar da juyayin shahadar fira ministan kasar Yemen da kuma wasu ministocin kasar a matsayin wani bangare na wuce gona da iri na sojojin ‘yan...
Majalisar shawarar Musulunci ta gudanar da zama na musamman don tattauna hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen takaddamar neman sake dawo da tsohon takunkumi kan kasar Iran Kakakin fadar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya sanar da matakin da babu makawa Iran za ta dauka kan domin kalubalantar matsayin gungun tawagar Turai Troika, yana mai jaddada cewa: Dukkanin jam’iyyun siyasa a majalisar dokokin kasar sun amince cewa tilas ne martanin Iran ya kasance mai azanci da mai da martani, lamarin da zai wurga makiya cikin nadama. Abbas Goudarzi kakakin fadar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya yi ishara da zama na musamman da aka yi a yau Talata a yayin wani taron manema labarai, inda ya...
Kwace makaman kungiyar Hizbullah… Fadan ne da ba zai yi nasara, inda daga karshe zai zame siyasa bayan gazawar nuna karfi Ana ci gaba da tabka muhawara kan batun neman kwance damarar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Labanon, a daidai lokacin da ‘yan sahayoniya da Amurka ke kokarin cimma wannan buri a siyasance bayan gazawarsu ta hanyar nuna karfin soji. Shugaban kasar Labanon Joseph Aoun ya yi imanin cewa; Kwance damarar kungiyar Hizbullahi ya dogara ne da samar da sharuddan da suka dace. A nasa bangaren, shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri ya yi watsi da duk wata barazana, yana mai kallon makaman ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi a matsayin abin daukaka da alfahari. A halin da ake ciki kuma,...
Majiyar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 na daban suka jikkata a Gaza cikin sa’o’i 24 Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin mutanen da suka yi shahada sakamakon yakin kisan kiyashi da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 ya karu zuwa shahidai 63,633, tare da jikkatan wasu 160,914. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun cewa: Falasdinawa 76 ne suka yi shahada yayin da wasu 281 suka jikkata a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, a cewar alkalumman baya-bayan nan da ma’aikatar ta...
Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta ne domin nuna gamsuwa da irin ci gaban da Gwamna Idris ya kawo wa talakawa. Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire “Mun tuntubi mutane da yawa kafin a zaɓe shi, kuma kowa ya tabbatar cewa shi ya cancanta.” A nasa jawabin, Sarkin Zabarmawa na Jihar Kebbi, wanda kuma shi ne tsohon...
Bugu da kari, kasashe membobin kungiyar sun amince da kafa bankin bunkasa harkokin SCO, wanda a cewar Wang, zai yi matukar bunkasa samar da ababen more rayuwa, da raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummun kasashe membobin kungiyar. Dadin dadawa, kasar Sin ta sha alwashin kafa sabon dandalin hadin gwiwa, da cibiyoyi masu nasaba da makamashi, da samar da ci gaba marar gurbata yanayi, da tattalin arzikin dijital, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da ilimi mai zurfi, da na koyar da sana’o’i da fasahohi. An kuma fitar da tsarin ingiza ci gaba mai inganci, wanda ya kunshi sassa irinsu na makamashi, da masana’antun sarrafa hajoji ba tare da gurbata yanayi ba, da tattalin arzikin dijital, da kirkirarriyar basira ko AI da...
Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya da ke Sakkwato ta bayyana aniyar karrama Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli CFR, da lambar yabo ta musamman saboda rawar da ta ce yana takawa wajen ƙarfafa haɗin kai da raya zumunci tsakanin ’ya’yan Daular Usmaniyya. A cikin sanarwar da cibiyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun shugabanta kuma Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ta ce za a karrama Sarkin tare da wasu fitattun ’yan Najeriya guda shida a babban taron shekara-shekara da cibiyar ke shiryawa. Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Taron zai gudana ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Satumba, 2025, a Cibiyar Karatun Alƙur’ani...
Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatu na makarantun firamare zuwa sakandire wanda zai fara aiki a sabon zangon karatu na bana da za a soma a watan Satumbar nan. Wannan na zuwa ne bayan kammala nazari mai zurfi kan manhajoji karatu a fannin ilimi a matakin farko da na manyan makarantun sakandire da kuma fannin fasaha. Manchester City ta ɗauki golan PSG, Gianluigi Donnarumma Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Gwamnatin ta ce ta ɗauki wannan matakin ne da nufin rage nauyin karatu kan ɗaliban da kuma inganta tsarin koyarwa a faɗin ƙasar. Ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id Ahmad, ce ta bayyana hakan a madadin Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa a ƙarshen...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta ɗauki mai tsaron ragar PSG, Gianluigi Donnarumma ɗan asalin ƙasar Italiya. Donnarumma wanda tsohon mai tsaron ragar AC Milan ne ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyar a Etihad, inda zai zai ci gaba da tsare ragar ƙungiyar zuwa kakar 2030. Ndume ya koka kan sabbin hare-haren Boko Haram a Borno Kemi Badenoch ta shiga tsaka mai wuya kan karatun likitanci Golan zai riƙa amfani da riga mai lamba 99 domin ranar haihuwarsa ta 1999, kamar yadda ƙungiyar ta sanar. A jawabin da ya yi dangane da komawa ƙungiyar, Donnarumma ya ce yana cike da farin ciki da jin daɗi. “Na koma ƙungiya da ke cike da zaratan ’yan wasa, sannan kuma ƙungiya...
Hukumar NDLEA a Kano ta kama kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na ɗauke da ƙwayoyi, tare da tabar wiwi guda 48. An cafke wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, bayan an gano kayan a cikin tirela ɗauke da kekuna a kan hanyar Zariya zuwa Kano a Gadar Tamburawa. ’Yansanda Sun Kama Masu Safarar Makamai A Katsina, Sun Ƙwato Makamai ’Yansanda Sun Kama ‘Yan Daba 107 A Kano, Sun Ƙwato Makamai Da Ƙwayoyi NDLEA ta ce tana tsare da wanda ake zargin da kuma kayayyakin, yayin da ake ci gaba da bincike. Hukumar ta buƙaci jama’a su riƙa sanar da ita duk wani abin da suka zarga na da alaƙa da miyagun ƙwayoyi. Daga kanmu, magana ta...
Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu. Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen. Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin. Sai dai kuma Sanata Ndume...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da kissan da sojojin HKI suka yiwa firay ministan kasar Yemen Ahmad Al-Rahawi da wasu jami’an gwamnatinsa. Ya kuma kara da cewa irin wadan nan hare-haren suna zagon kasa ga zaman lafiya a duniya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani sakon da ya aika ga gwamnatin kasar Yemen da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin na marasa imini, wanda sojojin HKI suka yi. Ministan ya yaba da yadda kasar Yemen ta tsaya kan kafafuwanta wajen taimakawa mutanen Gaza wadanda ake zalunta. Aragchi ya ci gaba da aibata MDD kan rashin daukar mataki kan HKI a yayinda an kusan...
Mutanen sudann daga yammacin kasar kimani dubu guda ne suka raya rayukansu sanadiyyar zai-zayar kasa, kuma kan tsaunukan Marre. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto Abdulwahid Muhammad Nour na kungiyar ‘The Sudan Libration Movementa’ Wato (SLM) wacce take iko da yankin yana fadar haka. Ya kuma kare da cewa, zaizeyar kasa ta aukune bayan ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya a yankin. Ya kuma kammala da cewa mutum guda ne kacal ya tsira da ransa a garin Marra dake kan tsaunin. Kungiyar ta bukaci taimakon MDD da kuma sauran kungiyoyin Agaji a duniya don fidda gawakin mutanen da zaizayar kassar ta bisne a kan tsaurin. Kasar Sudan dai tana cikin yaki fiye da shekaru...
Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi na Najeriya (ALGON), ta yi kira ga Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Rubuta Labaran Wasanni (SWAN) da ta ƙara mayar da hankali wajen yada labarai kan wasannin gargajiya, irin su langa da kokawa. Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe wanda shi ne shugaban ALGON reshen Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da shugabannin SWAN na jihar suka kai masa ziyarar ban girma, inda suka nemi goyon bayansa kan babban taron bita da ƙungiyar ke shirin gudanarwa. A cewarsa, ƙara bayar da muhimmanci ga wasannin gargajiya zai taimaka wajen jan hankalin matasa zuwa harkokin ci-gaban rayuwa, tare da rage yawan fadawa cikin laifuka da shan miyagun ƙwayoyi. Ya kuma shawarci SWAN da ta ƙulla alaƙa...
Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin. Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin. Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa...
Gwamnatin kasar Belgium ta bada sanarwan cewa zata bayyana amincewarta da samuwar kasar Palasdinu mai cikekken yenci, a babban taron MDD a cikin wannan watan a birnin NewsYork. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Belgium Maxime Prevot yana fadar haka a shafinsa na X a yau Talata. Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu dai sun rika sun dauki matakan kakabawa HKI wasu takunkuman tattalin arziki saboda kissan kare dangin da takewa al-ummar Falasdinu a gaza.. A cikin watan Yulin da ya gabata shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa kasarta zata amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta, kafada da kafada da HKI. Bayan haka ne wasu kasashen turai da...
Kasar Venezuela ta sami sakon tallafi daga kasar Iran a lokacinda ministan harkokin wajen kasar Vanezuela ya gaba da jakadan Iran a Caracas. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun bayyana cewa zasu kara karfafa dangantaka ta musamman dake tsakaninsu na tsaro da sauran bangariri masu musammancin da ke tsakaninsu. Saboda kare diyaucinsu da kuma iko a kan kasashensu. Ministan harkokin wajen Venezuela Efan Jeel ya bayyana cewa sun tattauna da Jakadan Iran a Venezuela Ali Shagni a ranar litinin da ta gabata. Ministan ya kara da cewa Venezuela ta sami sakon tallafawa daga kasar Iran don tunkarar barazanar da kasar take fuskanta daga kasar Amurka. Share 0 0 votes Article...
Ta ce cikin ƙasa da shekara biyu, Kaduna ta fito daga durƙushewar tsari zuwa zama jihar da ake ganin tsari. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa El-Rufai ya ƙara ƙoƙarin tayar da rikici bayan abokan siyarsarsa sun sha kaye a zaɓen cike gurbi na ranar 16 ga watan Agusta. Ta ce sakamakon ya nuna rashin amincewa da salon mulkin El-Rufai na “rabuwar kai da wariya” tare da amincewa da salon mulkin Gwamna Uba Sani. An yi ƙoƙarin jin ta bakin El-Rufai kan waɗannan zarge-zarge, amma ba a iya samun shi ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Al’ummar kurame sun koka bisa matsalolin da suke fuskanta a fannin kiwon lafiya, sakamakon rashin masu yi musu fassara a asibitoci a Jihar Yobe. Malam Kolo Abba, Shugaban Ƙungiyar Kurame a Ƙaramar Hukumar Damaturu, ya ce kurame majinyatan sukan koƙarta wajen fahimtar ƙa’idojin likitoci da na kiwon lafiya, amma duk da hakan suna cikin haɗari. Abba ya yi wannan kira ne ta bakin wani mai fassara a taron masu ruwa da tsaki kan shirye-shiryen tattaunawa kan kasafin kuɗin shekarar 2026 da aka shirya don inganta aiki. Ya ce rashin masu fassara a asibitoci alama ce ta rashin kula da kurame a jihar, don haka akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don tabbatar da samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum...
’Yar Najeriya kuma Shugabar Jam’iyyar Conservative a Birtaniya, Kemi Badenoch, ta shiga tsaka mai wuya kan iƙirarinta na cewa Jami’ar Stanford ta ba ta gurbin karatun horon shiga likitanci bisa rangwamen kuɗi tun tana ’yar shekara 16. An fara sanya alamar tambaya a kan iƙirarinta ne bayan da wani tsohon jami’in kula da ɗaukar ɗalibai a jami’ar mai suna Jon Reider, ya musanta iƙirarin na Kemi Badenoch, wadda ta yi kaurin suna wajen sukar ƙasarta ta haihuwa. Kemi Badenoch ta yi iƙirari cewa ta samu gurbin ƙaramin tallafin kuɗi daga Jami’ar Stanford, amma rashin kuɗin iyayenta ya hana ta amfani da damar. Sai dai Jon Reider, wanda a lokacin yake kula da ɗalibai daga ƙasashen waje da tallafin karatu a Stanford,...
Kan batun yiwuwar Obi zai koma PDP, Wike ya yi watsi da shi, ya ce hakan zai jawo wa jam’iyyar matsala. “Obi ya zargi PDP, ya ce jam’iyyar ta lalace. Yanzu kuma jam’iyyar ta gyara kenan a gare shi? Wannan zai kashe jam’iyyar,” in ji shi. Wike ya ce dawo da Obi saboda kawai neman mulki zai rusa ƙa’idoji da mutuncin jam’iyyar. Ya dage cewa hanyar da PDP za ta sake bi domin farfaɗowa ita ce bin tsarin rabon mulki, adalci da gaskiya, ta yadda shugabancin ƙasa zai koma Kudu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Rahotanni sun bayyana cewa Kotu a kasar Finland ta yanke wa dan Najeriya mai ‘rajin kafa kasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci. Kotun ta same shi da laifin koƙarin harzuka jama’a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan kungiyar ta’addanci. Haka kuma ta same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara shida a gidan yari. Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi kokarin karfafa rajin kafa yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
An gudanar da janazar manyan jami’an gwamnatin kasar Yemen 9 da suka yi shahada a wani harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar a kansu,a lokacin da suke gudanar da wani zama na gwamnati, domin bin kadun ayyukan ma’aikatun da suke jagoranta. Dubban daruruwan mutane ne dai suka halarci janazar wadda ta gudana a birnin San’a fadar mulkin kasar ta Yemen a jiya, inda aka gabatar da jawabai daban-daban, da ke kara tabbatar da aniyar al’ummar kasar Yemen wajen ci gaba da bin tafarkin wadanda suka yi shahada, domin mara baya ga al’ummar Gaza mara kariya. A nasa bangaren Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan wannan hari na wuce gona da...
’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai masu haɗarin gaske, tare da tarin harsasai, a wani samame a Jihar Katsina. A farkon wannan mako ne ’yan sanda da ke sintiri suka tare wata mota ƙirar Volkswagen Golf, da asubahi, inda suka gano bindiga ƙirar GPMG da sauran makamai a cikinta a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku. Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya sanar da cewa masu safarar makaman matasa ne masu shekara 12 da kuma 25, daga ƙauyen Ɓaure a Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar. Makaman da aka gano Sun shiga hannun hukuma bayan da aka gano suna ɗauke da wata babbar bindigar sojoji mai haɗarin gaske, ƙirar GPMG. Jami’an sun...
shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana cewa, Aikewa da sojojin ruwan Amurka a yankin Caribbean itace barazana mafi girma ga al’ummomin yankin a cikin wannan karni. Da yake magana a wani taron manema labarai, Maduro ya ce an jibge jiragen ruwan sojan Amurka guda 8 dauke da makamai masu linzami 1,200 da kuma na nukiliya a gabar tekun Venezuela. Inda Ya kira wannan matakin da cewa shi ne mafi muni da Amurka ta dauka a tsawon shkaru a yankin Caribbean. Maduro ya zargi Washington da aiwatar da manufar matsin lamba ta soja a kan Caracas, wanda ya tilasta wa Venezuela ayyana cikakken shirin tsaron kasa. “Venezuela kasa ce mai zaman lafiya, amma al’ummarta mayaka ne kuma ba za su...

Araghchi : China da Rasha sun bi sahun Iran wajen kin amincewa da yunkurin E3 na dawo mata da takunkumai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a jiya a Shafin X, kwanaki hudu bayan da kasashen Turai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, sun yi amfani da tsarin dawo da dukkanin takunkumin MDD a kan Iran. Ya ce, a cikin wasikar hadin gwiwa da suka aike wa...
A lokacin wani taro da ya gudana tsakanin shugaban kasar iran Mas’ud pezeshkiyan da kuma babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio gutteres a kasar china ya bayyana cewa iran tana da hakkin ta mallaki fasahar nukiliya na zaman lafiya, kana ya nuna damawarsa game da batun takunkumi da kasashen turai ke son sake kakabawa iran, Wannan bayanin na Gutteres ya kara fito da matsayin iran a mataki na kasa da kasa na hakkin mallakar fasahar nukiliya domin ayyukan zaman lafiya, a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun tankiya tsakanin iran da kuma kasashin turai game da shirin ta na nukiliya da kuma yunkurin sanya mata takunkumai, A nasa bangaren shugaban kasar Iran Mas’ud pezeshkiyan ya bayyana cewa...
Tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami ya tsallake rijiya da baya a garin Birnin Kebbi yayin da wasu matasa suka kai wa tawagarsa hari. Abubakar Malami da tawagarsa, wasu ’yan bangar siyasa sun tare su, a unguwar GRA, inda suka yi amfani da sanduna da addun da sanduna suka farfasa motocin Malami tare da jikkata mutanensa, Kodayake babu asarar rai. Bayan dawowar tsohon ministan a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, gida ya yi zargin siyasa ce ta a da aka kai masa harin, yana mai jaddada cewa, harkar siyasarsa babu gudu babu ja da baya. “Shari’a ta tanadi ka kare kai, in aka kawo maka hari amma kai kar ka kai wa kowa hari, maganar siyasa ba gudu ba ja...
Kazalika, shugaba Xi ya yi kira da a yi kokarin hada karfi da karfe wajen kiyaye kyawawan sakamakon da aka samu bayan yakin duniya na biyu, da samar da karin alfanu ga daukacin bil’adama ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin shugabancin duniya, da gina al’umma mai makoma ta bai-daya ga bil’adama. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutum sama da 800 sun mutu, yayin da wasu fiye da 2,500 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6 da ta auku a lardin Kunar da ke gabashin Afghanistan, kusa da iyakar Pakistan. Girgizar ƙasar wadda ta auku da misalin ƙarfe 12 na daren Lahadi ta rusa gidaje da dama da aka gina da laka da duwatsu, lamarin da ya sanya dubban mazauna kwana a waje. Manchester United za ta ɗauki golan Antwerp, Senne Lammens An kama uba da ɗansa kan yi wa ’yar shekara 13 fyaɗe a Gombe Rahotanni sun ce yara da mata na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu, kuma tuni an yi jana’izarsu. Mai magana da yawun gwamnatin Taliban, Zabihullah Mujahid, ya bayyana fargabar...

Peng Liyuan Da Matan Shugabannin Kasashe Membobin SCO Masu Halartar Taron SCO Sun Ziyarci Kogin Haihe Na Tianjin
A yau ranar 1 ga watan Satumba da yamma, uwargidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matan shugabannin kasashe membobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO masu halartar taron kolin SCO na shekarar 2025 sun ziyarci kogin Haihe na birnin Tianjin tare. Peng Liyuan da sauran matan shugabannin sun hau jirgin ruwa tare da sauraran tarihin birnin Tianjin da yadda ya bunkasa. Peng Liyuan ta bayyana cewa, birnin Tianjin birni ne da ya hade dogon tarihi da zamani, kana kogin Haihe ya kasance tare da bunkasar birnin Tianjin da kuma al’adu daban daban, tana fatan za su ji dadi a yayin ziyarar. Dukkan bakin sun yaba da al’adun gargajiya masu kyau na kasar Sin, da kuma nasarorin da...
Mukaddashin daraktan ofishin bunkasa tattalin arziki, hada kai da raya cinikayya a hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka ta AU, mista Patrick Ndzana Olomo, ya ce nahiyar Afirka da Sin na da makoma mai haske a fannin raya hadin gwiwa, don bunkasa harkokin noma da shawo kan matsalar kamfar abinci a Afirka. Olomo, wanda ya yi tsokacin a ranar Juma’a yayin da ya ziyarci cibiyar gwajin fasahohin noma, inda kwararrun kasar Sin ke baje kolin fasahohin zamani na inganta noma dake birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha, ya ce kasashen Afirka da Sin na aiki tare wajen samar da gamammen tsarin bunkasa noma, wanda zai ingiza matsayin nahiyar Afirka zuwa ga cimma nasarar samar da isasshen hatsi da wadatuwar abinci....
Ya ba da tabbacin cewa, Majalisar za ta kara sanya ido domin tabbatar da gaskiya da rikon amana ga yadda ake sarrafa kudaden jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Shugaban Zimbabwe Ya Sauka Beijing Domin Halartar Bikin Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Mamayar Dakarun Japan
A yau Litinin shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya iso birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin domin halartar bikin cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin kin mamayar dakarun Japan, da yakin kin tafarkin murdiyya na duniya. Shugaba Mnangagwa ya sha ziyartar kasar Sin, inda a shekarar da ta gabata ma ya zo birnin Beijing domin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC tare da gudanar da ziyarar aiki a kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC) sun cafke wani mutum mai shekaru 48, Ibrahim Haruna, tare da ɗansa mai shekaru 15, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 13 fyaɗe a unguwar Jekadafari da ke Jihar Gombe. Wakilinmu ya ruwaito cewa an gabatar da waɗanda ake zargin ne a hedikwatar hukumar a ranar Litinin. An kama ɗan shekara 60 kan yi wa mai shekara 24 fyaɗe Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Mai magana da yawun hukumar a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya ce bisa binciken da suka gudanar, uban da ɗan sun aikata laifin ne a lokuta daban-daban. A cewarsa, Ibrahim Haruna wanda tela ne ya yi aika-aika ne a shagonsa na ɗinki, yayin...
Ya bayyana cewa, matan sun fito ne daga jihohin Kano, Katsina, Borno, Jigawa, da Zamfara, inda aka yi musu alkawuran samun ingantattun ayyukan yi a kasar ta Saudiyya. An kama daya daga cikin wadanda ake zargi da safarar matan mai suna Mohammed Saleh mai shekaru 45 da haihuwa. Babale ya ce, ana ci gaba da kokarin damke wasu da ake zargi da hannu wajen safarar mutanen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki. A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin...
Shawarar da Iran ta gabatar ga kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai zai durkusar da darajar kudin dalar Amurka A jawabin da ya yi a wajen taron kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai a kasar China, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ba da shawarar kafa tsarin hada-hadar kudi ga kungiyar da rage dogaro da kudin dala. A rana ta biyu ta taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 25, wanda aka shirya a birnin Tianjin na kasar China, tare da halartar shugabannin kasashe fiye da 20, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, da inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi, domin dakile illar da takunkumin da ake kakaba wa kasashe na bangare guda zai haifar....
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za...
Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Afghanistan ya haura 800, yayin da ake sa tsammanin karuwar wadanda suka jikkata Hukumomin kasar Afganistan sun sanar da cewa: Adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a gabashin Afghanistan ya haura 800, yayin da sama da 1,500 suka jikkata, adadin da ake sa ran zai karu. Da sanyin safiyar yau Litinin ne, kamfanin dillancin labarai na RTA ya ruwaito hukumomin lafiya na kasar na cewa, suna ci gaba da kokarin gano hakikanin adadin wadanda suka mutu, yayin da suke ci gaba da kokarin isa wasu yankunan da lamarin ya shafa. Ma’aikatar lafiya ta kasar ta sanar da cewa, Girgizar kasar ta lalata kauyuka uku a gundumar Konar gaba...
Dakarun Kai Daukin Gaggawa ta kasar Sudan sun kai hare-hare kan sansanin Abu Shouk da ke birnin El Fasher da manyan bindigogi Majiyar sojojin Sudan ta shaidawa gidan talabijin na Al Jazeera cewa, dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) sun yi luguden wuta kan sansanin ‘yan gudun hijira na Abu Shouk da ke El Fasher, babban birnin arewacin Darfur a ranar Litinin. Haka zalika majiyoyin ba su bayar da alkaluman hasarar dukiya ko hasarar rayukan mutane da aka yi a sansanin ba, wanda mazauna sansanin ke fama da matsananciyar rayuwa. Ofishin kai daukin gaggawa na sansanin ya tabbatar da cewa: Mazauna yankin na fama da karancin abinci, magunguna, da ruwa, wanda hakan ke shafar lafiyarsu da mayar...
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, wanda ya shigo kasar Sin don halartar taron koli na kungiyar hadin-kai ta Shanghai wato SCO na bana, ya zanta da dan jaridan babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a birnin Tianjin, inda ya ce, Xi Jinping shugaban kasa ne mai sanin ya kamata wajen tsara manyan tsare-tsare. Guterres ya ce, akwai misalai da dama da suke iya tabbatar da haka. Alal misali, shugaba Xi ya taba sanar da burin gina na’urorin samar da wutar lantarki bisa makamashin da ake iya sabuntawa, wadanda karfinsu ya zarce kilowatt biliyan 1.2 zuwa shekarar 2030 a kasar Sin, wanda aka riga aka cimma shi. Kazalika, ya yi alkawarin cimma nasarar kaiwa...
Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta kama wani dattijo mai shekaru 60, Ajayi Femi, bisa zargin yi wa wata budurwa mai shekaru 24 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, CSP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Lahadi. An kashe mutum 5 an sace limamai da hakimi a Sakkwato Simon Ekpa: An ɗaure ɗan Nijeriya kan laifin ta’addanci a Finland Ya bayyana cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu ta hannun sashen da ke bincike cin zarafin mata na rundunar da ke Ikeja. A cewar Hundeyin, lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Agusta, 2025, inda ƙanwar wacce abin ya faru da ita ta kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Meiran, daga nan...
Yayin da yake zantawa da ’yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, firaministan kasar Pakistan Shehbaz Sharif, ya bayyana cewa, Xi Jinping shugaban kasa ne mai matukar hangen nesa. A cewar firaministan, Xi Jinping, shugaban kasa ne wanda ke mayar da hankali sosai kan kyautata rayuwar jama’a, kuma a karkashin jagorancinsa, kasar Sin ta samu nasarar yaki da matsanancin talauci, al’amarin da ke bukatar matukar hangen nesa da babbar hikima. Kazalika, shugaba Xi yana amincewa da ra’ayin cudanyar sassan kasa da kasa. Firaminista Shehbaz ya kara da cewa, ba sauya yanayin tattalin arzikin kasar Sin kawai shugaba Xi ya yi ba, har ma ya mayar da kasar zuwa matsayi na biyu a karfin tattalin...
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya rushe majalisar kwamishinoninsa. Sakataren Yaɗa Labarai na gwamnan, Bologi Ibrahim, ya ce gwamnan ya sanar da rushe majalisar kwamishinoninsa ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jihar a safiyar Litinin ɗin nan. Ya kuma yaba musu bisa gudunmawar da suka bayar wajen kawo ci-gaba mai ma’ana a jihar tare da yi musu fatan alheri. Sai dai kuma gwamnan ya sake nada sakataren gwamnatin da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da mataimakinsa a da wasu jami’ai a kan muƙamansu
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan harkokin Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya musanta zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi cewa Gwamnatin Shugaba Tinubu tana biyan kuɗaɗen fansa ga ’yan bindiga don sako waɗanda suka sace. El-Rufai ya yi wannan zargi ne a wani shirin talabijin na Channels, inda ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya ta ƙara ƙamari, duk da cewa gwamnati ta yi ƙoƙarin rage yadda ake rahoto a kafafen watsa labarai. “Har yanzu ina kan bakata cewa waɗannan ’yan bindiga a halaka su baki ɗaya, ba a rika lallashi ko yin sulhu da masu ta’addanci ba. Wannan bai taba aiki a ko’ina ba,” in ji shi a yayin tattaunawar. Martanin ONSA A martanin da aka fitar da...
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sallami dukkan mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar. Gwamnan ya bayyana labari sallamar ta su ne a taron majalisar da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Minna, babban birnin jihar, da safiyar yau Litinin 1 ga Satumbar 2025 Girgizar Ƙasa Ta Kashe Sama da Mutune 600 A Afghanistan Daje Na Jam’iyyar APC Ya Lashe Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Neja Ya gode wa mambobin majalisar bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a duk inda makomar aiki ta kai su. Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa ya bar Sakataren Gwamnatin Jihar, da Shugaban Ma’aikatansa da kuma Mataimakinsa da wasu manyan jami’an ofishinsa a muƙamansu. Daga kanmu,...
’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja. A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu. “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace...
Ana jin tsaron daruruwan mutane ne suka rasa ransa sanadiyyar girgizan kasa mai karfin ma’aunin richter 6 da ta fadawa yankin tsaunuka na kasar Afganistan dake kan iyaka da kasar Pakisatan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran rauters na cewa an jirage masu saukar ungulu suna sauke wadanda suka ji rauni, sannan wasu suna taimaka masu suna daukansu zuwa cikin motocin daukar marasa lafiya. Majiyar kasar ta bayyana cewa da misalign tsakiyar dare ne girgizan kasar ta auku, sannan cibiyar kula da gargizan kasa ta kasar Jamus ta bayyana cewa karfin girgizan kasar ya kasar karfin ma’aunin richter 6.2. Dangane da wannan labarin kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar...
A safiyar yau litininn ce aka fara jan’izar shugaban gwamnatin kasar Lemen Ahmad Ghalib Arrahwi da ministocinsa da suka yi shahada a hareharen da HKI ta kai kansu a lokacinda suke taro a birnin San’a babban birnin kasar. Tashar talabijin ta al-amayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa an gudanar da taron janaizar ne a ‘dandalin 70 dake tsakiyar birnin San’a babban birnin kasar. Labarin ya bayyana cewa da farko an kai gawakin jam’an gwamnatin ne zuwa masallacin Jama’a, kuma sun hada da Firay ministan kasar Ahmad Ghalin da ministan watsa labarai Hashin sharafuddeen, ministan sharia, Mai sharia Mujahid Ahmad Abdullahi, ministan tattalin arziki da masana’antu Mu’in Almuhakiri ministan wutan lantarki da ruwa Ali saif Hassan Assami’ii, ministan noma...
Sojojin kasar Yemen sun bada labarin kai hari kan wani jirgin daukar man fetur na HKI a arewacin tekun maliya a safiyar yau litinin. Mai magana da yawun sojojin kasar ta Yemen Burgediya Yahyah Saree ne ya bada wannan sanarwan a wani jawabin da ya gabatar a faifai bidiya a safiyar yau Litinin, tare da amfani da makamai mai linzami samfurin Bailistik. Ya kuma tabbatar da cewa harin ya kai ga hadafinsa ya kuma wargaza jirgin ruwan na HKI dauke da manfetur zuwa haramtacciyar kasar. Gwamnatin kasar Yemen dai tana yaki da HKI tun bayan fara yakin tufanul Aksa a cikin watan Octoban shekara da 2023. Kuma HKI ta sha kaimata hare-hare, amma a wannan karon ta kai hare-hare kan...
Sojojin HKI sun kashe wata yar jarida mai aikiwa tashar talabijin ta “Qudsul- Yau” a wani harin da ta kai a zirin gaza. Islam Abed ta hadu da ajalinta a lokacinda jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan birnin gaza a jiya Lahadi da yamma. Wanda ya kara yawan yan jaridan da HKI ta kashe a wannan yakin Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ‘Al-asksal Yau’ tana yin All..wadai da HKI, sannan ta kara da cewa, kissan Islam Abed ba zai kawo karshen rahotannin da yan jaridu suke aikawa duniya dangane da ayyukan ta’addancin da HKI take aikatawa a gaza da kuma kasar Falasdinu da suka mamaye ba. Haka ma ofishin tashar talabijin ta Al-aksa a...
Hukumomin Afghanistan sun bayyana cewa adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasa da ta afku a gabashin ƙasar ya haura mutane 610, yayin da aka samu ƙarin mutane 12 da suka mutu a Nangarhar, abin da ya kai jimillar mutuwar zuwa 622. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta ce sama da mutum 1,500 ne suka jikkata a lamarin. Rahotanni sun nuna cewa asibitoci da dama, musamman na lardin Asadabad, sun cika da marasa lafiya. Shugaban asibitin, Dr Muladad, ya bayyana cewa suna karɓar marasa lafiya daga girgizar ƙasar “a duk bayan minti biyar,” kuma mutane 188 cikin sa’o’i kaɗan aka kawo asibitin, ciki har da mata da yara. Ya Zama Wajibi Amurka Ta Sauke Nauyin Dake Wuyan Ta Game Da...
Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala sanarwar a hukumance da misalin ƙarfe 7 na yamma. Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi A farkon tattaunawar, Newcastle ta dage cewa sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 kafin ta sayar da ɗan wasan, amma daga bisani...
Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Aƙalla mutum 610 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu sama da 1,300 suka jikkata sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta afku a ƙasar Afghanistan. Rahotanni daga hukumomi da kafafen watsa labarai na duniya sun ce ibtila’in ya auku ne a yankin gabashin ƙasar Afghanistan, kusa da iyakarta da Pakistan. Rahoton Hukumar Binciken Ƙasa ta Amurka (USGS) ya bayyana cewa ƙarfin girgizar ƙasar ta kai matakin 6.0, kuma cibiyar ta kasance a wani yanki mai tazarar kilomita 27 daga birnin Jalalabad, inda ake da yawan jama’a kimanin 300,000. An gano cewa girgizar ta afku a zurfin kilomita takwas kacal daga saman ƙasa, wanda hakan kan ƙara tsananta illarta. Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki...
Allah Ya yi wa Shugabar Ma’aikata ta Babban Birnin Tarayya, Abuja, Misis Grace Adayilo, rasuwa a safiyar Litinin ɗin nan. Shaidu sun tabbatar wa wakilinmu cewa ta rasu ne ’yan sa’o’i kaɗan da suka gabata. Kodayake kawo yanzu ba a sanar da rasuwar a hukumance ba. Misis Grace Adayilo ita ce mace ta farko kuma ’yar asalin yankin Babban Birnin Tarayya ta farko da ta riƙe wannan muƙami. ta kasance tsohuwar Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Birnin Abuja (AMAC), kafin Minista Nyesom Wike, ya naɗa ta Shugabar Ma’aikata. Rushe Kasuwar Alaba Rago: Ya kamata a biya ’yan Arewa diyya Gargaɗi kan zagin Sahabban Annabi Muhammad (SAW) Ita ce ta wakilci Wike a babban taron Majalisar Taro ta Ƙungiyar G-7 da...
Ya kuma tuna da tsohon abokin ajinsu wanda ya kasance tsohon Sufeton ƴansanda, marigayi Solomon Arase, wanda ya rasu a ranar Lahadi a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya. El-Rufai ya bayyana shi a matsayin mutum nagari, yana mai cewa tsarin ƴansanda na yanzu ya sha bamban da lokacin da Arase ya jagoranta. Daga ƙarshe, ya ce zai sake rubuta ƙorafi ga IGP da kuma hukumar kula da ƴansanda (PSC), yana mai gargadi cewa idan jami’an tsaro suka zama kariya ga masu tada fitina, to hakan zai kai ƙasa ga rugujewa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA). NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya. Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul Malik al-Houthi ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da Isra’ila ta kai a birnin San’a wanda ya kai ga shahadar firaministan kasar Yemen da wasu jami’an farar hula da dama. A cikin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin na jinjinawa shahidai, al-Houthi ya bayyana cewa, “laifi na kai hari kan ministoci da ma’aikatan farar hula ya kara tabbatar da laifukan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin,” yana mai jaddada cewa dukkan wadanda suka yi shahada suna gudanar da ayyukansu ne a fagagen da ba na soja ba. Da yake mika ta’aziyyarsa ga iyalan shahidai, abokan aikinsu, da al’ummar kasar Yemen, ya tabbatar da cewa wuce gona da...
Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa. A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan Lahadin cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na fadada Shirin da ake kira da Isra’ila Babba a cikin yankin kasashen Larabawa. Kasashen mambobi sun yi gargadin illar da wadannan buri ke ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya kara da cewa mambobin kawancen sun tsaya tsayin daka tare da al’ummar Palasdinu dangane da harin wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza, musamman yin Allah wadai da...
’Yar Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Khadijah, wadda aka fi sani da Andijo, ta rasu. Ta rasu a Abuja tana da shekara 35, kuma ta bar ’ya’ya uku. Trust Radio za ta fara watsa cikakkun shirye-shirye a ranar Litinin Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata An yi jana’izarta a fadar Sarkin Katsina ƙarƙashin jagorancin Imam Mustapha Gambo. Ɗaruruwan mutane sun halarci jana’izar, ciki har da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati da kuma al’ummar gari. Bayan kammala jana’izar, Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa mai tausayi kuma mai son zaman lafiya. Ya roƙi Allah Ya gafarta mata, Ya kuma bai wa iyalanta haƙurin wannan rashi. Haka kuma, Gwamnan...
Bugu da kari, a wannan rana shugaba Xi ya gana da shugabannin wasu kasashe da suka zo nan kasar Sin don halarar taron, ciki har da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, shugaban Azerbaijan Ilham Heydar oglu Aliyev, firayim ministan Armenia Nikol Pashinyan, shugaban Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov, da shugaban Maldives Mohamed Muizzu,da Firaministan Vietnam Pham Minh Chinh kana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidan rediyon Trust Radio mallakin kamfanin Media Trust Group, zai fara watsa cikakkun shirye-shiryenta a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba, 2025. Wannan na zuwa ne bayan tashar ta kammala gwajin watsa shirye-shiryenta tare da samun amincewar Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye na Ƙasa (NBC). Kilishiyar Waja ta tallafa wa matan gidan yari da kayayyaki a Gombe Gwamnatin Sakkwato za ta fara biyan masallatan Juma’a kuɗi duk wata Babban Daraktan Kamfanin Media Trust, Malam Ahmed I. Shekarau ne, ya bayyana wannan ci gaba. Ya bayyana hakan a matsayin abin alfahari, inda ya ce Trust Radio za ta mayar da hankali kan yaɗa shirye-shirye na gaskiya, adalci da kuma abin da ya shafi jama’a. Za a riƙa watsa shirye-shirye daga Abuja...

Xi Jinping Da Uwargidansa Peng Liyuan Sun Shirya Liyafar Maraba Da Baki Na Kasa Da Kasa Ga Mahalarta Taron SCO
Shugaba Xi ya yi imanin cewa, kungiyar SCO za ta ba da karin gudunmawa wajen samun ci gaba, da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe membobinta, da tara karfin kasashe masu tasowa, da kuma taimaka wa ci gaban wayewar kan dan Adam, a karkashin hadin gwiwa na dukkan bangarori. Kafin liyafar maraba, Shugaba Xi da madam Peng Liyuan sun yi maraba da shugabannin kasashen waje da matansu cikin fara’a, inda suka mika musu hannu tare da gaisawa, kuma suka dauki hotuna tare da su.(Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ruhi mai karfi da aka samu a lokacin yakin turjiyar ya kasance wani muhimmin ginshiki mai karfi, wanda ya jagoranci jama’ar kasar Sin zuwa shawo kan wahalhalu da cikas a yunkurinsu na farfado da kasa, kamar yadda makalar ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jaddada Muhimmancin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada muhimmancin aiwatar da yarjejeniyar bisa manyan tsare-tsare tsakanin Iran da China A daidai lokacin da shugaban kasar Iran ya kai ziyarar aiki zuwa kasar China, asusun kula da shafukan sada zumunta na ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya wallafa wani bangare na jawabinsa cikin harshen chinanci kan muhimmancin dangantakar Iran da China. Kididdigar ofishin kula da tsare-tsare da wallafa ayyukan jagoran juyin juya halin Musulunci ya wallafa bayanansa kan kasar Iran da kuma damar da kasar China ke da ita ta taka rawa a fagen duniya da kuma wajibcin aiwatar da yarjejeniyar tsare-tsare tsakanin kasashen biyu, wanda ya zo daidai da ziyarar...

Pezeshkian: Taron Kolin Shanghai Wata Muhimmiyar Dama Ce Ta Bunkasa Alakar Bangarori Da Dama Na Yankin
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Taron koli na Shanghai wata muhimmiyar dama ce ta bunkasa huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi la’akari da karfafa dangantaka da kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) daya daga cikin manufofin ziyararsa a kasar China da halartar wannan taro. Ya ce, taron kolin na Shanghai wata dama ce mai matukar muhimmanci da kuma dacewa don inganta huldar bangarori da dama da mu’amalar shiyya-shiyya da sauran kasashe. Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya bayar da safiyar Lahadi a filin jirgin sama na Mehrabad na Tehran kafin ya tashi zuwa kasar China don halartar taron kolin Shanghai: Kasashe mambobin kungiyar Shanghai sun kai kimanin...
Mataimakin babban kwamandan “IRGC” ya bayyana cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna yakar Iran Mataimakin babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Fadavi ya tabbatar da cewa: Makiya sun kasa cimma wata manufa tasu a tsawon kwanaki 12 da suka yi suna kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Iran. Duk da tsare-tsare masu yawa da kuma sanar da manufofinsu a baya, makiya sun kasa cimma wata manufa da suka ayyana a cikin yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan Iran, lamarin da ya tilasta musu amincewa da shan kashi ta hanyar amincewa da tsagaita bude wuta cikin hanzari. Fadavi ya kara da...
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada ci gaba da gwagwarmaya soji kan makiya ‘yan mamayar Isra’ila Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Tafarkin al’ummar Yemen na goyon bayan al’ummar Falastinu yana ci gaba kuma tabbatacce kuma yana kara ruruwa. A cikin jawabinsa Sayyed al-Houthi ya ce: ‘Yan kasar Yemen suna fuskantar makiya a dukkan fagage: ta fuskar siyasa, soja, tattalin arziki da kuma ta kafofin watsa labarai, ba za su yi rauni ba sakamakon wuce gona da iri da ake yi kan su. Ya kara da cewa al’ummar kasar Yemen suna yin jawabi da ya hau kansu wajen taimakawa wa al’ummar Falastinu, yana mai bayyana cewa; Suna tare da...

Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya
Kenya ta tono gawarwakin mutane 32 a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin ransu kan mace-macen ‘yan darikar addini masu tsattsauran ra’ayi Hukumomin kasar Kenya sun tono gawarwaki 32 a makon da ya gabata a kudu maso gabashin kasar, wani sabon bala’i da ya sake haifar da sukar gwamnatin kasar, wadda a baya ta yi alkawarin murkushe kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi bayan mutuwar daruruwan mabiya kungiyar asiri ta “Apocalypse” shekaru biyu da suka gabata. Gwamnatin Kenya da mazauna yankin sun danganta gawarwakin da aka gano a kauyen Kwa Binzaro da wata kungiyar kiristoci da ake zargi da hannu wajen kashe mutane fiye da 400 a dajin Chakahola da ke kusa a shekarar 2023. Babban likitan gwamnati a...
A nata bangaren, darektar kula da yankin Asiya da Fasifik da Gabas ta Tsakiya a ma’aikatar kula da hadin kan Afirka da harkokin wajen kasar Senegal Cathy Diagne Thioye, ta bayyana dandalin FOCAC a matsayin abin koyi a bangaren hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Ta yi kira ga bangarorin biyu da su ci gaba da yin aiki tare don aiwatar da muhimman ayyukan da suka sa a gaba a karkashin tsarin dandalin. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yu ya ce, kasar Sin ta tafka asarar rayukan sojoji da fararen hula sama da miliyan 35 da kuma asarar tattalin arzikin da ya zarce dalar Amurka biliyan 600 a lokacin yakin duniya na biyu. Ya yi nuni da cewa, tsayin dakan da kasar Sin ta yi ya yi mummunar wargaza mulkin danniya, tare da ba da gudummawa mai tarihi ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.” (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar. Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu Shugaban hukumar, Dokta Michael Odey, ne ya bayyana sakamakon a cibiyar hukumar da ke kan titin Aba Fatakwal, da yammacin ranar Lahadi. Ƙarin bayani na tafe…