2025-09-17@23:30:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1678

«Hausa da Hausawa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce Iran ba ta fargabar shiga sabuwar tattaunawa don warware duk wasu batutuwan da ba su dace ba, amma ba ta fargabar fuskantar wani sabon yakin da makiya za su iya sanyawa kasar. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a ranar Laraba bayan da ya raka shugaba Pezeshkian a ziyarar da ya kai kasar Sin. “Ba mu da tsoron tattaunawa, kamar yadda ba mu da tsoron yaki,” in ji shi. Wannan furuci ya zo ne a daidai lokacin da ake zargin Amurka da sha’awar shiga sabuwar tattaunawa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Tehran ba ta yi watsi da yiwuwar shiga sabon tsarin diflomasiyya...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da jan APC cikin harkokin siyasa kafin lokacin zaɓen 2027. Sai dai ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba. NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta Yayin da yake ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a Abuja, Tinubu ya yaba da ƙoƙrinsu wajen yaƙi da rashin tsaro tare da alƙawarin yin aiki da su kan batun ’yan sandan jihohi da kuma ayyukan gina hanyoyi. “A siyasa, ’yan adawa suna ƙoƙarin janyo mu mu fara kamfen da wuri. Amma duk da haka, ba zan bari a karkatar da hankalina ba. Na mayar da hankali...
    Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, dan Majalisar Wakilan Najeriya ya ce jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a shirye yake ya tattauna da jam’iyyar APC kan batun komawa cikinta. Dan majalisar, wanda makusancin Kwankwason ne dai a ’yan makonnin da suka gabata sau biyu yana ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja a kan batun Kwankwason. NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta Kofa ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a shirinsu mai suna Politics Today ranar Laraba. Sai dai Kofa wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar ya ce ya ce wasu daga cikin ’yan jam’iyyar...
    Gwamnatin Nijeriya ta bayyana goyon bayanta kan shirin mayar da rubuta Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da komfuta wato CBT daga shekarar 2026. Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi. An kama wata uwa kan binne jaririyarta a Kebbi Hatsarin kwale-kwale ya yi ajalin mutum 29 a Neja Da yake jawabi a gaban Majalisar Dokoki da manyan masu ruwa da tsaki a wani taron wayar da kai a Abuja, Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya ce jarabawa ta tsarin CBT da za a dinga yi a duk faɗin ƙasar, zai ƙarfafa tsarin ilimin ƙasar. Alausa ya ce Gwamnatin Tarayya tana...
    Firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko ya bayyana a wata hira da ya yi da wakilin rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a kwanan baya cewa, yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye bayar da labarun abubuwan da suka faru da su ya yi matukar burge shi. Sonko ya ce, duk kasar da ba ta iya tuna abubuwan da suka faru da ita a tarihi za ta yi matukar wahala ta dauki darasi daga abin da ya gabata, kuma tana iya saurin maimaita kura-kurai da kuma shan wuyar tashin hankalin da aka shiga a tarihi. Abin da ya yi matukar ba shi mamaki shi ne yadda jama’ar kasar Sin suke mutunta tarihi da kiyaye labarun abubuwan...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Bakhae ya yabawa dan majalisar dokokin kasar Irish Michael McNamara dangane da aibata kasashen turai yadda suka dulmuya kansu a cikin kissan kiyanshin da HKI take aikatawa a Gaza, da kuma yadda suka yi watsi da nauyin da ya rataya a kansu don tabbatar da zaman lafiya da adalci a duniya, amma suka ki sauke shi. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa Bakhae yana fadar haka a a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X, inda ya nakalto Michael McNamana ya ke yin tar da HKI kan kissan kiayshin da yake aikatawa a gazam da kuma rushe-rushen da kuma korar Falasdinawa da take...
    Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya sauke Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana...
    Ali Larijani, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, hanyar yin shawarwari da Amurka tana nan a bude, duk kuwa da takun sakar diflomasiyya da ake yi. A cikin wani sakon da ya wallafa a kan X, Larijani ya jaddada cewa “hanyar tattaunawa da Amurka ba a rufe ta ba,” yana mai jaddada cewa Iran “tana bin shawarwari ne na hankali.” Babban jami’in na Iran ya  nanata cewa Washington na gabatar da bukatu da ke kawo cikas ga tsarin shawarwarin tun daga farko. Ya kara da cewa, Amurka ta gabatar da batutuwan da ba za a iya cimma matsaya a kansu ba, kamar rage  karfin makamai masu linzami na Iran, inda ya ce wannan da ma wasu...
    Hukumar kwallon kafa ta Masar ta yi watsi da shawarar buga wasan sada zumunci da Zambia saboda masu horar da ‘yan wasan Zambia sun hada da ‘yan Isra’ila, kamar yadda kafafen yada labaran Masar suka rawaito a wannan Laraba. Wannan rashin amincewar ba a kai ga kai ga babban kocinta Avram Grant ba, wanda a baya ya taba horar da Ghana, ko mataimakinsa Eyal Lachman, sai dai a fagen siyasar da suke wakilta. Rahotanni sun bayyana cewa, an shirya wasan ne domin hutun kasa da kasa na watan Nuwamba, wanda zai gudana bayan kammala wasannin neman cancantar shiga gasar cin kofin  Afirka, kuma wasan share fage ne gabanin gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a Morocco daga...
      Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.   A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu.   A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma.   Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yammacin Turai sun fara amfani da takunkumi kan kasar Iran bisa umarnin  ‘yan sahayoniyya da Amurka Dangane da matakin da kungiyar gungun Turai ta dauka na son sake dawo da takunkumin da ya shude kan kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Kasashe uku na Turai ne suka fara aiwatar da shirin sanya takunkumi bisa umarnin ‘yan sahayoniyya da Amurka. Baqa’ ya fara taron manema labarai na mako-mako da jajantawa al’ummar Yemen da Falastinawa, yana mai cewa: “A yayin da ake gudanar da juyayin shahadar fira ministan kasar Yemen da kuma wasu ministocin kasar a matsayin wani bangare na wuce gona da iri na sojojin ‘yan...
    Majalisar shawarar Musulunci ta gudanar da zama na musamman don tattauna hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen takaddamar neman sake dawo da tsohon takunkumi kan kasar Iran Kakakin fadar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya sanar da matakin da babu makawa Iran za ta dauka kan domin kalubalantar matsayin gungun tawagar Turai Troika, yana mai jaddada cewa: Dukkanin jam’iyyun siyasa a majalisar dokokin kasar sun amince cewa tilas ne martanin Iran ya kasance mai azanci da mai da martani, lamarin da zai wurga makiya cikin nadama. Abbas Goudarzi kakakin fadar shugaban majalisar shawarar Musulunci ta Iran ya yi ishara da zama na musamman da aka yi a yau Talata a yayin wani taron manema labarai, inda ya...
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta ne domin nuna gamsuwa da irin ci gaban da Gwamna Idris ya kawo wa talakawa. Cibiyar Ayyukan Daular Usmaniyya za ta karrama Sarkin Zazzau Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da sabon manhajin karatun firamare da sakandire “Mun tuntubi mutane da yawa kafin a zaɓe shi, kuma kowa ya tabbatar cewa shi ya cancanta.” A nasa jawabin, Sarkin Zabarmawa na Jihar Kebbi, wanda kuma shi ne tsohon...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya tura a shafinsa na X a ranar Litinin. Ya kuma kara da cewa, ba yadda wadannan yara zasu je makaranta saboda yakin, babu makarantun da zasu shiga don HKI ta rusa mafi yawan makarantu a gaza, sannan ta kashe da dama daga cikin malaman makarantun a yankin. Lazzarini ya yake nanata bukatar a tsagaita budewa juna wuta saboda yara a gaza su sami damar zuwa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba, yana mai jaddada cewa: Iran na daukar muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian za...
    ’Yan gudun hijira daga sama da kauyukka 10 a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun ’yan bindiga a yankinsu. Mata da mazan sun buƙaci daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Neja. A yayin zanga-zangar a ranar Lahadi, wani daga ƙauyen Rinaye ya shaida wa Aminiya cewa, “Rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalinta da jami’an tsaro gare mu a ɗauki matakin korar mana ’yan bindigar su bar yankinmu. “Yau (Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yadda Gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, da magoya bayansa suka kaurace wa zaben kananan hukumomin jihar, da yadda APC ta lashe kujeru 20 a cikin 23 sun haifar da muhawara a tsakanin ’yan Najeriya.   Shin wannan sakamako alama ce ta yarjejeniyar sulhu da aka cimma a tsakanin Gwamna Fubara da Minsitan Abuja Nyesom Wike a Fadar SHugaban Kasa? NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Amsar wannan tambaya shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci za iyi yunkurin bicikowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya  bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa. A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan  Lahadin  cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na fadada Shirin da ake kira da Isra’ila Babba a cikin yankin kasashen Larabawa. Kasashen mambobi sun yi gargadin illar da wadannan buri ke ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya kara da cewa mambobin kawancen sun tsaya tsayin daka tare da al’ummar Palasdinu dangane da harin wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa a zirin Gaza, musamman yin Allah wadai da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi wa  wasu daga cikin manyan jami’an kasar Yemen, tare da yin kira ga al’ummar duniya da su tinkari irin wadannan munanan ayyuka  na rashin bin doka da oda. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi tir da wadannan ayyuka na  ta’addanci, tare da jaddada bukatar  daukar matakin gaggawa daga kasashen duniya don dakile aniyar yahudawan sahyuniya ta kawo hargiti a gabas ta tsakiya, wanda kai tsaye yake shafar tsaro na kasashen duniya. Ta bayyana wannan munanan aiki da cewa, ba wai kawai laifukan yaki da laifin cin zarafin bil’adama ba ne, har ma  yana a matsayin ramuwar gayya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren Majalisar kolin tsaron kasar Iran ya jaddada cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin Babban Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Iran na adawa da duk wani sauyi na siyasa a yankin da kuma cutar da alaka tsakanin Iran da Armeniya. Ali Larijani, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran, ya gana tare da tattaunawa da Armen Grigoryan, sakataren kwamitin koli na tsaron kasar Armeniya a safiyar yau. A cikin wannan taro, babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana gamsuwar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take da shi kan matakin tattalin arziki, siyasa, tsaro da kasar Armeniya, tare da jaddada hadin gwiwa da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a tarurruka da kuma kafafen yana labarai na gwamnati. Wannan dai ya sami suka daga yan jarida wadanda suke ganin kundin tsarin mulkin kasar na kowa da kowa don haka hana kafafen yada labarai masu zaman kansu gudanar da tattaunawar bai dace ba. Hakama hana jamiyyun adawa, wadanda basa dasawa da gwamnati shima bai kamata ba. Sékou Jamal Pendessa na kungiyar yan jaridu a kasar ya...
    Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya Juma’a cewa, sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio ya yanke shawarar  soke takardar izinin shiga kasar ga wasu mambobin kungiyar ‘yantar da ‘yancin Falasdinu (PLO) da hukumar Falasdinu (PA), ciki har da shugaban PA Mahmoud Abbas, gabanin taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a birnin New York na watan Satumba mai zuwa. Wadannan matakai na nufin cewa da alama Abbas ba zai iya zuwa New York  don gabatar da jawabinsa na shekara kamar yadda ya saba yi ba. Wannan mataki dai na cikin jerin takunkuman da Amurka ta kakabawa jami’an Falasdinawa a watan Yulin da ya gabata, a daidai lokacin da wasu kasashen yammacin duniya ke neman amincewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Francesca Albanese, Jami’a mai tattara bayanai kan al-amuran Falasdinawa a MDD ta yi tir da gwamnatin kasar Jamus dangane da yadda jami’an tsaron kasar suke dirar mikiya kan masu goyon bayan Falasdinawa a birnin Berline. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Albanese tana fadar haka a yau Jumm’a ta kumamkara da cewa: Ina kiran mutanen Jamus kan cewa ku ne kuka samar da ikidar Nazi, a yayinda mu a kasar Italia da Spaine muka samar da akidar Fasim a nahiyar turai a baya, wana ya kai kasashen turai ga lalacewa.. Jami’ar ta bayyana haka ne bayan dirar mikiyan da jami’an tsaro na Jamus suka yi kan masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa wadanda kuma suke bukatar HKI ta...
    Bayan sanarwar da E3 (Faransa, Jamus, da Burtaniya) suka yi na haifar da hanyar da za ta kai ga dawo da takunkumin da aka kakaba wa Tehran kan shirinta ma nukiliya, Majalisar Dokokin Iran ta tsara tare da gabatar da wani kudirin doka na gaggawa da ke ba da shawarar ficewa gaba daya daga yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Hossein-Ali Haji-Deligani, Mataimakin Shugaban Kwamitin Mataki na 90 na Majalisar Dokokin Iran, ya tabbatar da cewa za a shigar da kudirin zuwa tsarin majalisar a rana mai zuwa sannan a sake duba shi a wani budadden zama. “Kamar yadda muka fada a baya, wadannan kasashe sun riga sun fara aiwatar da takunkumin da aka kakaba mana. Babu wani sabon abu...
    Daraktan Tsara Tafiye-tafiye na Gwamnan Kano, Abdullahi Ibrahim Rogo, ya maka jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar a gaban kotu, bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar kiransa da ɓarawo. ‎A kwanakin baya ne dai jaridar ta zargi Daraktan da karkatar da kudade har sama da Naira biliyan shida da rabi zuwa asusunshi, kodayake daga bisani Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya wanke shi daga zargi, inda ya ce ba satar kudaden aka yi ba, na aiki ne. Magauta sun sa NNPCL a gaba – Ojulari Babu ƙawancen da NNPP ta ƙulla da wata jam’iyyar — Kwankwaso To sai dai jaridar ta sake yin labari mai taken “Gwamnan Kano ya kare hadiminsa barawo, ya ce gwamnatin Ganduje ma ta...
    Harshen Hausa shine kan gaba a yawan masu magana a Afrika ta Yamma ta yadda yake da karbuwa a Nijeriya, Nijar, Ghana, Kamaru, Benin, Gabon, Togo, Afrika ta Tsakiya, Sudan da Saudiyya da sauran su. Hasalima kowace nahiya ta duniya akwai jami’ar da ake koyar da harshen Hausa da Hausanci. Bunkasar Harshen Hausa ya sa harshen ke barazanar batar da kananam harsuna wadanda tuni wasu da dama a yau suka bace ba amo ba labarin su a bisa ga yadda yake mamaye harsuna a mabambantan kasashe. Sai dai duk da kima da martabar da Harshen Hausa yake da shi da yadda daruruwan miliyoyin al’umma ke magana da Harshen har yau Jamhuriyar Nijar kadai ce kasar da ke amfani da Hausa...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta mayar da martani ga Tawagar Turai na kokarin dawo da takunkumi kan kasarta Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa a matsayin martani ga sanarwar da Tawagar Tura ta yi wa kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da baya kan ka’ida dangane da kuduri mai lamba 2231. Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kakkausan harshe tare da yin Allah wadai da shelanta batu da baya kan doka da tawagar Turai Faransa da Jamus da Birtaniya suka yi ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da kuduri mai lamba 2231 na shekara ta 2015. Wannan matakin bai dace ba, wanda ya ci karo da Tsarin Raba Rikici (DRM) na Haɗin gwiwar...
    A yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu akwai shugabanni da tsoffin ‘yan siyasa da manyan jami’ai, da jakadun dake kasar Sin da sauransu kusan 50 daga kasashe 30 na Turai da suka tabbatar da za su halarci bikin da za a yi albarkacin cika shekaru 80 da samun nasara a yaki da kutsen Japan da yaki da mulkin danniya a duniya. Wannan ya nuna niyyarsu ta hada hannu wajen tunawa da tarihi da kiyaye zaman lafiya da adalci.   Guo ya jaddada cewa, kasar Sin ta shirya bikin ne da nufin tunawa da tarihi da magabata, da kiyaye zaman lafiya da ma tabbatar da makoma mai kyau ga bil...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran jam’iyyar NNPP a Nijeriya, Sanata Rabi’u Kwankwanso, ya ce suna jin daɗin jam’iyyarsu, kuma a halin da ake ciki babu wani ƙawance da suka ƙulla da wata jam’iyyar. Yayin da yake jawabi a wajen taron majalisar ƙoli na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, Sanata Kwankwaso ya ce ba gaggawa suke yi ba. Sanusi Mikail Sami ya zama sabon Sarkin Zuru Ambaliya: Manoma sun yi asarar miliyoyin Naira a Taraba Tsohon gwamnan na Kano ya ce kawo yanzu babu wata jam’iyya da suke tattaunawa da ita domin ƙulla ƙawance, sai dai ya ce hakan ba yana nufin ba za su tattauna da wata ba. “’Yan jam’iyyarmu ba gaggawa suke yi ba, komai muna yinsa a hankali,” in ji shi....
    An kashe mutane 24 tare da raunata wasu 55 a harin da Dakarun  Kai Daukin Gaggawa suka kai kan birnin El Fasher Kungiyar likitocin kasar Sudan ta sanar a jiya Alhamis cewa: Fararen hula 24 ne suka mutu sannan wasu 55 da suka hada da mata 5 suka samu raunuka sakamakon luguden wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kai ranar Laraba a garin El Fasher dake arewacin Darfur. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarto cewa, an kai harin ne a tsakiyar kasuwa da unguwar Awlad al-Reef, inda ya bayyana lamarin a matsayin wani kisan gilla da aka yi da gangan kan fararen hula da ba su dauke da makamai. A cikin sanarwar da ta fitar,...
    Tawagar Sudan karkashin jagorancin babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa (NISS) Manjo Janar Ahmed Mufadal ta isa Mogadishu babban birnin kasar Somalia a wata ziyarar aiki da ta kai kasar, inda ta gana da shugaban kasar  Hassan Sheikh Mohamud a fadar shugaban kasa dake Mogadishu. Jagoran tawagar ta Sudan Mufadal Sheikh Mohamud ya aike da sako daga shugaban kwamitin rikon kwarya na kasar Sudan, Laftanar Janar Abdel Fattah Al-Burhan. Sakon ya hada da jaddada aniyar Khartoum na karfafa hadin gwiwa da Somaliya, musamman a fannin tsaro da leken asiri. Taron ya samu halartar babban daraktan hukumar leken asiri ta kasar Somalia  (NISS), Mahad Mohamed Salad, wanda ya tattauna da Mufadal hanyoyin inganta  hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen da yankin...
    Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a kan babban titin da ke shiga garin tare da rike hotunan shahidan Hizbullah, da kuma wasu hotuna wadanda suke kiran jakadan da suna “Dabba” ya sa Barrack ya fasa ziyarar. Tom Barrack yana daga cikin jami’an gwamnatin Amurka suke son tilastawa shuwagabannin gwamnatin kasar Lebanon, sun kwance damar kungiyar Hizbullah na kasar da karfi. Hizbullah wacce ta dauki shekaru tana hana HKI shiga kasar kasar....
    Masu zanga zanga za wasu yankunan kudancin kasar Lebanon sun tilastawa jakada na musamman na gwamnatin Amurka a kasar Siriya da Lebanon Tom Barrack ya fasa ziyarar da yake son kaiwa wasu yankuna a kudancin kasar Lebanon. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya bayyana cewa mutane a garin Sur sun yi gangami a kan babban titin da ke shiga garin tare da rike hotunan shahidan Hizbullah, da kuma wasu hotuna wadanda suke kiran jakadan da suna “Dabba” ya sa Barrack ya fasa ziyarar. Tom Barrack yana daga cikin jami’an gwamnatin Amurka suke son tilastawa shuwagabannin gwamnatin kasar Lebanon, sun kwance damar kungiyar Hizbullah na kasar da karfi. Hizbullah wacce ta dauki shekaru tana hana HKI shiga kasar kasar....
    Kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da sojojin HKI tun watan Octoban shekara ta 2023 ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a halin yanzu tana rike da gawakin falasdinawa 726 wasu gawakin sun yi fiye da shekaru 10 a hannusu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa su shiga cikin labarin don karban gawakin shahidai Falasdinawa daga wadannan yahudawa. Kungiyar ta kara da cewa rike gawakin falasdinawa ya karu tun bayan fara yakin tufanul Aksa wato a cikin watan oct. Shekara ta 2023. Kungiyar ta bayyana cewa yawan falasdinawan da HKI ta kashe tun kimani shekaru 2 da suka gabata ya fi yawan...
    Hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD (OHCHR) ta bayyana cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa 982 a yankin yamma da kogin Jordan tun cikin watan Octb. Shekara ta 2023. Wannan banda wasu 42,000 da suka tilastawa barin gidajensu daga yankin. Banda haka sun rusa gidajen shaguna da sauran abinda Falasdinawa suka mallaka. Banda haka yahudawan da suke yankin suna kai farmaki kan Falasdinawa a yankin, inda suke kashe wasu Har’ila yau kungiyar red cross ta bayyana cewa ta sha jinyar wasu Falasdinawa a yankin Yamma da kogin Jordan wadanda suka sha hayaki mai guba wanda sojojin HKI suke jefa masu a yankin, Labaran sun kara da cewa a yau laraba sojojin yahudawan sun kai hare haren kan Falasdinawa a Nablus...
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba za a cimma abin da Amurka ke so ba ta hanyar kai harin soji kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, kuma a duk wata tattaunawa dole ne Amurka ta kare sharuddan da Iran ta gindaya mata domin samun ci gaba mai daure wa. Araqchi wanda ya gana da Asharq Al-Awsat bayan halartar wani zama na musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi don...
    Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin cewa dawowar Jonathan ko Obi na iya sauya tsarin PDP wajen fafatawa da jam’iyyar mai mulki ta APC. Jonathan na da magoya baya masu tsayi da suka daɗe a PDP, yayin da Obi kuma ya fi jan hankalin matasa. Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko za su amince da wannan kira, da kuma yadda PDP za ta shawo kan matsalolin cikin gida kafin zaɓen fidda gwani. Zuwa yanzu, babu wanda ya fito fili daga cikinsu ya tabbatar da komawarsa PDP. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Hukumar ta SEMA ta dauki nauyin kwashe fasinjojin da suka makale, da bayar da agajin gaggawa, da kuma tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa sun samu kulawar gaggawa a inda ya dace.   “Gwamnan ya ba da umarnin a baiwa fasinjoji duk wani tallafi da ya dace don rage tasirin wannan mummunan lamari, duk wanda ya samu rauni za a kula da shi cikin gaggawa, yayin da ake ba da tallafin gaggawa na psycho-socio da tallafin likita ga wadanda abin ya shafa,” in ji Maiyaki.   Sanarwar ta ci gaba da cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin jirgin, inda ta kara da cewa gwamnatin jihar na sanya ido sosai kan lamarin tare...
    shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita ce mafi kyamata a tsakanin al’ummar duniya. Shafin yanar gizo na KHAMENEI.IR na yaren yahudanci ya wallafa wani kaso na jawabin Jagoran a jiya litinin a wajen taron juyayin shahadar Imam Ali dan Musa al-Rida Jagoran shiriya na Iyalan gidan Manzon Allah {s.aw}. Sanarwar ta kara da cewa: “Makiyar al’ummar Iran a yau, ita ce gwamnatin ‘yan sahayoniyya, wacce duniya ta fi kyama a duniya....
    Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen Hausa da tarihinsa. A Nijeriya, cibiyoyi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sukan shirya taruka da laccoci. A jami’o’i irin su Jami’ar Bayero ta Kano da sauransu, masana da ɗalibai su kan tattauna kan ci gaban Hausa a fannin kimiyya da fasaha, da kuma ƙirƙiro sababbin kalmomi da ke dacewa da zamani. Haka kuma, jama’a na amfani da wannan rana a kafafen sada zumunta domin wallafa...
    Gwamnatin Kano ta musanta rahotannin da ke zarginta da karkatar da Naira biliyan 6.5 daga baitul-malin jihar, tana mai cewa labarin “ƙarya ne da ‘yan adawa suka kitsa domin ɓata mata suna.” Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin. PDP ta miƙa wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027 PDP ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa Sanarwar ta ce labarin da aka wallafa a wani shafin yanar gizo a ranar 22 ga watan Agusta, wani yunƙuri ne na ɓata sunan gwamnatin da kuma lalata martabar jami’anta kafin Zaɓen 2027. Sanarwar ta ce taƙaddamar wadda a yanzu haka tana gaban kotu ta...
    Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a. Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba. Rushe Kasuwar Alaba Rabo: Mun yi asarar fiye da N20bn — ’Yan Arewa Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya isa kasar Saudiyya domin halartar wani babban taro na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi. A yayin da yake jagorantar tawagar diflomasiyya ta kasar Iran, Araghchi ya isa birnin Jeddah na kasar Saudiyya a jiya Lahadi domin halartar taron kungiyar OIC da za a bude a wannan  Litinin bisa bukatar da  Iran da kuma wasu kasashe gabatar na yin hakan. A yayin taron na kwanaki biyu, mahalarta taron za su tattauna kan matsalolin  jin kai a zirin Gaza, da yiwuwar kawo karshen kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palastinu, da kuma gurfanar da ‘yan sahayoniya masu laifi a gaban kotu. Kungiyar ta OIC ta ce taron zai mayar...
    Wasu majiyoyi na kusa da Putin dai sun bayyana cewar, ya na fatan ganawar da za su yi ta gaba da Zelensky da Trump zai jagoranta ta kasance a Mo scow.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Aƙalla gidaje 70 ne suka ruguje wasu da dama suka lalace sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya a Ƙaramar Hukumar Malam Madori ta Jihar Jigawa. Yankunan da ibtila’in ya shafa sun haɗa da Tonikutara, Gandun Sarki, Gandun Bundugoma da rukunin gidajen Shagari Quarters, bayan ruwan sama da aka kwashe sa’o’i da dama a ranar ya mamaye kwalbatoci da magudanan ruwa a yankin. Dan-Ummah Abba, wani magidanci da lamarin ya shafa a Gandun Sarki ya bayyana cewa gidansa da yake zaune a ciki sama da shekara 30 ya rushe a sakamakon lamarin. Daga nan ya roƙi Gwamnatin Jihar Jigawa da ta kawo musu ɗaukin gaggawa. NAJERIYA A YAU: Halin Da Muke Ciki Bayan Rasa ‘Yan Uwanmu A...
    Kungiyar Hamas da sauran bangarorin Falesdinu na gwagwarmaya sun amince da kudurin tsagaita bude wuta da masu shiga tsakani na Masar da Qatar suka gabatar, kamar yadda wani babban jami’in Falasdinu ya shaidawa Al Mayadeen. Bayan haka, Hamas a cikin wata sanarwa ta tabbatar da cewa ta amince da kudurin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, wanda Masar da Qatar suka mika a jiya. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar Hamas da bangaren Falasdinu sun sanar da masu shiga tsakani kan  amincewa da shawarar da Masar da Qatar suka mika a jiya. Babban jami’in ya shaidawa Al Mayadeen cewa, a karkashin shawarar sojojin Isra’ila za su janye kilomita daya daga yankunan arewaci da gabashin Gaza, sanan kuma garuruwan al-Shujaiyya da...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon sabbin baburan hawa ga shugabannin jam’iyyar APC na mazabun kananan hukumomi 12 na shiyyar Jigawa ta Arewa maso yamma wadda Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya bayar da kyauta. A jawabin sa, Gwamna Umar Namadi ya yaba da kokarin Sanatan tare da shawartar shugabannin da suka sami ababan hawan da su yi amfani da su yadda ya kamata. A jawabin sa, Sanata Babangida Hussaini Kazaure ya ce ya bada baburan ne domin saukakawa shugabannin jam’iyya gudanar da ayyukan su cikin sauki. Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa nasarorin da ya samu a shekaru biyu da ya yi akan karagar mulki.   Usman Mohammed Zaria
    Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana gudanar da ayyukan gyara da ginawa da kuma inganta hanyoyin mota domin cimma kudirin ta na bunkasa bangaren aikin noma. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da aikin sanya kwalta akan hanyar Dandi da Farin Daba zuwa Gada a karamar hukumar Kazaure. Ya ce gwamnatin jihar ta bada kwangilar aikin ne akan kudi sama da Naira miliyan dubu 8 da miliyan 200 tare da wa’adin kammala aiki a watanni 18. Kazalika, Malam Umar Namadi ya kuma bude aikin gina hanyar Farin Daba, Galo Babba zuwa Galo Karama da aka ba da kwangilar su kan naira miliyan dubu shida da miliyan 300. Ya kara da cewar, aikin zai saukaka wa manoma kai...
    Jaridar Wall Street Journal ta bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da neman kasashen da za su karbi ‘yan gudun hijiran Falasdinawan Gaza! Jaridar Wall Street Journal ta buga wani rahoto da ke cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da gudanar da tattaunawar da ta bayyana na zaman natsuwa domin tura ‘yan gudun haijiran Falasdinawa daga Gaza. Kasashen da suka hada da Libiya, Siriya da Sudan ta Kudu. Rahoton wanda Samar Sa’ed, Robbie Gramer, da Omar Abdel Baqi suka shirya, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suke yunkurin tura dubban daruruwan Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa gare su, matakin da suka gabatar cewa akwai hanyoyin jin kai, amma gwamnatocin yammacin Turai da kasashen...
      Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna.   Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare na Gwamnatin Tarayya kai tsaye.   Yayin taron Annual Speech and Prize-Giving Ceremony na makarantar, Shugaban makarantar Hauwa’u Memorial, Nasir Musa, wanda ya wakilci AMA Foundation, ya bayyana cewa yanzu haka ana daukar nauyin marayu 120 a makarantar firamare, wasu 120 a Makarantar Sakandare na FGC Kaduna, sannan dalibai 16 sun samu gurbin shiga Jami’ar Jihar Kaduna (KASU). Ya jinjina wa wanda ya assasa...
    Gwamnatin shugaban Trump ta bada umurnin a dakatar da bawa Falasdinawa daga Gaza visar shiga Amurka, bayan da wata kungiyar wacce take goyon bayan HKI ta gabatar da korafi kan cewa Falasdinawa da suka ji rauni da dama suna zuwa Amurka don jinyan raunukan da suka sami a asbitocin Amurka. Jaridar ‘the nation’ ta kasar Amurka ta nakalto ma’aikatar harkokin wajen Amurka na fadar haka a shafinta na X, ta kuma kara da cewa a halin yanzu an dakatar da bawa dukkan falasdinawa daga Gaza visar shiga Amurka. Sannan bayan an kammala bincike mai yuwa a bawa wasu yan kasan Visar, bisa aikin jinkai da kuma don jinya kawai. Wasu kungiyoyin kare hakkin na Falasdinawa a Gaza, sun yi tir...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya aika da jajensa ga mutane da Firai ministan kasar Pakisatan kan ambaliyar ruwa da ta faru a kasar bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 300 da kuma bacewar wasu. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban y ace kasar Iran a shirye take ta bada agaji ta kuma aike da yan kwana-kwana don taimakawa kasar fita daga wannan halin da take ciki. Shugaban yayi fatan warkewa da sauri ga wadanda suka jikata ko suka ji ciwo a sanadiyyar wannan ambalin ruwa a kasar ta Pakisatn. Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya jawo ambaliyar ruwa mai yuwa, ya kuma rufe gidaje,...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa. Zaɓen cike gurbin na Babura-Garki ya fara ne da tsauraran matakan tsaro a fadin mazabar. Jami’an tsaro suka kasance a rumfunan zaɓe da wuraren da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya. A daidai ƙarfe 8:30 na safe, jami’an Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) sun isa rumfar Garki-Kofar Fada (003) inda suka fara shirye-shiryen zaɓe. Mr Ibrahim Shehu, jami’in zaɓe a rumfar, ya shaida wa...
    Kasashe 31 na duniya sun yi Allah wadai da kalaman fira ministan Isra’ila na shirin mamaye yankunan kasashe don kafa ‘Babbar kasar Isra’ila Kalaman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbare kasar Isra’ila” ta janyo suka daga Larabawa da Musulunci. Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi 31, tare da manyan sakatarorin kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da kuma kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha, sun yi Allah wadai da kalaman Netanyahu dangane da abin da ake kira “Babbar Isra’ila”, tare da la’akari da furucin a matsayin rashin mutunta dokokin kasa da kasa da kuma barazana kai tsaye ga tsaron kasashen Larabawa da...
    Mutane kimani 60 ne zasu gurfana a gaban kotu a kasar Burtaniya, saboda goyin bayan kungiyar mai goyon bayan Falasdinu, wata :frre Palastine’ wacce kuma gwamnatin ta bayyanata a matsayin kungiyar yar ta’adda. Labarin ya kara da cewa wannan shi ne zanga zangar da aka fi kama mutane tun lokacinda aka fara zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a shekara ta 2023. Masu goyon bayan Falasdinawa 3 wadanda aka kama a cikin watan Julin da ya gabata, an rika na gabatar da su a gaban kotu kuma kuma za’a tuhumesu karkashin doka da “Yan ta’adda na kasar.  Yansanda sun bayyana cewa kotu tana iya yanke hukuncin zaman gidan kaso har na tsawon watanni 6 a kan ko wanne daga cikinsu. A...
    Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana. Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli. “Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu...
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da ya jagoranci ‘yan kwamatin domin ziyarar aiki a sakatariyar karamar hukumar Gwiwa. Yace a lokacin irin wannan ziyarar, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi domin tabbatar da gudanar harkokin kananan hukumomi kamar yadda ya kamata, ta hanyar aiki da tanade-tanade da kuma ka’idojin kashe kudade. Alhaji Aminu Zakari ya kuma lura cewar Kwamatin yana kafa kananan kwamitoci domin ziyarar gani...
    “Mun amshe bukatun, sannan bayan hakan kwamitin yin nazari kan sake yi wa tsarin mulki garambawul wanda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Jibrin Barau yake jagoranta zai tattance tare da shirya rahoto ga majalisar. “Da zarar rahoton ya kammala, majalisar dattawa tare da hadin gwiwar majalisar wakilai za su gudanar da cikakken jin ra’ayin jama’a. Wannan zai ba da dama ga dukkan masu ruwa da tsaki da suka hada da masu goyon baya da masu adawa su gabatar da hujjojinsu. Bayan haka, majalisun guda biyu za su yanke shawara kan wadannan bukatun. “Batun kirkirar sabbin jihohi abu ne mai matukar muhimmanci wanda ke bukatar duba batutuwan al’umma, yankuna, da samun alkaluman tarihi. A wasu lokuta, ko a cikin jihohin da...
    Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa.   Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin domin jajantawa iyayensa da ‘yan uwansa .   “kwamishinan ya Kara da cewa ‘Mai girma gwamna Uba Sani Yaso yazo da kansa amma bisa wasu abubuwa da suka bijiro hakan ya sanya ya wakilto mu saboda haka gwamna ya kadu matuka da samun labarin rasuwar Abubakar”.   Maiyaki, yace domin ganin an dakile matsalar yawaitar tu’ammali da muyagun kwayoyi, gwamnatin jihar Kaduna ta Kafa wani...
    Daya daga cikin manyan nasarorin da Dakta Bello Matawalle ya samu shi ne kaimi da aka yi wurin yaki da ta’addanci, ta hanyar kyautata hadin gwiwa da Sojojin kasa, da Sojojin sama da sauran hukumomin tsaro. An yi rugu-rugu da matattaran ‘yan ta’adda a Arewa Maso Gabas, wanda hakan ya yi sanadiyar raguwar hare-hare. A Arewa Maso Yamma kuwa, gagarumar gudummawa da ma’aikatar tsaro a karkashinsa ta amfani da karfin soja ya yi mummunar illa ga matattarar ‘yan ta’adda wanda hakan ya kyautata fata da al’umma ke da shi cewa an kusan share musu hawaye.   2. Kula da walwalar sojoji da karfafa musu gwiwa Ganin cewa karfin Sojan Nijeriya ya dogara ne a rundunarta, Dakta Bello Matawalle ya inganta...
    Kamfanin jirgin sama na British Airways ya hana fasinjoji 58 hawa jirginsa da zai tashi daga Abuja zuwa Landan saboda matsala da ƙofar jirgin ta samu. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa saboda dalilan tsaro. Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda Daraktan Yaɗa Labarai da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya wallafa a shafinsa na X cewa matsala ce ta sa aka hana fasinjojin hawa jirgin. Ya ce an bai wa fasinjoji 30 wajen kwana a wani otel, yayin...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya ta yaba wa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa nada Alhaji Muhammad K. Dagaceri a matsayin shugaban ma’aikata na jiha. Shugaban  ƙungiyar na kasa, kuma mataimakin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa TUC, Kwamared Shehu Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya kai ziyara ga shugaban ma’aikata, Alhaji Muhammad Dagaceri, a ofishinsa. Ya tabbatar wa shugaban ma’aikatan da cikakken goyon baya da haɗin kan ƙungiyar wajen cimma manufofin da aka tsara a matsayinsa na shugaban ma’aikatan jiharta Jigawa. “Kungiyarna sa ran yin haɗin gwiwa da zai ƙara inganta aikin ma’aikata da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.” In ji shugaban ƙungiyar. A jawabinsa, Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana godiyarsa bisa wannan...
    Gwamna Malam Umar Namadi na jihar Jigawa ya bayyana harkar kiwon dabbobi a matsayin babbar harkar tattalin arziki ta biyu a jihar baya ga noma. Ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamishina na farko na ma’aikatar ci gaban kiwon dabbobi da aka kafa kwanan nan, Farfesa Salim Abdurrahman Lawal, a zauren majalisar zartarwa na gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, baya ga noma, kiwon dabbobi shi ne babban abin da mutanen jihar Jigawa suka sanya a gaba. Malam Umar Namadi ya kara da cewa kafa wannan ma’aikata na cikin shirin gwamnati na bude manyan damarmaki da ke cikin wannan bangare. “Mun dauki mataki na musamman domin ingantawa da bunkasa bangaren kiwon dabbobi. Mun yi hadin gwiwa da...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari ga daukacin al’ummar Falasdinu ne Babban sakataren kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi ya tabbatar da cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna kai hari kan dukkanin al’ummar Falastinu ne, yana mai jaddada cewa: Makiyan ‘yan sahayoniyya sun aikata kowane irin laifi da kowane nau’i na wuce gona da iri kan al’ummar Falastinu a zirin Gaza. A jawabin da ya gabatar kai tsaye kan sabbin ci gaban da ake samu a hare-haren wuce gona da iri kan zirin Gaza da kuma ci gaban yanki da na duniya, Sayyed al-Houthi ya yi nuni da cewa, yawan hare-haren da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai cikin...
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar ‘yan bindiga,” in ji shi. Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ɗauki matakaki a kan waɗanda suka aikata wannan kisan gilla, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wata ɓarna a Zamfara. Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sunusi Ahmad Rashad, wanda ya raka gwamnan, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin. “Wannan ziyara tana da...
    Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa. Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka...
    Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba. Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa...
    Miistan harkokin wajen kasar Masar ya sake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labarana Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar na cewa jami’am gwamnatin kasashen biyu da kuma Grossi sun tattauna al-amura da suka shafi sake komawa kan taburin tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya ne bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran. Badar Abdullatf ministan harkokin wajen kasar Masar yana kokarin sake maida dangantakar hukumar AIEA da kuma Iran bayan tayi tsami a watan yunin da ya gabata, inda Iran tana zargin Grossi da hada kai da Amurka...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya. A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce wannan ziyara za ta ba tawagarsa damar fahimtar dabarun noma da sarrafa shinkafa, samun horo a aikace, tare da koyo game da dukkan sassan harkar noman shinkafa. Ya bayyana cewa, wannan zai taimaka wa Liberia rage dogaro da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje. “A Liberia muna cin shinkafa safe, rana da dare. A shekarar 1979, an yi tarzomar shinkafa da ta kifar...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki. “Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar  reshen jihar,  cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa  ma da wajen ta.” In ji shi. “Na...
    An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.   Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta NUJ ta shirya domin fara taron makon manema labarai na shekara ta 2025, da kuma bikin cika shekara 45 daka guda a Ilorin jihar Kwara   Ya shawarce su da su bi ka’ida wajen gudanar da ayyukansu na yada labarai.   Imam Lukman ya bukaci masu aikin yada labarai da su kasance masu adalci da kyautatawa a tsakaninsu .   A nasa jawabin, Fasto...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya.   An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja inda aka kai shi Abuja domin ci gaba da bincike.   Gwamna Umar Bago ya bayyana matakin a matsayin nuni da irin jajircewar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Nijeriya.   Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim, ya ce, “Eh gaskiya ne, zan iya tabbatar da cewa hukumar...
    Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata. Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta. Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara....
    Wata majiyar Falasdinawa ta shaida wa AFP cewa “Masu shiga tsakani na aiki don samar da wata hanyar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta” wadda za ta sa a sako dukkan sauran fursunonin da ake tsare da su a Gaza “a rukuni guda.” Shawarar na iya hadawa da “tsagaita bude wuta na kwanaki 60, sannan kuma a yi shawarwarin tsagaita bude wuta na dogon lokaci, da kuma yarjejeniyar musayar dukkan fursunonin Isra’ila da suke da rai da wadanda suka mutu, a cikin rukuni guda,” a cewar majiyar. Tawagar kungiyar Hamas karkashin jagorancin Khalil al-Hayya ta isa kasar Masar domin halartar shawarwarin tsagaita wuta a zirin Gaza. Tun da farko dai kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto wasu majiyoyi suna cewa wasu...
    Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen yi wa masu adawa da ita barazana. Saƙon da ɗan takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2023 ya wallafa wannan Talatar a shafinsa na X, na zuwa ne bayan tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal da EFCCn ta yi. Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi A cewar Wazirin Adamawa, “dalilin da EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, shi ne saboda yana cikin jam’iyyar adawa ta haɗaka. “Wannan yana ƙara nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ci gaba da yaɗa manufofinta na musgunawa, tsoratarwa, da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron majalisar dinkin duniya. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta fitar ta bayyana cewa: Mataimakin fira ministan kasar ta Iraki, kuma ministan harkokin wajen kasar Fuad Hussein ya gana da Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran. Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, da aikin layin dogo da zai hada Shalamcheh...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da gargadi game da hawan keken masu kananan shekaru da rashin biyayya ga fitilun ababen hawa a cikin babban birnin Kano.     Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.   Gargadin na zuwa ne bayan an samu munanan hadurran kan tituna guda 16 a cikin watan Agustan 2025, wanda ya yi sanadin jikkata da asarar dukiyoyi.     Rundunar ta lura cewa hawan keken ƙananan yara yana haifar da babban haɗari ga mahaya da sauran masu amfani da hanyar.     An shawarci iyaye da masu kula...
    Ma’aikatar lafiya a Gaza ta sanar da isar shahidai 69 da wadanda suka jikkata su 362 zuwa asibitoci a cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata. Daga cikin shahidan akwai wadanda yunwa ce ta kashe su, da kuam wadanda suka yi shahada a wajen neman samun agajin abinci, ida Isra’ila take kai hari kansu abbu kakkautawa. A cikin rahotonta na kididdiga na yau da kullun, ma’aikatar ta gano mutuwar mutane biyar da suka hada da yaro daya sakamakon yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, wanda adadin wadanda suka yi shahada sakamakon yunwa ya kai 222, ciki har da yara 101. Ma’aikatar ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka mutu a harin ta’addancin Isra’ila ya karu zuwa shahidai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Samun matasan da ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’ummominsu abu ne da ba kasafai ake samu ba a wannan zamani. Amma duk da haka, wasu matasa sun sadaukar da rayuwarsu wajen bayar da gudunmawarsu wajen ci-gaban al’ummarsu. NAJERIYA A YAU: Yadda Damina Ke Shafar Masu Ƙananan Sana’o’i DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Shirin Najeriya  A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin gudunmawar da matasa ke bayarwa wajen ci-gaban al’ummarsu. Domin sauke shirin, latsa nan
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa. Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara. Wannan sabon...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce yaki da talauci muhimmin mataki ne na hanzarta ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Ya bayyana haka ne a lokacin shirin gwamnatin jihar mai taken “Gwamnati da Jama’a” wanda aka gudanar a karamar hukumar Ringim. Malam Umar Namadi ya jaddada muhimmancin horas da matasa sana’o’in hannu da samar da yanayin kasuwanci mai kyau domin cimma wadannan manufofi. Saboda haka, ya yi kira ga zababbun wakilai, masu rike da mukaman siyasa, shugabannin kasuwanci da sauran attajirai da su taimaka wa al’ummarsu domin kara bunkasa ci gaba da habaka tattalin arziki. A yayin taron, Kwamishinan jin kai da harkokin musamman na jihar, Auwal Danladi Sankara, ya raba naira miliyan 50...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya. Ta kuma zargi hukumar da kiran wasu shugabannin adawa kan shari’o’in da suka dogara da tsoffin zarge-zarge na siyasa. UEFA...
    Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) ta sanar da cafke wani mutum, Salisu Muhammad, mai shekaru 45, bisa zargin kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin da ke Karamar Hukumar Kiyawa a Jihar Jigawa. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Muhammed Badarudeen ya fitar a Dutse, babban birnin jihar, lamarin ya faru ne a ranar kasuwa lokacin da marigayin yake gudanar da aikinsa. Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani Tankokin mai sun yi bindiga a Zariya Rahotanni sun nuna cewa, ana zargin Salisu ya buga wa jami’in dutse a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa. Hukumar ta ce ta kama wanda ake zargin ne a gidansa da ke Shuwarin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya  yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.” A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya yi jawabi kan  ziyarar mataimakin babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA wanda ke shirin isa birnin Tehran a yau litinin. Araqchi ya bayyana cewa “babu wani shiri na ziyartar wata tashar nukiliya kafin a cimma wata matsaya kan hakan,” ya kara da cewa wannan tsarin “zai dogara ne kan dokar majalisar dokokin kasar Iran kawa,” kuma “ba za a fara wasu...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza. Mataimakiyar  Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman  cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba. Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin...
    Wata kotu a kasar Chadi ta daure tsohun firai ministan kasar Succes Masra shekaru 20 a gidan kaso da taran caifa biliyon guda a jiya Asabar. Shafin yanar gizo na Labarai Afrika Newas ya kara da cewa kotun ta tabbatar da laifin kan dan siyasar, kuma dan adawa da gwamnatinn Debi, da laifin watsa wasu kalaman batanci da raba kan mutane, har ila yau da hannu cikin rigimar Mandakao ina ya kai ga rasa rayuka masu yawa. A cikin watan Mayun da ya gabata. Lawyan dan siysan ya bayyana rashin amincewa da hukuncin, ya kuma bayyana cewa an yi amfani da sharia don warware matsalar siyasa ne kawai. Akai wasu mutane 74 wadanda suka gurfana a gaban kotun dangane da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati  a jiya Asabar a nan Tehran. Jakadan ya gabatarwa ministan rahoto kan inda dangantaka tsakanin Iran da saudiya yake. A na shi bangaren ministan ya bayyana kara karfin da dangantaka tsakanin kasashen musulmi biyu yana taimakawa da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
    dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron.   “Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane   Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya.   Mahalarta taron sun hada da; Sakataren Gwamnati na Tarayya, Sanata George Akume, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Christopher Musa, Hafsan Hafsan Sojin Sama Hassan Bala, Kwamanda Janar na NSCDC Dr. Ahmed Abubakar Audi, Shugaban Gwamnonin Arewa, Mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara Da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Hon. Abdulrazak...
    Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a hare-haren Isra’ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza. “Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina,” kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar. Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.
    Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon saukar agajin da aka kai a zirin Gaza ya kai Falasdinawa 23 tare da jikkata wasu 124 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon saukar da agaji ta hanyar jiragen sama tun bayan fara yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan zirin Gaza ya karu zuwa 23, yayin da wasu 124 suka samu raunuka, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar. Ofishin ya tabbatar da cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, cewa: Akasarin wadannan kayan agajin da jiragen saman ke watsowa ta sama suna fadowa ne a yankunan da ‘yan mamaya suka mamaye, ko kuma a cikin unguwannin da...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza. Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi. Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka. DW ya ruwaito cewa, dukkan...
    Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba,  sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a  nan gaba.” A ranar  Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan...