2025-09-17@21:54:19 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1678

«Hausa da Hausawa»:

    Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da ta karfafa matakan yiwa kananan hukumomin jihar 27 jagoranci akan sha’anin mulki da harkokin kudi domin inganta ayyukan su. Shugaban Kwamatin, Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan kiran a karshen ziyarar kwanaki 3 da kwamatin ya yi a ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar a Dutse. Alhaji Aminu Zakari wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa a majalisar dokokin jihar Jigawa, ya ce ziyarar kwamatin na da nufin tantance yadda ma’aikatar ta ke gudanar da ayyukan ta, ta fuskar harkokin mulki da na kudi da kuma dangantakar aiki tsakanin ta da kananan hukumomin jihar 27 kamar yadda tsarin mulki ya dorawa majalisa nauyi. A nasa jawabin, mataimakin shugaban...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
    Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa  tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar  kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya. Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai. A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya  bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi...
    Nijeriya dai ta daɗe tana fama da ta’addancin Boko Haram da ISWAP a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...
    Gwamnatin  kasar Iran ta bayyana wasu abubuwan da bata amince da su ba, a jawabin bayan taro na musamman na kungiyar kasashen musulmi ta (OIC) wanda aka gudanar a birnin Doha na kasar Qatar a ranar litinin 15 gawatan Satumba da mukeciki. Sannan ta kara tabbatar da goyon bayanta ga gwagwarmayan da Falasdinawa suke yi da HKI don kwatar kasarsu da ta mamaye. A cikin wani bayanin da ma’aikatar harokokin wajen kasar Iran ta fitar a yau Laraba, Jumhuriyar Musulunci ta Iran, tana kara jaddada goyon bayanta ga al-ummar Falasdina, kuma tana kara jaddada tir da allawai da kissan kiyashin da HKI take yi a Gaza da kuma sauran yankunan falasdinawa da ta mamaye. Kuma tana godewa mutanen kasar Iran...
    Falasdinawa 78 ne aka kashe a yau a Gaza, mafi yawansu a birnin Gaza a yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a kasa da kuma umarnin tilastawa mazauna Gaza yin kaura. An bayar da rahoton karin mutuwar mutane uku sakamakon yunwa da killace yankin. Mazauna Gaza sun bayyana tashin bama-baman a matsayin abun tashin hankali da kuma yunkurin shafe wata al’umma. Sojojin Isra’ila sun zafafa kai hare-hare a birnin Gaza, inda suka kai hari kan unguwannin da ke da yawan jama’a. Katangar da Isra’ila ta kakaba mata da kuma karancin abinci na ci gaba da zurfafa rikicin jin kai. Yakin da Isra’ila ta kwashe watanni ana yi a Gaza ya janyo hasarar rayukan fararen hula da dama....
    A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.   Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku wannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Yakin da aka kwashe fiye da shekara ana yi yankin zirin Gaza ya haifar da mummunar asara rayukan fararen hula, yayin da lamura ke ci gaba da dagulewa a yankin inda Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi ta hanyar kai hare-hare ta sama da kasa da kuma tana amfani da yunwa a matsayin wani makami na kisan mummuke, hakan ya jawo damuwa sosai a mataki na kasa da kasa na irin laifukan yaki da kuma cin zarfin dan adam da Israila ke yi. Tun watan oktoban shekara ta 2023 sojojin isr’ila sun kai hare-hare da yayi sanadiyar shahadar falasdinawa sama da 64964 tare da jikkatar sama da 165312, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana. Kungiyoyin...
    Tsohon Shugaban Ƙasar najeriya, Goodluck Jonathan, ya isa birnin Accra, na Ƙasar Ghana, domin halartar taron Democracy Dialogue na 2024 da Gidauniyarsa ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar. Taron na bana, mai taken “Dalilan Da Ke Sa Dimokuraɗiyya Ta Mutu”, zai hada shugabanni da masana don tattauna ci gaba, kalubalen, da makomar dimokuradiyya a Yammacin Afirka ke fuskanta. Jonathan ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta karfafa dimokuraɗiyya a yankin tare da kawo zaman lafiya, tsaro da kyakkyawan shugabanci. Taron Democracy Dialogue ya zama muhimmin dandali a kowace shekara a Yammacin Afirka don tattauna makomar dimokuradiyya, inda a baya ya kan jawo ’yan siyasa, kungiyoyi, da abokan hulda na kasa da kasa.  A wannan karon ana sa...
    Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ta haramta shirya duk wata muƙabala tsakanin mawaƙan yabon Annabi (S.A.W), tare da gayyatar mawaƙa Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi su bayyana a gabanta. Hukumar ta kuma gayyaci mawaƙan ne tare da sauran waɗanda suka jagoranci muƙabalar da fitattun mawaƙan biyu suka yi ranar Litinin, da su bayyana a gabanta cikin sa’o’i 24. Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu Hakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɓullar wata muhawara da aka yi tsakanin Usman Maidubun Isa da Shehi Mai Tajul’izzi kuma ta karade shafukan sada zumunta, wacce hukumar ta bayyana a matsayin karya dokokin aikinta. Shugaban...
      Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar. Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata. NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan
    JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa  wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar. Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar. An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin...
    Babban daraktan kamfanin dillancin labaran kasar Qatar ya bayyana cewa taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ke tafe yana nuni da wani muhimmin sauyi na hadin kan kasashen larabawa da musulmi dangane da laifukan da ake aikatawa kan al’ummar Palastinu. A cewar Pars Today, dukkanin idanuwa a ranakun Lahadi da Litinin (15-16 ga Satumba, 2025) za su kasance a Doha, babban birnin kasar Qatar, wanda zai karbi bakuncin taron gaggawa na shugabannin kasashen Larabawa da na Islama, don ba da amsa ga baki daya kan harin da Isra’ila ta kai kan Qatar. Ana gudanar da wannan taron gaggawa ne a cikin yanayi na musamman na yanki da na duniya kuma ya biyo bayan harin da...
    “Sauran motocin da ke cikin ayarin, ciki har da wacce ke ɗauke da shugaban majalisar, da ƙyar suka iya tsayawa wanda tsakaninsu mitoci kaɗan ne daga wurin da haɗarin ya afku,” in ji wani ganau.   Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa, an garzaya da jami’an ‘yansandan da suka samu raunuka zuwa babban asibitin Gumel a sume amma daga baya sun farfaɗo.   Da yake magana kan lamarin, mataimakin shugaban majalisar, Aqeel Akilu, ya yi godiya ga Ubangiji cewa, ba a rasa rayuka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake. A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.   A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.   Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.   Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.   A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.   Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana...
    Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.” Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce harin, ha’inci ne da wauta.” Sakatare-Janar na Kungiyar ya bayyana “cikakken goyon baya” ga Qatar bayan abin da ya kira “cin zarafin Isra’ila”, yana mai jaddada cewa dole ne kasashen duniya su dauki kwakkwaran mataki kan Tel Aviv. Shi ma da yake jawabi a taron share fagen kasashen musulmin da na Larabawa, firaministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar. Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, yayin da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa da na kasashen musulmi suka halarci taron gaggawa na Doha, domin tattauna harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a kasar Qatar. Babban jami’in na Hamas ya yi kira ga shugabannin yankin da ke halartar taron da su mayar da Isra’ila saniyar ware a siyasance da ta fuskar tattalin arziki...
    Ramezan sharif  wani babban jami’I yace idan gwamnatin HKI ta yi kuskure kan kasar Iran, za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin, yace ba zamu jira taimakon kowa ba wajen kare kasarmu domin muna da karfi wajen kare kasa. Da yake Magana a gaban manema labarai a wajen bikin cika shekaru 2 na ambaliyar alaqsa wanda dakarun gwagwarmayar yanto palasdinu suka kaddamar kan HKI,yace harin ya fantsama alamarin falasdinu a duniya, Har ila yau ya kara da cewa harin na 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ya nuna cewa isra’ila ba ta da wahalar yin galaba akanta, kuma al’ummar Palastinawa sun kuduri aniyar ci gaba da gwagwarmaya da gwamnatin mamaya da ta shafe shekaru tana aiwatar da kisan...
    Rahotanni sun bayyana cewa an fara taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da na musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, domin share fage na taron shuwagabannin kasashen da zaa yi gobe litinin in mai duka ya kaimu , domin tattaunawa kan harin baya bayan nan da Isra’ila ta kai Qatar, Taron zai tantance matakin diplomasiya da zaa dauka kan hari da Isra’ila takai kasar  Qatar a yankunan fararen hula da zimmar kasashe jamai’an kungiyar Hamas, harin yayi sanadiyar shahadar mutane 5 har da jami’an tsaron kasar  Qatar, kuma harin ya fuskancin yin tir daga kasashen duniya. Taron gaggawar da kungiyar kasashen musulmi  oic ta kira yana nuna yadda ake goyon bayan kasar Qatar a yankin, da kuma nuna damuwarsu...
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma a ENL Consortium, za su rinƙa yin amfani da lambApapaETO bisa nufin rage cunkoso a ciki da kuma wajen Tashar ta Apapa.ɗauke da launin rawaya,” Inji Lawal. Ya bayyana cewa, wannan sabon garanbawul ɗin da aka yi, za ta taimaka wajen matsalar ƙetarawa hanyar da manyan motocin ke fuskanta a Tashar ta Apapa. Lawal ya ci gaba da cewa, bisa nazarin da aka gudanar a...
    Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce. Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno. Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba....
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana dalilin da ya sa tawagarta ba ta halarci kada kuri’a kan batun Falasdinu ba Ofishin Jakadancin Iran ya jaddada cewa, duk wata hanyar warware matsalar Falastinu a zahiri dole ne ta dogara kan amincewa da hakkin al’ummar Falastinu na dogaro da kai da kuma watsi da duk wani batun tilasta musu yin gudun hijira. Ta kuma jaddada cewa, za a iya samun dawwamammen zaman lafiya ne ta hanyar kawo karshen mamaya da kuma samun cikakken ‘yancin kai gami da samun ‘yancin kai na kasar Falasdinu, tare da la’akari da ainihin nufin ‘yan asalinta-Musulmi, Yahudawa, da Kirista—ta hanyar kuri’ar raba gardama mai ‘yanci, kamar yadda aka gabatar a cikin takardar yarjejeniya mail amba S/2019/862. A...
    Kona mutanen da suka rasa matsugunansu a cikin tantunansu, a cikin dare mai wahala ga zirin Gaza Da sanyin safiyar Lahadi 14 ga watan Satumban shekara ta 2025 jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka ci gaba da kai munanan hare-haren bama-bamai a zirin Gaza, musamman birnin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata da dama. Sun kuma tayar da bama-bamai tare da tarwatsa gidaje da hasumiyai da nufin tilasta wa mazauna wurin tserewa tare da raba mafi yawan adadinsu da muhallinsu domin gudu zuwa tsakiya Gaza da kuma kudancin gabar tekun. Majiyoyin lafiya a asibitin Al-Shifa sun ba da rahoton mutuwar wani Bafalasdine tare da jikkatar wasu a wani harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wata...
    Amurka ta bayyana cewa: Harin da Isra’ila ta kai wa Qatar ba ya barazana ga kawancenta haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Asabar din nan cewa: Harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai a Doha babban birnin kasar Qatar a makon jiya ba zai shafi dangantakar Amurka da Isra’ila ba, duk da rashin gamsuwar da shugaba Donald Trump ya yi da yakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da yi da kungiyar Hamas a Gaza. Kafin ya tashi zuwa birnin Tel Aviv na Isra’ila, Rubio ya jaddada cewa, gwamnatin Amurka na ci gaba da tallafawa yahudawan sahayoniyawa, yana mai cewa a wasu lokuta ana samun aukuwar lamarin da kan iya...
    Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta yi nasarar korar Falasɗinawa sama da mutum 250,000 daga birnin Gaza tun bayan da suka fara zafafa kai hare-hare a yankin. Wannan dai na zuwa ne a yayin da jami’an Falasɗinu suka ce da dama sun gaza ficewa daga kudancin ƙasar saboda cunkoso. Najeriya ta daɗe tana fama da shugabanni marasa nagarta — Sanusi II ’Yan rakiyar amarya 19 sun mutu a hatsarin mota a Zamfara Mai magana da yawun sojojin Avichay Adraeeya wallafa haka a shafin X, yana cewa fiye da kashi 1 bisa huɗu na waɗanda suka rage a Gaza sun gujewa birnin don kare lafiyarsu. Sai dai, Hukumar Tsaron Farar Hula ta Gaza, ta ba da rahoton cewa adaɗin waɗanda suka...
    Tsohon kwamandan dakarun IRGC na kasar Iran Mosen Razai ya bayyana cewa kasashen yanking abas ta tsakiya su saurari fadowar boma boman HKI a kan kasashensu idan sun ki daukar matakin hada kai da kuma samar da rundunar kawance don fuskantar haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rezayi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, kasashen Saudiya, Turky da Iraki su jira randa boma-baman HKI zasu fada a kan kasashensu. Rezai ya bayyana haka ne rana guda kafin a fara taron gaggawa na kasashen larabawa da musulmi a yau lahadi a birnin Doha na kasar Qatar. Ya ce idan taron na Doha ya kasa samar da kawaice kasashen don fuskantar...
    A birnin Auckland, babban birnin kasar New Zealanda, dubban mutane sun fito tattaki da jerin gwano don goyon bayan al-ummar Falasdinu a gaza kan kissan kiyashin da HKI take wa mutanen gaza kimani shekaru biyu da suka gabata. Tashar talabejin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, a jiya Asabar 13 ga watan Satumba ne masu shirya jerin gwano a birnin Auckland, na kasar suka bada labarin cewa wannan shi ne tattaki mafi girma wanda aka gudanar a cikin kasar don goyon bayan al-ummar Falasdinu tun lokacin da aka fara yakin kimani shekaru biyu da suka gabata. Wadanda suka shirya zanga zangar sun bayyana cewa mutane kimani 50,000 suka fito wannan tattakin na goyon bayan Falasdinawa a Gaza, da...
    Wani gini mai hawa uku da ake ginawa ya rufta kan mutane a unguwar Yaba, da ke Jihar Legas. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ginin ya rufta ne da misalin ƙarfe 8 na dare. Gwamnatin Kuros Riba ta bankaɗo ma’aikatan bogi 800 HOTUNA: Mahaifiyar Dangote ta halarci gasar karatun Alƙur’ani ta Shetty a Kano Shaidu sun ce akwai mutane biyar zuwa shida a cikin ginin lokacin da abin ya faru. NEMA ta ce ta ceto mutum huɗu, kuma an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu. Sai dai hukumar ta ce ba a tabbatar da adadin waɗanda har yanzu suke ƙarƙashin ginin ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...
    Jami’in kungiyar Hamas yayi tsokaci kan yunkurin kashe tawagar kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a Doha Jami’in kungiyar gwagwagrmayar Musulunci ta Hamas, Osama Hamdan ya ce: Yunkurin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi na kashe tawagar da ke tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar wani hari ne kai tsaye kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tsagaita wuta. Ya kara da cewa a wata hira da aka yi da shi a gidan telebijin, “yunkurin kashe tawagar Hamas hari ne kai tsaye kan shirin shugaba Trump, idan har Isra’ilawa sun amince da Shirin na Trump, to su saurari martanin Hamas, maimakon mayar da martani ta hanyar jefa bam a birnin Doha da wurin taron jami’an kungiyar.” Hamdan ya yi...
    Sama da Falasdinawa 228,800 ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren kisan kiyashin ‘yan sahayoniyya kan Gaza a cikin wannan mako Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; Falasdinawa 38 ne suka yi shahada yayin da wasu 200 suka jikkata da aka kai su asibitoci a yankin cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana a cikin rahotonta na kididdiga ta yau da kullun cewa, daga cikin wadanda suka yi shahadan akwai biyu da aka ciro daga karkashin baraguzan ginin, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu daga kisan kiyashin da sojojin mamayar Isra’ila ke yi tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023 zuwa shahidai 64,756 da kuma jikkatan 164,059. Tun...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci babban taron kasashen musulmi da na  Larabawa da za a yi a Doha a ranakun Lahadi da Litinin, taron da Qatar ta kira domin samar da tallafi ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar a ranar 9 ga watan nan kan kasar ta Qatar. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce zasu halarci taron yana mai cewa shi da shugaban kasar za su gabatar da jawabai. “Lokaci ya yi da za a yi aiki, kuma kalmomi kadai ba su isa ba,” in ji shi yayin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na IRIB a yammacin ranar Alhamis, yana...
    Ma’aikatar kula da cinikayya ta Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, biyo bayan amincewar kasashen Sin da Amurka, He Lifeng, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma mataimakin firaministan kasar, zai jagoranci wata tawaga zuwa Spaniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Satumba, domin tattaunawa da tawagar Amurka. A cewar ma’aikatar, bangarorin biyu za su tattauna kan haraje-harajen Amurka da yadda aiwatar da matakan kayyade fitar da kayayyaki da batun manhajar TikTok da sauran batutuwan tattalin arziki da ciniki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, SABER wani shiri ne na shekaru biyar, wanda ya dogara da aiki, wanda Bankin Funiya ke tallafawa, wanda aka tsara shi cikin tsanaki domin wargaza shingayen faɗuwar jari, da zaburar da sana’o’i masu zaman kansu, da samar da ayyukan yi masu ɗorewa ga al’ummar Zamfara.   Za a raba Naira 150,000 ga mutum 2,000 a faɗin jihar domin tallafa wa ƙananan sana’o’i. Bugu da ƙari, mutane 1,000 a ƙanana da matsakaitan sana’o’i za su karbi Naira 500,000 kowanne. Haka kuma, mutane 60 daga matsakaita da manyan ‘yan kasuwa za su ci gajiyar tallafin Naira miliyan biyar kowannen su. A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa, SABER ba wani abu ba ne na yau...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Bai kamata a ji tsoron tattaunawa ba saboda hanya ce ta jaddada zaman lafiya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Ana gudanar da dukkan ayyukan diflomasiyya cikin cikakken hadin kai tare da hukumomin da abin ya shafa, kuma bisa takamaiman umarni da ayyuka. Ya ce: “Ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare hakki da tsaron al’umma, kuma ba za su taba tasirantuwa da kage-kagen yanayi ba, kuma za su yi aiki da karfi da azama wajen tabbatar da muradun al’ummar Iran.” Wannan dai ya zo ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Iran a yammacin jiya Alhamis, inda ministan harkokin wajen kasar Abbas...
    Mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasan ya jaddada ccewa; Dole ne duniya ta daina yin shiru game da zaluncin ‘yan sahayoniyya Ali Akbar Velayati mai ba da shawara ga jagora kan harkokin kasa da kasa ya yi Allah wadai da wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai a kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne duniya ta daina yin shiru kan zaluncin yahudawan sahayoniyya saboda ba su san iyaka kan laifukansu ba. Velayati ya bayyana a shafinsa na twitter game da harin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya suka kai wa kasar Qatar yana mai cewa: Keta dokokin kasa da kasa da keta alfarmar kasashe ya zama al’ada ga ‘yan sahayoniyya, kuma dole ne duniya...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za ta kai musu hari idan har ta samu iko, yana mai jaddada cewa, hanyar tunkarar haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ita ce mayar da martani mai karfi kanta. Limamin Sallar Juma’ar na Tehran ya bayyana a cikin hudubarsa cewa: “A matsayinsa limamin sallar Juma’ar Tehran, yana cewa, kuma dole ne gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya su ji cewa: Idan haramtacciyar kasar Isra’ila ta...
    Akalla Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a Falasdinawa 48 ne suka yi shahada a ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan zirin Gaza tun daga wayewar garin yau Juma’a. Majiyoyi a asibitocin Gaza sun bayyana cewa: Shahidai 27 ne a kai zuwa asibitin Al-Shifa, shahidi daya zuwa asibitin Al-Ma’amoudiya, shahidai uku zuwa asibitin shahidan Al-Aqsa, da shahidai biyar zuwa asibitin Nasser. Wani Falasdine ya yi shahada kana wasu kuma suka jikkata lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai hari a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan da ke arewacin birnin Gaza. Share 0...
    A yayin da suka yi alƙawarin yin adawa da aiwatar da harajin, ƙungiyar ta ƙara da cewa: “Yajin aiki na kan tebur idan gwamnati ta yi ƙoƙarin watsi da wannan gargaɗi ta ci gaba da aiwatar da waɗannan manufofi. Don haka, TUC ta umarci dukkan kwamitocin jihohi, rassan ƙungiya, da tsarin ta a faɗin ƙasa da su kasance cikin shiri, sanya ido, kuma su jira ƙarin sanarwa wanda zai iya kai wa ga ɗaukar mataki mai ƙarfi idan gwamnati ta ƙi sauraron muradin jama’a.” Ƙungiyar ta kuma kira ga abokan hulɗarta – ƙungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin ƙwararru, ɗalibai, ƙungiyoyin kasuwa, shugabannin addini da duk ƴan Nijeriya masu kishin ƙasa – da su tsaya tare da ita a wannan gwagwarmaya. “Tare,...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa yayin da ya sanya hannu kan yarjejeniyar gaggauta ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a yankin El, na yamma da kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye. A jiya Alhamis ne Netanyahu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, duk da kashedin da sassan kasa da kasa suka jima suna yi, cewa hakan zai gurgunta damar falasdinawa ta kafa kasa mai cin gashin kai. Yankin da Isra’ila ke fatan ginawa, mashigi ne a bangaren gabashin birnin Kudus, tsakanin birnin da yankin unguwar Ma’ale Adumim, ana kuma ganin gina shi zai haifar da mummunan tasiri, kasancewar hakan zai raba gabashin birnin Kudus da arewacin gabar kogin Jordan, wanda hakan zai dakile damar samar da dunkulalliyar kasar falasdinawa a nan...
    An samu ambaliyar ruwa a tituna da dama na tsakiyar Babban Birnin Tarayya Abuja sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka da safiyar Alhamis. Yankunan da ambaliya ta fi shafa sun hada da Asokoro, Guzape, Jabi, Kado da kuma Wuse. Wasu direbobi da suka zanta da Aminiya sun ce sun sha wahala wajen samun hanyar wucewa a unguwannin Asokoro da Guzape yayin ruwan saman. Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki A wani bidiyo da wani mai suna Prince Adebisi Adetunji ya wallafa a shafinsa na Facebook, an ga yadda ruwan ya mamaye titin Asokoro, inda direbobi da mazauna yankin suka yi ta kokarin yadda za su tsallake...
    “Gwamnatin Jihar Kaduna ta shirya tsaf domin ɗaukar matakin gaggawa kan kowanne yanayi da ka iya tasowa sakamakon wannan hasashen yanayi. An umurci KADSEMA da ta yi aiki tare da dukkan hukumomi masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken shiri. Ana roƙon jama’a da su bi dukkan umarnin kariya, su share magudanan ruwa, kuma su guji wuraren da ambaliya ke yawan faruwa a wannan lokaci,” in ji Maiyaki.   Hakazalika, sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), Dakta Usman Hayatu Mazadu, ya jaddada muhimmancin kasancewa cikin shiri da kuma bin matakan kariya da ke cikin sanarwar.   “Hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu guguwar iska da ruwan sama mai yawa musamman a ranakun Laraba...
    Da safiyar yau Alhamis ne aka gudanar da taron manema labarai game da taron tattaunawa karo na 12 na dandalin Xiangshan wanda za a gudanar a nan Beijing daga ran 17 zuwa 19 ga watan Satumban nan a cibiyar taro ta duniya ta Beijing, bisa taken “Hadin kai don kare tsarin duniya, da habaka ci gaban zaman lafiya”, inda za a gudanar da cikakken zama har sau 4 tare da kuma tarurruka 8 na rukuni-rukuni, da kuma taron shugabanni, da taron tattaunawa tsakanin matasan jami’an soja da masana, da na tattaunawa tsakanin manyan masana na Sin da na kasashen waje. Wakilan da za su halarci taron sun hada da na kasashe masu arziki, da manyan kasashe masu tasowa, da kananan...
    Rahotanni daga ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin, na cewa an kara wasu wurare hudu dake kasar Sin, cikin jerin muhimman wuraren ban ruwa na kasa da kasa ko WHIS. Wuraren sun hada da yankin ban ruwa na tafkin Chishan, da gonaki kan tuddai na kabilar Hani na Yuanyang, da madatsar ruwa ta Jianjiangyan, da tsohon mashigin ruwa na Mentougou dake kan kogin Yongding. An ce, za a shigar da wuraren cikin sabon jerin ne a hukumance yayin taro na 76, na kwamitin zartarwar hukumar kasa da kasa mai lura da wuraren ban ruwa da magudanansu ko ICID, taron dake gudana a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia. Da wannan kari, adadin wuraren dake kasar Sin da aka...
    Gwamnatin Belarus ƙarƙashin jagorancin Shugaba Alexander Lukashenko ta saki fursunoni siyasa 52 ciki har da fitaccen ɗan adawa, Mikola Statkevich da kuma ɗan jarida Ihar Losik, a wani yunƙuri da aka danganta da ruwa da tsakin Amurka. Shugaban Lithuania, Gitanas Nauseda, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter), yana mai cewa: “Mutum 52 da aka daure bisa dalilan siyasa sun tsallako kan iyaka daga Belarus zuwa Lithuania lafiya.” Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Kotu ta yanke wa jagoran Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 Ya ce yana “matuƙar godiya” ga gwamnatin Amurka da Shugaba Donald Trump bisa rawar da suka taka wajen sasantawa da cimma wannan matsaya. Daya daga cikin wadanda aka sako shi ne...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan shi ne karo na biyu da Tinubu ya ziyarci Faransa cikin watanni shida, bayan ziyararsa ta baya a watan Afrilu 2025. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa tafiyar ta kasance wani ɓangare na hutun shekara-shekara, ba don abin da ya shafi lafiyarsa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa idan kasashen Larabawa ba su goyi bayan ‘yan gwagwarmaya ba, to su ma za su fuskantar hare-haren Isra’ila” A jawabinsa babban sakataren kungiyar ta Lebanon ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila da Amurka suna aikata munanan laifuka a zirin Gaza da kuma yammacin gabar kogin Jordan da ke mamaye, yayin da al’ummar Falastinu suka yi tsayin daka duk kuwa da irin matsalolin da suke fuskanta. Bugu da kari, Sheikh Naim Qassem ya yaba da sadaukarwar Iran da al’ummarta da kuma al’ummar kasar Yemen, kan yadda suka tsaya tare da al’ummar Falastinu. A cewarsa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana goyon bayan Falastinu da al’ummarta da kuma tsayin daka domin...
    Stéphane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana a jiya Laraba cewa, MDD ta yi maraba da yarjejeniyar da Iran ta kulla da hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA, kan “tsarin da zai ba da damar komawa bincike a Iran”. A yayin taron manema labarai a wannan rana, Dujarric ya ce wannan yarjejeniya wani mataki ne mai kyau da Iran da IAEA suka dauka don komawa cikakkiyar hadin gwiwa. Majalisar tana kuma fatan za a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar. Dujarric ya kuma jaddada muhimmancin cikakkiyar hadin gwiwar Iran da IAEA. Yana mai cewa, hakan yana da muhimmanci wajen kafa wani tsari na dogon lokaci, wanda zai “tabbatar da shirin nukiliyar Iran gaba daya don zaman lafiya”. A ranar Larabar, yayin ziyararsa a Alkahira, babban birnin...
    Za a kuma ƙaddamar da sabon shiri, Nigeria@65 Compendium, wanda zai zayyano ci gaban ƙasa a fannoni kamar shugabanci, tattalin arziƙi, da ci gaban ƙasa a tsawon shekarun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Zaɓen Nijeriya INEC ta amince da jam’iyyar ’yan haɗaka ta ADC, ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark. Wannan tabbaci na zuwa ne bayan hukumar ta wallafa sunayen shugabannin jam’iyyar a shafinta na intanet, abin da ya kawo ƙarshen dogon jira da aka yi tun bayan ayyana ta a matsayin jam’iyyar haɗin kan ’yan adawa a ranar 2 ga Yuli. Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal Yadda zanga-zangar adawa da rashawa ta rikiɗe zuwa tarzoma a Nepal Tun a watan Yulin ne dai gamayyar ’yan adawa suka ayyana David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar, tare da tsohon Gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin sakatarenta na ƙasa. Sai dai kafin yanzu, INEC ba ta sanya sunayensu a...
    Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun banka wa gidansu wuta a unguwar Dallu da ke birnin Kathmandu a ranar Talata. Bayanai sun ce masu zanga-zanga a ƙasar mai tsaunuka da ke fama da tashin hankali mafi muni cikin shekaru da dama sun tarfa matar tsohon firaministan ne a cikin gida kafin su kunna wutar. An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi An harbe ’yan sanda 3 har lahira a Kogi An garzaya da ita asibitin kula da waɗanda ibtila’in ƙuna ya afkawa da ke Kirtipur cikin mummunan yanayi, amma daga ƙarshe ta ce ga garinku nan sakamakon munanan raunuka da ta samu. Rasuwarta ta zo ne a daidai lokacin...
    Sojojin HKI a yau Laraba sun tsananta hare-hare a cikin birnin Gaza, inda ta rusa hasumiyyar Birnin inda daruruwan falasdinawa suke rayuwa, saboda cimma manufarta na mamaye birnin gaba daya. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a safiyar yau laraba ce jiragen yakin HKI suka yi ruwan boma bomai kan Hasumiyar Tayba II wanda ke unguwar Rimal na birnin Gaza sun kuma dai-daita shi da kasa. Tun cikin kwanakin da suka gabata ne sojojin yahudawan suka fara rusa dogayen gine-gine a birnin Gaza, da nufin korar duk mutane birnin, hasumiyuar Tayba II na daga cikin dogayen gine-ginen da falasdinawa suke zama a cikinsa a gaza wanda HKI suka rusa..  Tun watan da ya gabata ne gwamnatin...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    Wasu mahara sun harbe jami’an ’yan sanda uku har lahira da safiyar ranar Laraba a wata madakatar mota da ke garin Egbe, a Ƙaramar Hukumar Yagba Yamma a Jihar Kogi. Kakakin rundunar jihar, SP William Aya, ne ya tabbatar da harin. Babban layin wutar lantarki ya sake faɗuwa Injin niƙa ya yi ajalin matar aure mai ’ya’ya 6 a Gombe Ya ce harin ya faru ne a kan iyakar Jihar Kogi da Jihar Kwara. SP Aya, ya ƙara da cewa, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Miller Dantawaye, ya tura tawaga ta musamman domin bincika yankin domin kama waɗanda suka kai harin. “Ina tabbatar muku cewa ’yan sandanmu uku sun mutu a Egbe yau. Kwamishina ya tura tawaga ta musamman, kuma muna...
    Babban Layin wutar lantarki na Najeriya ya sake faɗuwa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Kotun Ghana ta ɗaure ’yan Najeriya 3 shekaru 96 saboda satar mota Mamakon ruwan sama ya hallaka mutum 3 a Zariya Bayanan da Hukumar Gudanar da Wutar Lantarki, sun nuna cewa wutar ta ragu daga megawat 2,917 zuwa megawat 1.5 daga tsakanin ƙarfe 11 na safe zuwa 12 na ranar Laraba. Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC), ya tabbatar da faruwar matsalar a saƙon da ya aike wa kwastomominsa. Ya ce wutar ta ɗauke ne sakamakon matsalar da aka samu daga layin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe. “Saƙonmu zuwa...
    Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi  hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a fara aiwatar da harajin man fetur a watan Janairun 2026 ba lokacin da za a fara aiwatar da wasu harajin da shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a bana. Har yau, babu wani shiri na gaggawa na aiwatar da shirin fara cire harajin kashi 5 na man fetur  da ‘yan kasa suke sha,” in ji Ministan a martanin da ya mayar dangane da cece-ku-ce...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza A matsayin martani ga kuri’ar raba gardama kan halaccin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Gaza da ake zalunta, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamene’i ya ba da izini na addini na fitar da wani kaso na kudaden Khumusi don haka. A cikin cikakken labarin, a baya-bayan nan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba da izini na addini na ba da izinin bayar da wani kaso na kudaden Khumusi ga al’ummar Falastinu da ake zalunta a Gaza. Ga rubutun tambaya da amsar, kamar yadda gidan yanar gizon KHAMENEI.IR ya...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kasashen musulmi da na Larabawa su yi Allah wadai da yin tir da harin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga ‘yan uwanta na kasar Qatar, yana mai cewa: Dole ne kasashen musulmi su dauki mataki da gaske wajen tofin Allah tsina kan gwamnatin mamayar Isra’ila da yin tir da laifukan da take aikatawa kan al’ummomi. A cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani a yammacin jiya Talata, shugaba Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, rashin imanin da Amurka ke da shi ne ya sa yin shawarwari da wannan kasa ba shi da amfani. Wannan labarin daga Pars Today ya yi nazari kan matsayin Imam Khamenei dangane da mugun imanin Amurka da manufofinsa. Menene ra’ayin Imam Khamenei kan mugun imanin Amurka da manufofinsa? Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a wata ganawa da yayi da dakarun Basij na Iran ya yi ishara da cewa Amurka ba ta cika alkawuran da ta dauka yana mai cewa: “A cikin JCPOA, sun ce, ‘Idan kun rage ayyukan masana’antar nukiliya ku, za mu yi waɗannan abubuwa: ɗage takunkumi, ɗaukar wasu ayyuka, yin wannan da wancan.’ Shin sun yi...
    “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun rubuta a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me yasa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: Mun tashi don ci gaba da bege. Rasa bege na nufin watsi da mutanen Gaza da kuma mika su ga gwamnatin zalunci. “Jared Sacks” da “Zukiswa Wanner,” marubuta da masu fafutukar al’adu da ke zaune a Cape Town, sun lura a cikin wata kasida ga Al Jazeera mai taken “Me ya sa za mu je Gaza tare da jiragen ruwa na ‘Sumoud’ na duniya?”: A cikin watanni 23 da suka gabata, mun shaida yadda gwamnatin wariyar launin fata ta...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun jari a duniya, Gwamna Lawal ya jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen sauya labarin Zamfara daga ƙalubale zuwa wani babban matsayi mai cike da damarmaki.   “Gwamnatina ta himmatu wajen samar da ingantaccen yanayi da ɗorewar yanayin zuba jari. Ina nan a yau a matsayin abokin tarayya, a shirye nake na ba ku cikakken haɗin kai don buɗe hanyoyin jin daɗin gare mu duka....
    Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai birnin Doha na kasar Qatar ya kuma bayyana cewa hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Haka ma babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Ahmad Gaith ya yi tir da hare-haren da HKI ta kai gine-gine a Doka. Sannan kasashen Iran Saudia da Hadaddiyar daular Larabawa duk sun yi allawadai da hare-here. Gwamnatin kasar Turkiyya ta yi allawadai da...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi watsi da abinda yazo cikin bayanin bayan taro na kungiyar kasashen Larabawa na cewa tsiran Abu Musa da Tumb babba da karami mallakin UAE ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran na fada a cikin bayanin da ta fitar a safiyar yau Talata kan cewa, da wadannan kasashen sun fidda bayanai kan al-ummar gaza wadanda HKI take kissa dare da rana da yafi masu. Bayanin ya bukaci kasashen Larabawa su maida hankalinsu kan kasar Falasdinu da aka mamaye su kum yi aiki don hada kan a-ummar musulmi su tunkari HKI a kan ta’asan da take aikatawa a gaza, da sun yi abinda...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata...
    A cikin jawabai daban-daban da kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sukayi sun yi marhabin da farmakin da wasu mahara suka kai a jiya Litinin a arewacin birnin Quds, inda suka bayyana hakan a matsayin martani ga kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniyawa take yi kan al’ummar Falastinu, musamman a zirin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Irna, ya nakalto daga shafin tashar talabijin ta Al-Masirah cewa, kungiyar Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar tana mai jinjinawa da aikin wanda ta danganta da jarumtaka. Muna mika gaisuwar bajinta ga farmakin da mayakan gwagwarmayar Falastinawa biyu suka kai a matsugunan yahudawan sahyoniya ta Ramot da ke arewacin birnin Quds da suka mamaye. Ta kara da cewa wannan farmakin wani martani ne ga laifuffukan...
    Hukumomi sun shawarci jama’a su tabbatar da cewa gidajensu suna da tsaro da karko, tare da kaucewa gina gidaje a kan magudanan ruwa a wannan lokacin na damina. Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa Kirikasamma na daga cikin wuraren da za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Kwamitin ya kuma jaddada buƙatar wayar da kan jama’a da kamfen ɗin mutunta kai, da haɗa ɗabi’a mai kyau a cikin kundin karatu, da ɗaukar iyaye da ke taimaka wa ‘ya’yansu wajen magudi a matsayin masu laifi. Kwamitin ya gargadi cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, za a ci gaba da lalata ingancin tsarin ilimi a Nijeriya, abin da zai karya harsashin ci gaban ɗan Adam da tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tawagar kasar Iran ta maza da mata a wasan wushu a bangaren sanda da taolu ta samu gagarumar nasara inda ta samu lambobin yabo guda guda 10, zinariya 6 Azurfa guda 2 sai kuma tagulla guda 2, a wasan zakarun na washu karo na 17 da aka gudanar a kasar brazil, Gasar Wushu ta duniya ita ce ta farko a gasar da kasar Sin ta mamaye. inda Iran ta samun kambun mataimakiyar zakara ta sha gaban manyan kasashe biyu kamar Malaysia da Hong Kong, ya nuna irin gagarumin sauyi  a cikin tsarin wushu na duniya,  kuma ya nuna irin kaifin basira da bangarorin biyu suke da shi na maza da mata. Tawagar kasar Iran ta samu lambobin yabo guda 10...
    Kasar Sin da Tarayyar Afrika (AU), sun yi alkawarin karfafa goyon bayan juna wajen gina tsarin jagorantar harkokin duniya bisa adalci tare da tabbatar da zaman lafiya a duniya. An yi alkawarin ne a ranar Juma’a yayin wani taron manyan jami’ai a Addis Ababa na Habasha, albarkacin cika shekaru 80 da Sinawa suka yi nasarar turje wa harin Japan da yakin duniya na II. Da yake jawabi ga taron, Jiang Feng, shugaban tawagar kasar Sin a AU, ya nanata bukatar tunawa da tarihi da karfafa hadin gwiwa a duniya domin shawo kan kalubalen tsaro da duniya ke fama da su. Da yake jawabi a madadin kwamishinar kula da harkokin lafiya da jin kai da ci gaban al’umma Amma Twum-Amoah, babban...
    Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gube saboda nuna goyon bayan isra’ila kan kisan kare dangi da take yi a Gaza, ,  sun bukaci gwamnati da ta soke gayyatar wanda suka bayyana shi a matsayin babban mai laifin yaki dake da hannu wajen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar Gaza, da hakan ya sabama dukkan dokokin kasa da kasa. Mazu zanga zangar sun daga kwalaye da a ciki aka rubuta cewa trump kada ka zo,kuma mafiywancin wadanda suka halarci zanga-zangar mata ne da yara, kuma kungiyar dake nuna goyon bayan falasdinu ce ta jagoranci zanga-zangar, fira ministan malesiya anwar...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada suna da yawa a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan sassa daban-daban na Zirin Gaza a jiya Asabar Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da gwabza kazamin yakin da take yi a zirin Gaza a rana ta 701, lamarin da ya yi sanadiyar shahadan Falasdinawa da dama da kuma jikkatan wasu, da suke cikin masifar yunwa da kuma tilastawa Falasdinawa sama da miliyan biyu gudun hijira, a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru da kuma ci gaba da goyon bayan Amurka. Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama a yankuna daban-daban na zirin Gaza, inda suka auka wa unguwanni da dama da makamai masu linzami,...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wani mataki na tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afrika an kaddamar da wat kungiyar mai manufartallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka tare da saukaka ayyukan raya kasa da sarrafa albarkatun cikin gida. Bankin shigo da kayayyaki na Afirka ne ya kaddamar da kungiyar Don tallafawa kasuwanci, fitar da kayayyaki, da sarrafa albarkatun kasa a Afirka, wanda aka sanar da kirkiro da shi a yayin bikin ranar Afirka. Shugaban bankin Afrexim Bank Oramah Benedict ne ya sanar da hakan a hukumance a birnin Algiers, a yayin bikin ranar ‘yan kasashen Afirka. An gudanar da bikin ne a gefen ranar al’ummar kasashen Afirka, wanda firaministan rikon kwarya na kasar Aljeriya Sifi Ghrib ya jagoranta, tare da halartar jami’ai daga Afirka da dama. Ayman...
    A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, akalla Falasdinawa 68 ne suka yi shahada a Zirin Gaza, wanda ya kawo adadin wadanda suka rasu a yakin kisan kare dangi na Isra’ila tun watan Oktoban 2023 zuwa sama da 64,368. Akalla Falasdinawa tara ne sukayi shahada a wani kazamin harin da aka kai ta sama a birnin Gaza da Khan Yunus, ciki har da takwas lokacin da aka kai hari kan wani gini a unguwar Sheikh Radwan. Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto cewa, a ranar Asabar, wani yaro ya yi shahada a wani harin da Isra’ila ta kai kan wata mota a sansanin al-Mawassi da ke Khan Yunis. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bayan harin bam da Isra’ila...
    Ƙungiyoyin makarantu da na addinin Musulunci a Jihar Gombe, sun roƙi gwamnatin jihar da ta sassauta dokar taƙaita hawa babur daga ƙarfe 7 na yamma zuwa 6 na safe, domin sauƙaƙa zirga-zirga yayin bukukuwan Mauludi. Shugaban ƙungiyar makarantun Islamiyya na Jihar, Alhaji Muhammadu Nuhu, ya ce yawancin masu zuwa wajen bukukuwan na amfani da babura ne. NNPP ta kori Kofa daga jam’iyyar, ta yi barazanar maka shi a kotu ’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo Ya ce ana kammala bukukuwan da misalin ƙarfe 10 na dare, amma dokar tana fara aiki tun 7 na yamma, don haka suka roƙi a sassauta dokar saboda muhimmancin Mauludi. Alhaji Nuhu, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa...
    Kasashen Duniya da dama ne suka damu game da irin halin da ake ciki a yanki gaza da kuma yadda yake kara ta’azzar inda adadin wadanda ke mutuwa yake kara yawa sosai kullum fiye da kowanne lokaci. Yanayin tsarin ilimi a Gaza yana gab da rushewa baki daya, inda makarantu da dama ko dai an rusa su,ko kuma sun koma sansanin yan gudun hijira, sojojin Isra’ila da gangan suke kai hari Asibitoci da wuraren kula da lafiya,  jami’an bada agaji sun yi  gargadin cewa idan yanayin ya ci gaba da tafiya a haka zai zama babban balai musamman ga yara kanana,a bangaren kwakwalwa da kuma ci gaba. Sai dai isra’ila ta yi ikirarin cewa dukkan hare-harenta tana kai wa a...
    Dubban magoya bayan kungiyar Hizbullah ta kasar labanon ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanar a cikin dare a birnin berut domin nuna adawa game da shirin Amurka da HKI na neman yan majalisar dokokin kasar su amince da batun kwance dammarar kungiyar hizbullah. Bukatar , wanda manzon musamman na Amurka tom barak  ya mika, da yan majalisar suka amince da shi wanda ministocin yan shi’a suka yi watsi da ita, sun bakaci ya kasance sojojin gwamnati ne kawai za su rike makamai, wanda ke ishara ga hakkin hizbullah na mallakar makamai don kare kanta, lamarin da yan gwagwarmaya da magoya bayansu suke ganinsa a matsayin wani makatani ne  kai tsaye na Amurka da isra’ila don matsin lamba da zai jefa...
    Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta kira yawaitar rashin ɗa’a daga wani rukunin magoya bayan tsohon gwamna kuma Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, da ta kira da suna “Badaru Boys.” Sanarwar ta zargi wannan rukunin da haddasa rikice-rikice a wuraren tarukan siyasa, tare da yunƙurin ɓata sunan gwamnatin Gwamna Malam Umar Namadi. Ta bayyana cewa hakan ya faru a wurare da dama ciki har da Majiya, Gumel da kuma zaben cike...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran yayi tsokaci kan shurun ​​da kasashen yamma suka yi dangane da bunkasa makaman nukiliyar Isra’ila A yayin da yake tsokaci game da shirun da kasashen yammacin duniya suka yi dangane da fadada kera makaman nukiliyar yahudawan sahyoniya, ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya bayyana cewa, yin shiru da suka yi zai kawar musu da duk wani abin da ya dace da su, har ma da yin kalamai dangane da hana yaduwar makaman nukiliya. A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin yanar gizo a dandalin sada zumunta na X, Araqchi ya kara da cewa: Iran ta yi gargadin cewa: Tsananin da kasashen yammacin duniya ke yi na yaduwar makaman nukiliya a...
    Wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Jakadan kasar Iran kuma wakilin dindindin na kasar Iran a kungiyoyin kasa da kasa a birnin Vienna Reza Najafi ya sanar da fara wani sabon zagaye na shawarwari tsakanin tawagar kasar Iran da jami’an hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, yana mai cewa, wadannan shawarwarin za su tabbatar da wani sabon salon hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA. Reza Najafi ya yi nuni da cewa, ana gudanar da wadannan shawarwari ne a matsayin ci gaba da tuntubar juna tsakanin Iran da hukumar IAEA domin ayyana hadin gwiwa a cikin tsarin dokar da majalisar dokokin kasar ta amince da shi a cikin...
    Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” ta bayyana cewa: An tauye hakkokin yaran Gaza na ‘yancin samun ilimi, kuma makarantu sun zama matsugunan ‘yan gudun hijira Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana a jiya Juma’a cewa: An tauye hakkokin yara a zirin Gaza tun daga hakkin samun ’yancin ilimi, inda a yanzu haka makarantu sun zame matsugunan ‘yan gudun hijira, saboda an rusa musu gidaje ko lalata musu, yara ba su da wurin koyon ilimi. Kungiyar ta kara da cewa “fiye da yara 700,000 a Gaza ba su da ilimin boko.” Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fada a jiya Juma’a cewa sanarwar da Katz ya yi na kara kai...
    Jami’an kasa da kasa sun dora muhimmanci sosai kan babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya. Kuma sun bayyana cewa, muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin bikin, ya jaddada cewa, kasarsa na tsayawa kan tafarkin samun ci gaba cikin lumana, kuma hakan ya kara wa kasashen duniya imani da kwarin gwiwar koyon darasi daga tarihi, da hada kai don inganta zaman lafiya da ci gaban dan Adam. Mataimaki na farko ga shugaban majalisar dokokin Duma ta kasar Rasha, kuma shugaban majalisar sada zumunci tsakanin kasashen Rasha da Sin Ivan Melnikov ya bayyana cewa, shugabannin kasa...
    Wanda aka kama sunansa iro Garba mai shekaru 25 daga Zangwaye Fulani a ƙaramar hukumar Ajingi a Jihar Kano. Ya amsa cewa shi da wasu mutane huɗu sun yi garkuwa da mutane a Kano, Jigawa da Bauchi. An kuma samu rigunan sojoji guda uku a hannunsa. Kwamishinan ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mutane huɗun da ake zargi da hannu a garkuwar da ta faru a Sumaila, da ke Jihar Kano. A wani lamari kuma, ’yansanda sun kama mutane huɗu da ake zargi da fasa shago a ƙaramar hukumar Malam Madori. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Nuhu Yusif Saleh (19), Hassan Ibrahim (19), da Nura Musa (22). An ƙwato akwati mai ɗauke da kuɗi Naira 870,000,...
    Jakadan kasar Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  Redha Najafi ya bayyana cewa Iran da hukumar nukiliya ta duniya sun koma teburin tattaunawa game da shirin nukiliya iran na zaman lafiya domin duba hanyoyin da zaa bi domin ci gaba da aiki tare, Yace iran ta bar kofa a bude domin tabbatarwa da hukumar ta IAEA cewa lallai shirin nukiliyart na zaman lafiya ne zalla. kuma zaman ya kunshi wakilai daga nan Tehran da kuma wasu jami’ai  daga maikatar harkokin waje da kuma hukumar kula da makamashin duniya ta iran. Iran ta ce yanayin da ake ciki tun bayan harin da Amurka da Isra’la suka kai a tashoshinta na nukiliya dole ne ayi la’akari da alakar dake...
    Yakin ya farkar da Sin da duniya baki daya, wanda ya zama tushen kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, daga bisani kuma ya dora kasar bisa tafarkin zamani. Ga duniya, mulkin mallaka ya fara wargajewa. Kasashe da dama sannu a hankali suka fahimci cewa, in sun jajirce, za su samu ‘yancin kai. Tasirin yaki da zalunci da danniya da Jama’ar Sinawa suka yi, ya sa kasar ta kudiri aniyar yaki da zalunci da danniya a duniya ta rungumi manufar tabbatar da zaman lafiya, inda ta nuna wa duniya cewa, lokacin wariya da danniya, tsarin rayuwar dabbobi (na sama ya buge na kasa), ba zai dore ba amma samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, na sama ya yi...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata laifuka musamman a lokutan bukukuwa. An kama mace ɗauke da bindiga da N2m a otal Gwamnatin Yobe za ta ɗauki nauyin jinyar Malam Nata’ala Ya ce an baza jami’an tsaro a wuraren taro, wuraren Mauludi da sauran wurare. Kwamishinan ya gargaɗi jama’a da cewa dokar hana ɗaukar makamai tana nan daram, kuma duk wanda aka kama da su zai fuskanci hukunci. Ya kuma ce ba...
    Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa  ya bayyana halin da Iran take ciki kan sabon zagayen tattaunawa Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya tabbatar da cewa, ana musayar sakonni tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai cewa maido da zaman tattaunawa da Amurka zai yiwu ne kawai bayan samun tabbacin cewa ba za a kai wa Iran hari makamancin wanda ya faru, kamar yadda ya faru a baya-bayan nan ba. A wata hira da ya yi da kafafen yada labaran Turkiyya, Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Ana gudanar da magana tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani na yanki da na kasa da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba gudana, yana mai jaddada cewa: Iran na ba da muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran da gaske take yi wajen kare muradunta daga bukatun Turai Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya yi hira da kamfanin dillancin labaran kasar China na Xinhua, inda ya tattauna kan taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO), da yarjejeniyar dogon lokaci da kasar China, da kuma batun makamashin nukiliya na kasar Iran. Baqa’i ya bayyana cewa: Yarjejeniyar shekaru 25 tsakanin Iran da China ta fara aiki kuma tana ci gaba. Ya kuma kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana da kyau kuma tana ci gaba gudana, yana mai jaddada cewa: Iran na ba da muhimmanci sosai kan dangantakarta da China, kuma ziyarar shugaban kasar Iran...
    Falasdinawa 79 ne suka yi shahidai sakamakon tashin gobara da farmakin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai zirin Gaza a jiya Laraba Majiyoyin kiwon lafiya sun sanar a cikin dare cewa: An kashe Falasdinawa 79 sakamakon tashin gobara da hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ciki har da mutane 16 da ke jiran agaji. Majiyar ta bayyana cewa, an mayar da shahidai 25 zuwa Asibitin Al-Shifa, 6 zuwa asibitin Sheikh Radwan, 7 zuwa Asibitin Al-Ahli Arab Baptist, 5 zuwa Asibitin Rehabilitation Hamad, 1 Asibitin Al-Awda, 12 zuwa Asibitin Shahidai Al-Aqsa, 23 kuma zuwa Asibitin Nasser. Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai farmaki a zirin Gaza, inda...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jagoranci tawagar gwamnonin Arewa maso Gabas zuwa fadar shugaban ƙasa domin ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba. Ganawar  wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ta mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan da suka shafi yankin Arewa maso Gabas da suka haɗa da kammala muhimman ayyukan gina hanyoyin mota 17 cikin gaggawa, da kuma ci gaba da haƙo mai a rijiyoyin kan iyaka, musamman ma rijiyoyin Kolmani da tafkin Chadi. Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu Mai taɓin hankali ta haihu a tsakiyar kasuwa a Oyo Sauran gwamnonin da suka halarci ganawar sun haɗa da: Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Gwamnan...