Aminiya:
2025-07-24@23:39:23 GMT

Ambaliyar Mokwa: Gwamnonin Arewa sun nemi daukin gaggawa

Published: 1st, June 2025 GMT

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta bayyana ambaliyar ruwa mai tsanani da ta faru a Mokwa, Jihar Neja, a matsayin babbar ibtila’i, yana mai kira da a ɗauki matakan gaggawa don tallafi da hana sake faruwar hakan.

Shugaban Kungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana haka a yayin mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Jihar Neja kan ambaliyar da ta faru a ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2025, sakamakon ruwan sama mai kamar da bakin ƙwarya da ya yi sanadin rasa rayuka, bacewar mutane, da lalacewar gidaje, gonaki, da kayan more rayuwa.

Ya yaba da agajin gaggawa daga Gwamnatin Jihar Neja karkashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago da kuma kokarin hukumomin agaji wajen aikin ceto da tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi kira da a hada kai don kawo ɗauki cikin gaggawa da kuma samar da mafita mai ɗorewa, yana mai cewa: “Wannan bala’i ya nuna bukatar daukar matakan da za su hana sake afkuwar irin wannan annoba.”

Layya da hukunce-hukuncenta a Musulunci Gwamnatin Tinubu na amfani da talauci a matsayin makami — Atiku

Ya kuma tabbatar da goyon bayan gwamnatinsa wajen tallafa wa waɗanda abin ya shafa tare da fatan a samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Gwamnonin Arewa Mokwa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Muhimmin Taron NEC

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja
  • Ɓullar Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja
  • Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
  • Jami’an Shige Da Fice Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
  • Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Gabanin Taron Jam’iyyar
  • Tinubu Ya Tattauna da Gwamnonin APC Kafin Muhimmin Taron NEC
  • NEDC ta raba wa mutanen da ambaliya ta shafa kayan gini a Yobe
  • UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi
  • Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare
  • Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC