NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC
Published: 23rd, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Me sa jiga-jigan ’yan siyasar Najeriya ɓangaren adawa suka zaɓi inuwar Jam’iyyar ADC domin haɗa hannu da nufin kawar da Shugaban Kasa Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC daga mulki?
Da daren Talata ne dai manyan ’yan adawar, waɗanda suka haɗa da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufai da kuma ɗan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, suka yanke shawarar tsugunawa a ƙarƙashin inuwar ADC din.
Shin ko wannan jam’iyya tana da inuwa mai ni’imar da za ta iya riƙe wannan haɗaka?
Shin waɗannan ’yan siyasa za su iya ci gaba da shan hannu da juna har su kawar da gwamnati mai ci?
NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Kula Da Lafiyar Jikinku DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi Da Hurumin Dakatar Da Fina-finanmu”Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan ƙarfin da wannan ƙawance yake da shi na ƙalubalantar gwamnati mai ci.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Atiku Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
“Iyakar kasa ba wai kawai yanki ne na tsaro ba. Yanki ne na al’adu; yanki ne na tarihi; haka nan ma yanki ne na tattalin arziki. Kula da shige da fice na da matukar amfani ga ci gabanmu. Wajibi ne Nijeriya ta zuba jari a kan kula da nau’in mutanen da take tacewa wajen shiga kasa da kuma irin mutanen da muke tacewa wajen fita daga kasa.
“Dole ne mu yi nazarin nau’in ayyukan da bakin-haure ke yi da kuma yadda suke shafar tattalin arzikinmu. Muna bukatar tsame mutanen da ke kawo cikas ga ci gabanmu”, in ji Babandede.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA