’Yan acaba sun yi wa mai fura fyaɗe Abuja
Published: 2nd, May 2025 GMT
Jami’an tsaron sa kai sun kama wasu abokai biyu masu sana’ar acaba, bisa zargin yin fyaɗe ga wata Bafulatana mai tallar fura da nono a Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wani jami’in tsaron sa kai, Usman Dantala, ya ce abokan biyu sun yi wa Bafulatanar fyade ne da tsakar rana a yankin Ikwa da ke Ƙaramar Hukumar Gwagwalada.
Ya bayyana cewa ranar Asabar da misalin karfe 2:12 na rana ne abokan biyu suka yaudari mai faurar ’yar kimanin shekaru 19 zuwa daƙin wani abokinsu inda suka yi mata fyade.
Jami’in ya ce, sun kira Bafulatanar ne da cewa za ta sayar musu da nono a gidan wani abokinsu. A can ne suka yaudare ta shiga daƙin suka kuma yi mata fyade.
An kama matashi kan ‘satar’ ’yar maƙwabcinsa Wulaƙancin da ake mana a Kudu ya yi yawa —Hausawan LegasDantala ya ce wani maƙwabci ne ya ji hayaniya daga daƙin ta tagarsa, wanda hakan ya sa fita ya sanar da jama’a.
“Nan take makwabcin ya sanar da sauran mutane, waɗanda suka ruga zuwa daƙin, inda suka samu mai furar tana kuka a tuɓe, yayin da ɗaya daga cikin samarin ya tsere.”
Ya ce jami’an sun kama ɗayan wanda ake zargin, wanda kuma ya kai su wata daba inda suka kama ɗayan ma.
Daga baya jami’an sun kai mai furar asibiti, inda aka tabbatar da cewa an yi lalata da ita; aka miƙa waɗanda ake zargin ga ’yan sanda.
Kakakin ’yan sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, ba ta samu damar yin tsokaci kan wannan lamari ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dubban Mutanen Burkina Faso Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Shugaban Kasa Ibrahim Traore
Kwanaki kadan bayan wani furuci daga babban jami’in sojan Amurka a Afirka akan shugaban kasar ta Burkina, dubban mutanen kasar sun yi gangami na nuna goyon bayan Kaftin Ibrahim Traore
Gangamin na mutanen kasar Burkina Faso, ya biyo bayan maganganun da su ka fito daga kwamandan sojojin Amurka a Afirka Janar Michael Langley wanda ya zargi sojojin dake Mulki da amfani da ma’adanan kasar saboda kashin kansu maimakon yi wa mutane aiki.
Mahalarta gangamin sun daga kwalaye dake dauke da rubutun yin tir da furucin jami’in sojan na Amurka da kuma nuna goyon baya ga shugaban kasar.
Daga cikin mahalarta gangamin da akwai fitaccen mawakin kasar, Ocibi Joan,wanda ya siffata jami’in sojan Amurkan da dabbar daji mai cin mutane yana mai yin kira a gare shi da kasarsa da su daina yin karya.
Haka nan kuma ya kara da cewa: ” Mutanen Burkina ba su fada da kowa,amma a lokaci daya, ba za su bar masu wawason dukiyar kasarsu ba.”
Wani mutum da ya halarci gangamin Haruna Sawadogo ya fada wa manema labaru cewa, idan suna son ganin bayan Kaftin Traore ne, to su fara ta kan mutanen kasar.
Hakan nan kuma jaddada cewa ba za su bari abinda ya faru da Thoms Sankara ya faru dakanar Troare ba.