Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Ta Tabbatar Da Harin ‘Yan Bindiga A Banga
Published: 9th, April 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da wani mummunan hari da ‘yan bindiga suka kai a garin Banga, da ke cikin karamar hukumar Kauran Namoda, inda aka kashe mutane biyu tare da sace wasu da dama.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu da ke Gusau, babban birnin jihar.
DSP Abubakar ya ce bincike na ci gaba da gudana domin gano adadin mutanen da aka sace a harin.
Ya tabbatar da cewa ana kokari don ganin an ceto mutanen da aka sace cikin koshin lafiya.
Yazid ya kara da cewa an kara kaimi wajen daukar matakan tsaro domin hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.
Shaidu sun shaida wa Rediyon Najeriya cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin tsakar dare a ranar Laraba, inda suka buda wuta daga wurare da dama, lamarin da ya haifar da firgici ga mazauna garin.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi ta barna na tsawon sa’o’i, inda suka kashe wani dattijo da wata yarinya ‘yar shekara 18 mai suna Amina.
Ya ce da farko maharan sun sace kimanin mutane 26, amma ba su samu nasarar guduwa da su baki daya ba, sakamakon hanzarin da jami’an tsaro da ‘yan sa-kai suka yi.
Wakilinmu ya samu rahoton cewa hadin gwiwar jami’an tsaro da ‘yan sa-kai ya kai ga kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga. An kuma tabbatar da cewa maharan sun kasa guduwa da shanun da suka sace.
A cewar shaidu, jami’an tsaro da taimakon jiragen saman rundunar sojin saman Najeriya sun toshe hanyar da maharan ke kokarin tserewa ta kusa da kauyen Yamutsawa.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.
AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.
Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.
‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.
Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.