Leadership News Hausa:
2025-10-14@21:50:32 GMT

Sin Za Ta Kara Matsa Kaimi Ga Raya Sha’anin Mata Na Duniya

Published: 27th, February 2025 GMT

Sin Za Ta Kara Matsa Kaimi Ga Raya Sha’anin Mata Na Duniya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 30 da gudanar da taron harkokin mata na duniya na Beijing. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da amfani da damar da aka samu ta cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka, da yin kokari tare da kasahen duniya wajen sa kaimi ga raya sha’anin mata na duniya.

Lin Jian ya bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Fabrairu, an gudanar da taron tattaunawa kan murnar cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka bisa bukatun Sin da wasu kasashen da abin ya shafa, a yayin da majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD ta gudanar da taronta karo na 58, inda shugabannin hukumomin MDD mata suka halarci taron tare da gabatar da jawabi.

Lin Jian ya ce, a matsayin ‘yar sama jannati ta farko ta kasar Sin wadda ta shiga sararin samaniya, Liu Yang ta yi jawabi ta kafar bidiyo cewa, tunanin zaman daidaito na sha’anin binciken sararin samaniya na kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana kokarin raya sha’anin mata, wato tabbatar da yanayin yin takara cikin adalci ta bisa kyakkyawan tsari, kuma wannan ne aikin da aka gudanar bisa tunanin sanarwar Beijing. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi

Kishi halak ne kuma so ne yake kawo kishin. Masu irin wannan kishin karshensu nadama ce. Kishi wani abu ne da ake jinsa a cikin rai, kuma kishi ba sai akan aure ake yin sa ba.Hanyoyin da ya kamata abi wajen magance irin wannan shi ne; muna tuna komai yayi farko to yana da karshe, sannan ba kanta farau ba kuma ba kanta karau ba. Muna saka hakuri da tawakkali mu yi kiyayya ba mai zurfi ba, sannan mu yi soyayya ba mai zurfi ba, a karshe sai abin ya zo mana da sauki. Allah ya sa mu dace, amin.

 

Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:

Abubuwa da dama na haifar da kishi amma mafi lura shi ne rashin godiya a wajen Allah subahanahu wata’ala da kuma son zuciya tare da son rai irin na mata. Kishi shi ne son kasancewa da namiji a matsayin abokin tarayya ko zamantakewar Aure ba tare da wata ta ji ra’ayin hakan ba ko kuma ta nuna bukata tare da ra’ayin akan namijin da wata ke rayuwa da shi ba. Hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin kishi musamman a lokacin da miji zai karo abokiyar zama sun hada da hakuri, danne zuciya, tare da juriya hadi da biyayya ga duk wani umarni daga wajen miji don kuma kaucewa sabawa umarnin Allah da Manzon sa (S.A.W).

 

Sunana Nabila Dikko, Argungun Jihar Kebbi:

To mafi akasarin dalilai da ke sa mata irin wannan kishi shi ne; karancin fahimta da rashin hakuri, da son mallaki namiji su kadai, da son zuciya, kuma hakan na kawo rashin zaman lafiya da rikici da lalacewar dangantaka. Kishi wani abu ne da ke sa zuciya ta dinga son mallakar wani abu ita kadai ko abin da kake da shi ko tsoron rasa shi. A musulinci, kishi halas ne idan bai kauce wa ka’ida ba. Domin magance kishi dole sai mace ta dogara ga addu’a, ta daidaita tunaninta, ta rungumi gaskiyar cewa mijinta yana iya kara aure, sannan ta mayar da hankali wajen kyautatawa maigidanta ba tare da yin abubuwan da ba su dace ba. Shawarata ga mata su kasance masu natsuwa, su guji haddasa rigima. Sai maza ku kasance masu adalci, ku bayyana gaskiya, ku kiyaye hakkin kowace mata, a daidaita adalci ku daina haddasa tsananin kishi a tsakanin matanku.

 

Sunana Aminu Adamu, Malam Maduri A Jihar Jigawa:

To, da farko dai akwai jahilci domin shi ke jawo mutum ya kashe kan sa, don indai mutum yana da ilimi ya san illar kashe kai. Sai na biyu kuma rashin rungumar kaddarar da Allah ya kaddarawa mutum domin ita kaddara bata canjawa. To, kishi wani abu ne da Allah yake halittar mutane da shi maza da mata to a lokuta da dama maza su kan yi kokari wajen sarrafa nasu sabanin wasu daga cikin mata da kishin yake sa su aikata aikin da-na-sani ko ma su hallaka kan su.

 

Sunana Hafsat Sa’eed, daga Neja:

Kishi yana cikin addinin musulunci amma kuma akwai kishin hauka irin wanda mace za ta je ta hallaka ‘yar’uwarta ko abin da ‘yar’uwarta ta yi sai ta yi. Mutum yana da wahala ya daukowa kansa babban aiki. Idan namiji zai karo aure ya kamata ka bashi goyan baya, ka yi masa fatan alkhairi, haka idan ta shigo ka samu ku zauna lafiya dole akwai abin da zai sa ka yi kishi sai ka yi daidai misali ba wanda ya haura ka’ida ba.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi, daga Jihar Kano:

Babbar magana ai wadanan dai sun hada kansu da wahala da kuma da-na-sani dan kishi dai babu komai a cikinsa sai wahala. To, shashanci ne da rashin sanin ciwon kai. Kishi dai wani halitta ne wani kuwa dorawa kaine, kishiya babu dadi amma ayi hakuri a kau da kai. Sun yi hakuri su kara hakuri.

 

Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos, a Jihar Filato:

Babu shakka kishi na zama guba a wajen easy matan, musamman a lokacin da mazajen su za su kara aure. Wasu kan nemi jefa kansu ga fushin ubangiji ta hanyar kokarin tilastawa mazajen su jingine bukatar su, ta kara aure, amma kuma su kawar da kai daga halayyar sa ta neman mata a waje. Sannan su a karan kansu, idan ma ba su sha guba sun hallaka kansu ba, suna shiga malamai, matsafa, da ‘yan tsibbu, wadanda ke aikata shirka, don neman biyan bukatun su. Akwai wadanda sanadiyyar kishi suke gamuwa da ciwon hawan jini da ciwon zuciya, ko matsalar kwakwalwa.

 

Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nijeriya:

Kishi kam masifa ce babba, soyayya da kauna ke janyo wa wasu kishi, wasu kuma kwadayin dukiya da kyle-kyelen duniya. Danganta kansu ga mutuwa a kowani lokaci namiji bai zamo lallai ya rigata mutuwa ba, sannan mace ta sani lallai kishi halitta ce, amma bai halarta akan auren wata har ya zamo kin iya kashe kanki ba ko saboda abun duniya. Shawarata a nan su rage mummunan kishi, su nemi na kansu, su zamo masu godiya da kulawa a rayuwa wasu matan ko auren ma babu bare kwadayin dukiya da kishi.

 

Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:

Tabbas ana samun mata masu kishin da ya wuce hankali saboda son zuciya kuma gaskiya makomarsu bata kyau. Kishi dabi’ace da Allah ya halicci mata akai har ma wasu mazan ya kamata su nuna kishinsu ta hanya mafi kyau lokacin da mijinsu zai kara aure kuma su sani da ba a auren da suma ba a aurosu ba. Shawara a nan ita ce kowa ya ji tsoron Allah akan hakan.

 

Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja Jihar Neja:

Kishiya halitta ce sai dai kowa da yadda yake sarrafa nasa kalar kishin, har kullum muna kira ga matan da suke da tsanani kishi da kar su bari kishi ya rufe masu ido har ya kai ga sun aikata abun da za su zo suna da-na-sani. Biyewa Zuciya, kuma sannan a dabi’ar dan namiji baya son macen da ta cika tsanani kishi. Kishi wata aba ce da ubangiji ke halittar bawa da shi ba tare da ya sani ba. Tsananta addu’a da mika al’amura ga ubangiji a yayin da mijinki ya zo maki da zancen kara aure, dole za ki ji babu dadi a ranki amma in ki ka dage da addu’a sai komai ya zo cikin sauki. Shawara ta kada mu bari zukatanmu ya zamana ita ke sarrafa mu ba mu ke sarrafa ta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Taskira Illolin Da Ke Tattare Da Mallaka Wa Kananan Yara Wayar Hannu October 4, 2025 Taskira Bukatar Mutane Su Kula Da Warin Jikinsu September 27, 2025 Taskira Amfani Da Rashin Amfanin Auren Jari August 23, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya
  • Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata
  • Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata
  • Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba
  • Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya
  • Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • Jami’ar MDD: Taron Kolin Matan Duniya Ya Zo Daidai Lokacin Da Ya Dace
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Tsokaci A Kan Mata Masu Tsananin Kishi
  • Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro