Al’umma Sun Nuna Alhininsu Kan Takaddamar Akpabio Da Sanata Natasha
Published: 26th, February 2025 GMT
An shawarci majalisar dokokin kasar da su mai da hankali kan ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin kasar nan domin inganta shugabanci nagari.
Masu kiran waya a shirin “KAKAKI” na gidan Rediyon Najeriya Karama FM ne suka bada shawarar hakan a lokacin da suke ba da tasu gudunmawar a kan batutuwan da suka shafi kasa.
Sun bayyana damuwarsu kan rahotannin karar da wata sanata daga jihar Kogi, Natasha Akpoti, ta shigar kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, biyo bayan zargin bata suna.
Alhaji Ibrahim Alaramma, Idris Adamu Danfulani, da Sani Batira sun jaddada bukatar shugabannin majalisar su tabbatar da kafa doka mai inganci don yaki da talauci da rashin tsaro.
Shi ma da yake jawabi, wani bako a shirin, Alhaji Suleiman Muhammad ya yi kira ga gwamnati da ta kara samar da ayyukan raya kasa da ababen more rayuwa kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba.
Suleiman Kaura
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kwamatin Tantance Ayyukan Kananan Hukumomi Na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ya Isa Sule Tankarkar
Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su.
Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi.
A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki.
Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da duba kudin tarukan bangaren zartaswa da na kansiloli domin tabbatar da bin ka’idojin kashe kudaden gwamnati.
Karamin kwamati na daya bisa jagorancin wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya ya duba aikin masallacin kamsissalawati na Rugar Danqulili, da famfunan tuka tuka a Gabala/Dangwanki da Yanyawai da Fulanin Tagai da Rugar Hardo Daudu da gidan ungozoma a asibitin Jeke, da shirin noman rani a Maitsamiya.
Kazalika, kwamati na biyu bisa jagorancin wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari ya duba aikin gidan ruwa mai amfani da hasken rana a unguwar Sule Gabas da masallacin Juma’a na Hammado da makarantar Tsangaya a Danladi, da masallaci kamsissalawati na gidan mulki na Shugaban karamar hukumar da famfon tuka tuka na Gidan Idi Ruwa.
A nasa Jawabin, Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar Malam Tasi’u Adamu, Ya lura cewar, tantance sha’anin mulki da harkokin kudin kananan hukumomi ko shakka babu zai taimaka wajen kawo ci gaban yankunan karkara.
Malam Tasi’u Adamu ya kuma yi addu’ar samun nasarar ziyarar kwamatin domin ta yi tasiri wajen kawo cigaban rayuwar jama’ar yankin.
Usman Mohammed Zaria