Nebenzia : Hare-haren Sojojin Isra’ila a Lebanon da Syria na kara dagula lamura a yankin
Published: 26th, February 2025 GMT
Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin.
A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula zaman lafiya a yankin shi ne yadda Isra’ila ke ci gaba da mamaye yankin Golan na klasar Syria.
Sauran abubuwan da ke haifar da rashin zaman lafiya, a cewar wakilin Majalisar Dinkin Duniya, su ne yadda “Isra’ila” ke hana ‘yan kasar Lebanon da suka rasa matsugunansu komawa gidajensu a Kudancin kasar, da kuma ayyukan tada hankali da ta yi ta hanyar kai farmakin soji a lokacin jana’izar Sayyed Hassan Nasrallah a wasu yankuna na kudancin kasar ta Lebanon.
Jakadan ya yi Allah wadai da hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila” ta kai a baya-bayan nan a Lebanon da Siriya musamman bayan da Haaretz ta fitar da hotunan tauraron dan adam da ke fallasa shirye-shiryen sojojin mamaya na Isra’ila a kan iyakar Siriya.
Hotunan sun bayyana cewa, Isra’ila ta kafa sabbin sansanonin soji kimanin guda bakawai, tun daga Dutsen Hermon da ke arewacin yankin da ta kwace tsakanin Siriya da yankunan Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma.
Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar.
A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin.
Yayin mika kayayyakin ga mai kula da cibiyar kiwon lafiya, shugaban karamar hukumar Kirikasamma, Alhaji Muhammad Maji Wakili Marma, ya bukaci ma’aikatan lafiya da su tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin rabon kayan.
Haka kuma, ya yaba da kokarin Gwamna Umar Namadi da sauran abokan hulda wajen gyara cibiyoyin kiwon lafiya da gina gidajen Ungozoma a Kirikasamma da kuma fadin jihar domin inganta ayyukan kiwon lafiya.
Usman Muhammad Zaria