Wakilin Jagoran Juyi A Wurin Jana’izar Sayyid: Gwgawarmaya Za Ta Ci Gaba
Published: 23rd, February 2025 GMT
Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim, ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa: Jagoran jihadi mai girma, kuma shugaban gwgawarmaya a cikin wannan yankin, Sayyid Hassan Nasrallah ( Allah ya daukaka matsayinsa) ya kai matsayi na koli na daukaka da izza.
Sayyid Mujtaba al-Husainy ya kuma ce; A wannan lokacin za a binne gangar jikin Sayyid a cikin kasar da ya yi jihadi saboda Allah akanta, amma ruhinsa da kuma tafarkinsa na gwgararmaya zai kara daukaka fiye da kowane lokaci a baya.
Sayyid Mujtaba al-Husaini ya kuma ce:Makiya su kwana da sanin cewa, gwgawarmaya za ta cigaba da wanzuwa domin fuskantar zalunci da girman kai na duniya, ba kuma za ta karaya ba har sai an cimma manufa, da izinin Allah.”
Da yake Magana akan Sayyid Hashim Safiyuddin ( Yardar Allah a gare shi) ya bayyana shi a matsayin wani daga cikin taurari masu haske a cikin tarihin wannan yankin. Ya kuma kasance mataimaki mai tsarkin zuciya ga Sayyid Hassan Nasrallah.
A karshe Sayyid Mujtaba al-Husaini ya yi addu’a ga wadannan shahidan biyu masu girma da kuma sauran mujahidai da dukkanin shahidai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Sunday Marshall Katung Ya Sauya Sheka Zuwa Jam’iyyar APC
Sanata Sunday Marshall Katung, wanda ke wakiltar mazabar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa, ya sanar da hukuncin da ya yanke na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yana mai cewa wannan mataki ne da ya dace domin inganta aikin wakilci da kuma tabbatar da ƙarin haɗin kai ga al’ummar mazabarsa.
A cikin wata sanarwa mai taken “Sabon Babin Rayuwa: Saƙon Haɗin Kai da Manufa Ɗaya,” Sanata Katung ya bayyana cewa wannan shawara ta biyo bayan dogon shawarwari da aka yi da mazauna mazabarsa, jagororin siyasa, iyalansa da abokan aikinsa.
Ya ce, “Wannan sauyin matsayi yana fitowa ne daga niyyar gaskiya ta yin wa mutanenmu hidima cikin inganci, da tabbatar da cewa muryarmu tana da ƙarfi kuma ana jin ta a manyan teburan yanke shawara da ke tsara makomar al’ummarmu.”
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya zama dole ne bayan kiraye-kirayen da aka yi daga sassa daban-daban na mazabarsa, tare da yabawa irin sha’awar da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, suka nuna wajen yin aiki tare da shi domin kawo “ci gaba mai tarihi da ban mamaki” a yankin.
Sanata Katung, yayin canza shekan tare da Hon. Daniel Amos da wasu abokansa a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya nuna gamsuwa da “ayukan ci gaban” jam’iyyar APC a yankin Kaduna ta Kudu, yana mai cewa suna nuna adalci, daidaito, da ci gaba.
Ya ce, “Zamanin warewa da nuna bambanci, musamman a baya-bayan nan, yana gushewa, kuma ana maye gurbinsa da gwamnatin da ke da manufa da haɗin kai.”
“Saboda haka muna matsawa gaba domin tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun dore kuma sun yadu zuwa sauran al’ummomi da dama a yankin,” in ji shi.
Sanatan ya kuma roƙi abokai da abokan aiki da ba su goyi bayan wannan mataki nasa ba, da su mutunta ra’ayoyi daban-daban, tare da kaucewa barin siyasa ta kawo rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Ya ambaci kalmar Thomas Jefferson da cewa, “Ban taɓa ɗaukar bambanci a ra’ayi na siyasa, addini ko falsafa a matsayin dalilin janye ƙauna daga aboki ba.”
“A tare, mu ci gaba da zama ɗaya a manufa, mu dage da fata, kuma mu mai da hankali wajen samar da makoma mafi kyau ga al’ummar Mazabar Kaduna ta Kudu.”
Sanata Katung ya tabbatar da ƙudurinsa na ci gaba da aiki don haɗin kai da cigaba.
Daniel Karlmax