Magoya Bayan Tottenham Sun Yi Zanga-Zanga
Published: 23rd, February 2025 GMT
Sama da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham 1,000 ne suka yi zanga-ganga kan shugaban kungiyar, Daniel Leby kafin wasa da Manchester United a Premier ranar Lahadin da ta gabata. An yi ta kuwa da cewar ”Leby ya bar kungiyar da kuma ”Enic ya bar Tottenham” yayin da magoya baya suka rinka daga tuta a kusa da filin wasa, wadanda ke kiraye-kirayen a kawo canji.
An kuma tsara yin zaman dirshan da zarar an tashi wasan Premier a karawa da United, inda magoya baya suka bukaci da kowa ya tsaya a filin wasan Tottenham. An kafa kyalle a wajen zaman masu gida da wajen zaman baki da aka rubuta sakon cewar ”lokacin canji ya yi” domin ”shekara 24 an sauya masu horarwa 16 da lashe kofi daya.”
Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9 Babbar Gasar Wasannin Kankara Ta Zama Damar Tabbatarwa Duniya Niyyar Karfafa Zaman LafiyaKafin Tottenham ta buga wasa da Manchester United ranar Lahadi tana ta 15 a teburi, wadda ta ci wasa daya daga takwas baya da ta fafata. Tottenham ta lashe League Cup a 2008 – tun bayan da Leby da Enic suka mallaki kungiyar daga Sir Alan Sugar, kusan shekara 25 da ta wuce. To sai dai Tottenham ita ce kan gaba a samun riba a Premier League a tsawon shekarun, inda Leby ya samar da £1.2bn da aka gina katafaren filin wasa da kasaitaccen wajen atisaye.
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa Gabon
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta.
AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa.
Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take.
‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar.
Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar Brice Oligui Nguema, wanda aka zaba a matsayin shugaban kasar a ranar 12 ga Afrilu.