Fursunoni 3 sun lashe Gasar Al-Ƙur’ani a Kano
Published: 14th, February 2025 GMT
Wasu fursunoni uku da ke tsare a gidajen yari daban-daban sun lashe Gasar Musabakar Al-Kur’ani da aka gudanar a Jihar Kano.
Fursunoni sun lashe gasar da Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Jihar Kano ta shinrya a matsayin wani bangare na tsarin ilimin fursunoni.
An shirya musabakar ce da nufin sauya tunanin fursunoni domin su zamo mutane da al’umma za ta amfana da su bayan sun kammala zaman gidan yari.
Mai magana da yawun hukumar gidajen yari a Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce an shirya musabakar ce domin kyautata halayyar masu zaman gidan yari.
Tirela ta murƙushe mutane a Gadar Hotoro a Kano Gwagwarmayar Ahmadu Haruna Zago, Bakaniken Jam’iyyaYa bayyana cewa furunan da ya lashe gasar yana tsare ne a gidan yarin Kumawa, inda ya samu kyautar Naira dubu dari.
Na biyu kuma a Gidan Yarin Goron Dutse yake tsare, kuma shi ma ya samu kyautar Naira dubu 50.
Mutum uku yana tsare ne a Gidan Yarin da ke Janguza kuma ya samu kyautar Naira dubu ashirirn.
Da yake jawabi a wurin taron, Shugaban Kungiyar Alarammomi, Gwani Shuaibu Shehu, ya yaba wa Kwamnturolan Hukumar Gidajen Yari na Jihar Kano kan zurfin tunaninsa wajen shirya musabakar.
Ya kuma yaba masa da sama wa tsararrun wuraren da suka dace domin gudanar da al’amuran addini da sauran abubuwan da za su inganta rayuwarsu.
Gwani Shuaibu ya kuam yaba wa Ko’odinentan hukumar kan harkokin addinin, DSC Murtala Nasidi Kabara bisa yadda suke koyar da fursunonin karatun Al-Kur’ani..
A nasa jawabin, Kwanturolan hukumar, Ado Inuwa ya bayayan godiyarsa ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II bisa halartar gasar musabakar da kansa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gidajen yari Gidan Yari a Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Kocin Kano Pillars Usman Abdullahi Ya Ajiye Aikinsa
Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Super Eagles lokacin da Jose Peseiro ke jan ragamar ‘yan wasan Nijeriya.
A kakar bara ta NPFL, ya jagoranci Kano Pillars ta ƙare a matsayi na 9.
Ko da yake Usman bai bayyana cikakken dalilin saukarsa ba, masu sharhi a wasan ƙwallon ƙafa na ganin matsin lamba daga magoya baya da rashin nasara sun taka rawa.
Har yanzu, ƙungiyar ba ta fitar da sabuwar sanarwa kan wanda zai maye gurbinsa ba.
Masu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa a Kano na fatan za a kawo sabon kocin da zai dawo da martabar Pillars a wasannin gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp