Hakuri Da Baiwa (Kyautar) Manzon Allah (SAW)
Published: 14th, February 2025 GMT
Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa.
Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu.
Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu.
Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa.
An karvo hadisi daga Anas khadimin Manzon Allah (SAW) ya ce, wani Mutum ya nemi kyauta daga Manzon Alla (SAW), sai ya ba shi Tumaki tsakanin duwatsu biyu cike da dabbobi amma Annabi sai da ya ba shi dukkansu (SAW). Wanann ya faru ne a lokacin yakin Hunaini, Sahabin shi ne Safwan bin Umayya. Annabi ya gan shi yana ta kallon tumakin, sai ya tambaye shi, sun burge ka ne? sai ya ce Ya Rasulallahi wane Balarabe ne zai ce bai son wannan, take Annabi ya ce masa ya dau sanda ya kora su ya bar masa. Sai Safwan ya koma wurin mutanensa ya ce musu ku Musulunta sabida ‘Muhammad’ (SAW) yana bayar da kyauta irin wacce ba ya tsoron talauci.
Wata rana Manzon Allah (SAW) ya bai wa Abu Sufyan Rakumi 100 a lokaci daya, ya bayar da dukiya mai yawa da ba a san adadinta ba da aka samo ganima a yakin Hunaini.
Yakin Hunaini, yaki ne da ya kasance bayan fitowar Annabi (SAW) da rundunar yaki sama da 10,000 don bude Makkah, amma kuma sarkin Hunain ya karya alkawari da Annabi (SAW), ya ji labarin rundunar da Annabi (SAW) ya fito da ita, sai ya tara ninkin ta Annabi Uku (30,000) kuma ya ce kowannensu ya fito da duk dukiyar da ya mallaka da kuma iyalansa (Mata da Yara), rundunar Hunaini dukkansu maharba ne. Bayan Annabi (SAW) ya bude Makkah, ya samu karin mayaka, sai ya nufi Hunaini, wasu daga cikin Sahabbai suka fara alfahari cewa “Yau babu wata runduna da za ta iya kayar da mu”, bayan Annabi ya fada wani kwari a hanyar zuwa Hunaini, ashe duk rundunar maharba su 30,000 suna sama kowanne da kibiya a hannu, kawai sai suka yo ruwan kibiyoyi ga sahabbai, nan fa kowa ya arta a guje sai Mutum 100 kacal, Annabi (SAW) ya watsa musu kasa duk ta cike idanuwan maharban sannan ya sa Baffansa Abbas ya kira Mutanen Madina. Allah ya ba wa Annabi (SAW) da rundunarsa Nasara, Kafirai sun bar dukiyoyinsu da Iyalansu.
Wannan dukiya da suka bari mai yawa, Annabi (SAW) ya jira ko za su dawo su Musulunta ya mayar musu da dukiyarsu amma ba su dawo a lokaci ba har sai da Annabi (SAW) ya rabar da dukiyar baki daya sannan suka dawo.
Annabi (SAW) ya nemi zabinsu a kan wanda ya fi, muhimmanci a wurinsu, Dukiyarsu ko Iyalansu, sai suka zavi Iyalansu, an ce Annabi ya maida musu da ‘yan mata sama da 6,000.
Annabi (SAW) ya ba wa baffansa Abbas dukiya (zinare) ya dauka iya karfinshi, an kawo wa Annabi (SAW) daga ganimar yakin kudi Dirhami 90,000, Annabi (SAW) ya sa aka shimfida tabarma a Masallaci, har sai da ya rabar da kudin gaba daya, Abbas ya ce ya dana a yakin Badr sai da kasa na biya fansar Mutum Uku, kai ka maida ni Talaka don haka yanzu ga kudi a maida min da kudina, shi ne Annabi (SAW) ya hore shi da ya diba zinare iya karfinshi. Bayan an gama rabo sai wani ya zo ya ce Ya Rasulallahi ina nawa? Annabi ya ce masa komai ya kare amma ya je ya ci bashi zai biya masa in an samu kudi. Sai Sayyadina Umar ya ce Ya Rasulallahi Allah bai dora maka abin da ba zaka iya ba, Annabi (SAW) ya ki wannan maganar, sai wani daga cikin Sahabbai ya ce Ya Rasulallahi ka ciyar, kar ka ji tsoron wani talauci daga Ubangjin Al’arshi, sai Annabi (SAW) ya yi farin ciki kuma aka ga bishara a fuskarsa.
An karvo daga Mu’awwizu bin Afra’a (Sadaukin Badr) yana cewa, wata rana na zo wurin Annabi (SAW) ina dauke da faifai da Dabino a kai, hakikanin Hadisin ‘yarshi ce ya aiko ba shi ne ya zo da kanshi ba, ta ce na zo wurin Annabi (SAW) da faifai akwai Dabino danye da Vuluvutu danye wanda bai girma sosai ba a kanshi, sai Annabi (SAW) ya ciko hannunsa da kayan kwalliya na Mata (Awarwaro) na zinari ya ba ni.
Khadiminsa Anas, ya kasance yana cewa, Annabi (SAW) ba ya ajiye komai sabida gobe a kan-kansa amma yana ajiye wa Matansa abincin Shekara, don haka in sun ba shi ya gode, in ba su bashi ba, daman nasu ne.
Yana daga cikin kyautar Annabi (SAW), wata rana wani ya tava zuwa wurinsa yana neman taimako Annabi kuma (SAW) lokacin babu, sai ya nemo rancen rabin masaki na Dabino ya bashi. Wanda kuma ya bai wa Annabi (SAW) wannan rancen, da ya zo amsar bashinsa sai (SAW) ya ba shi Masaki cikakke. Annabi ya ce masa, rabin biyan bashi ne, dayan rabin kuma kyauta ce.
কীওয়ার্ড: ya ce Ya Rasulallahi
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jadadda Cewa: Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kan Iran Zai Fuskanci Mayar Da Martani
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas ga manufofinta na ketare.
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Rudun gwamnatin yahudawan sahayoniyya, wadda take ganin za ta iya gindaya wa Iran abin da ya kamata ko kuma bai kamata ba, rudun tunani ne da ya yi nesa da hakikanin gaskiya, ta yadda bai cancanci mayar da martani ba.
Araqchi ya kara da cewa: “Duk da haka, jajircewar Netanyahu wani abin lura ne, a yayin da yake kokarin neman bayyana wa Shugaba Trump abin da zai iya ko kuma ba zai iya yi a diflomasiyyarsa da Iran ba!”
Ministan harkokin wajen ya yi nuni da cewa: “Abokanan Netanyahu a cikin tawagar Biden da ta gaza – wadanda suka kitsa makarkashiyar hana cimma yarjejeniya da Iran – suna kokarin nuna zaman tattaunawar da ake yi ba na kai tsaye ba da gwamnatin Trump a matsayin wani kuskure ne kuma tamkar hoton sauran yarjejeniyar nukiliya ce da aka gudanar.”