Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani
Published: 4th, February 2025 GMT
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsohon uban gidansa kuma magabacinsa Malam Nasir El-Rufai.
Uba sani ya ce babu kamshin gaskiya a maganganun da ke yawa cewa shi da tsohon gwamnan El-Rufai suna zaman doya da manja.
Ya bayyana haka ne a yayin hirar da kafar tala bijin ta TVC ta yi da shi a ranar Litinin, inda ya ce “alakarmu tana nan yadda ta ke, babu wata matsala, kamar yadda ake rade-radi.
Am fara tunanin cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Uba da El-Rufai ne bayan da gwamnati mai cin ya yi zargin Gwamnatin El-Rufai da barin masa bashin biliyoyin Naira da kuma karkatar da wasu kudade.
Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa BaA kwanakin baya Gwamnatin Uba Sani ta sallami wasu mukarraban El-Rufai da ke cikinta, masu rike da mukaman kwamishinoni kan zargin badakala.
Masu sharhi da magoya bayan tsohon gwamnan dai na zargin Gwamnatin Uba Sani da yi wa Nasir El-Rufai da mukarrabansa bi ta-da-kullin siyasa, zargin da ta karyata.
Zargin El-Rufai da karkatar da kudade, ya kai ga Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin binciken El-Rufai, wanda ta ce ta same shi da laifin da ake zargin sa, amma tuni ya musanta zargin.
Amma da aka yi wa gwamnan tambaya game da hakan, ya bayyana cewa bangaren majalisa na aiki ne a matsayin mai cin gashin kansa ba a karkashin gwamna ba, kuma suna da ’yancin gudanar da ayyukansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
Rahoton rashin fahimtar da aka fara yadawar, ya biyo bayan taron kwamitin zaman lafiya da kwantar da tarzoma na jihar, wanda Darakta Janar ya jagoranta a ranar 4 ga watan Satumba.
Rashin fahimtar sahihin sakamakon taron ya sa wasu suka rahoto cewa, kwamitin ya dakatar da Malamai daga yin wa’azi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar ba ta da hurumin haramtawa Malaman Addinin Musulunci yin wa’azi sai dai in ya bayyana a fili an taka ƙa’idojin hukumar da ta shimfiɗa”.
A cewar Hukumar, an kira taron ne domin gabatar da fom din rijistar yin wa’azi ko Da’awah da kuma bin tsarin tantancewa.
Ta bayyana shirin a matsayin wani yunkuri na wayar da kan jama’a don “hana rashin fahimtar juna da kuma daƙile yaɗuwar wa’azin yaudara” a faɗin jihar Neja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp