UNICEF Ya Kara Jan Hankalin Gwamnatin Najeriya Game Da Ilimin ‘Ya’ya Mata
Published: 27th, January 2025 GMT
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su kara himma wajen yara mata na samun damar yin karatu.
Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah, ne ya yi wannan kiran a Kano a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta 2025.
Ya kara da cewa alkaluma sun nuna cewa ‘yan mata miliyan 7 da 600 ba sa zuwa makaranta, inda shiyyar Arewa maso Yamma da arewa maso gabas ke da kashi 48 cikin 100 na adadin.
Ya danganta wannan kididdigar da abubuwan da suka hada da talauci da ka’idojin zamantakewa da nuna wariyar jinsi, wadanda ke dakile bai wa ‘ya’ya mata damar samun ilimi.
A lokacin da yake gabatar da bitar ayyukan UNICEF na inganta karatun yara mata da kuma ci gaba da karatu, shugaban ofishin kula da kananan yara na jihar Kano, Rahama Mohammed Farah, ya ce asusun ya samu hadin gwiwa da gwamnati da al’umma wajen magance matsalolin.
Ya ce UNICEF ta kuma yi amfani da tallafin kudi da sauran abubuwan karfafa gwiwa don karfafawa iyaye gwiwa, su yi rajistar ‘ya’yansu mata da tabbatar da ganin sun ci gaba da zuwa makaranta.
Ya yi bayanin cewa, “UNICEF ya yi kokari matuka a wannan fanni, ciki har da bayar da kudade domin karfafa musu gwiwa wajen tura ‘ya’yansu mata zuwa makaranta tare da tallafa musu zuwa matakin sakandare”.
Ya yi bayanin yadda asusun ya ke inganta fasahar rubutu da karatun ‘ya’ya mata ta hanyar cibiyoyin karatun ‘yan mata don ‘yan mata (G4G), inda kimanin ‘yan mata da ke zuwa makaranta miliyan 2 da 600 su ke samun ilimi ta hanyoyin sadarwa da suka hada da rediyo da talabijin a hakin yanzu.
“UNICEF ya kuma inganta kwazon malamai don ilmantar da ‘ya’ya mata, tare da kara yawan malamai a makarantun firamare 42,000“, inji Farah.
Ya yi bayanin cewa UNICEF ya kuma gina tare da gyara wuraren tsaftar ruwa a makarantu 33 a fadin jihohin Kano da Jigawa, wadanda ‘yan mata 19,622 ke amfani da su.
Ya ce asusun yana kuma aiki tare da masu tsara manufofi a fannin ilimi don tabbatar da ingantacciyar kariya ga yara da ayyukan makaranta ga yara mata, yayin da kuma yana inganta kwazon malamai da za su jagoranci yara mata.
Taron manema labaran ya samu halartar ‘yan jaridu daga jihohin Kano, da Jigawa da Katsina.
Usman Mohammed da Isma’il Adamu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
Daga Usman Muhammad Zaria
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.
Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.
Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.
Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen tsaro.
CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.