UNICEF Yace Yara Na Fama Da Karancin Abinci Mai Gina Jiki A Nijeriya
Published: 26th, January 2025 GMT
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025.
Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan 1.2 kuma daga cikin adadin yara 250,000 ne ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki (SAM).
A cewarta, don magance matsananciyar wahalar da ake fama da ita a fadin Najeriya, ciki har da Sokoto, Zamfara, da Katsina, ta bukaci sama da dala miliyan 250.
Ta kuma bayyana cewa, UNICEF na da niyyar kula da yara 400,000 ‘yan kasa da shekaru 5 da ke fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki yayin da karin yara 200,000 a yankin arewa maso yamma za su bukaci Shirye-shiryen Abinci a 2025 idan aka kwatanta da 2024.
“Sama da yara 300,000 a Sokoto da Zamfara na bukatar rigakafin cutar kyanda”
Domin magance kalubalen yadda ya kamata, wakiliyar UNICEF ta bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su fadada ayyukan kiwon lafiya da karfafa shirye-shiryen kiwon lafiyar al’umma.
Ta kara da cewa, lamarin yana bukatar daukar matakin gaggawa, da hada kai, da kuma jajircewa wajen ceto rayuka, da maido da fata, da gina kyakkyawar makoma ga yaran Zamfara da sauran su.
COV/AMINU DALHATU/Wababe
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa sauyin jam’iyyar da manyan ‘yan suke yi zuwa jam’iyyar APC ana kamba ma shi fiye da yadda ya kamata, yana cewa wannan sauyin ba zai shafi kokarinsa na neman mafita ga matsalolin Nijeriya ba. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano yau Litinin.
El-Rufai ya bayyana cewa shi ne na farko da ya koma jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) daga APC a kokarinsa na warware matsalolin Nijeriya ta hanyar kawar da tsarin kawancen siyasa.
Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC“SDP ta hankali wajen nemo mafita ga matsalolin Nijeriya da kuma ba da dama ga wadanda a siyasance ta hanyar kawancen jam’iyyu” in ji El-Rufai.
Ya kara da cewa sauyin jam’iyyar ‘yan siyasa ba shi ne babban batu ba, a cewarsa, babban batu shi ne wanda zai iya warware matsalolin Nijeriya da kuma isar da wannan ga al’umma ta yadda za su fita zabe a ranar zabe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp