2025-07-27@06:45:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3097
«wanzar da zaman lafiya»:
Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) ta sanar da cewa; Da akwai ‘yan kasar Sudan miliyan 4 da suke rayuwa a kasashen makwabta da suke fuskantar hatsarin yunwa. Sanarwar hukumar ta kunshi cewa mutanen sun fice daga kasarsu ne tun asali saboda neman abinci da kuma mafaka daga yakin da ya barke a cikin Sudan...
Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen. Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond. Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.76, kwatankwacin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako. Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu...
Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane...
Dakatar da ayyukan wuce gona da iri kan Iran wani sharadi ne na ci gaba da tattaunawar makamashin nukiliya Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa: Sharadin ci gaba da gudanar da zaman shawarwarin makamashin nukiliyar Iran shi ne dakatar da duk wani matakin wuce...
Dalibai 29 ne suka rasa rayukansu sakamakon turmutsitsin a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya yayin tserewa fashewar taransifoma Akalla dalibai 29 ne suka mutu a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wani turmutsutsu sakamakon fashewar tiranfomar lantarki a lokacin jarrabawar sakandare, a cewar ma’aikatar lafiya ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Wata takarda daga...
Kasar Sin ta kawo karshen aikin bayar da agajin gaggawa mafi girma a gundumar Rongjiang da ke lardin Guizhou, a yankin kudu maso yammacin kasar da misalin karfe 10 na safiyar ranar Lahadi, yayin da aka kammala ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya kamar yadda mahukuntan yankin suka bayyana. Lardin Guizhou da...
Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon kwana guda a wasu sassan jihar. Wannan na zuwa ne bayan wani hargitsi tsakanin jami’an tsaro da wasu ɓata-gari a yankin Kakuri. Wuraren da dokar ta shafa sun haɗa da Kakuri Bus Stop, Kurmi Gwari, Monday Market, Afaka Road, da Kakuri GRA. Wata sanarwa da Gwamnatin...
Adadin mambobin JKS na ci gaba da karuwa, inda rassanta ke ci gaba da ingantuwa. Baya ga haka, sassanta a matakin farko na kara karfi. Wannan na kunshe ne cikin rahoton kididdiga da sashen shirye-shirye na kwamitin kolin jam’iyyar ya fitar yau Litinin, gabanin bikin cika shekaru 104 da kafuwar jam’iyyar. Zuwa karshen 2024, jam’iyyar...
Hukumomin Iran sun bayyana cewa aƙalla mutum 935 ne suka rasa rayukansu a hare-haren Isra’ila yayin yaƙin kwanaki 12 da ya gudana tsakaninsu da ƙasar. Cikin waɗanda suka mutu sun haɗa har da mata 132 da yara 38, kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Shari’a, Asghar Jahangir, ya bayyana a wata sanarwa a ranar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin...
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran. Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar...
Bayan hare-haren da kungiyoyin yan ta’adda masu iko da kasar Siriya suka kai kan wani Cuci a kasar Siriya jami’an gwamnatin kasar Siriya sun nuna damuwarsu da yiyuwar wadannan kungiyoyi su kawo hare-hare a cikin kasar ta Lebanon musamman a cikin wadan nan kwanaki na makokin Imam Hussain (a). Wani Jami’in gwamnati a kasar ta...
JMI ta bawa kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen makamai masu linzami wadanda ake iya cillasu daga cikin tekuna mai suna Ghadr. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce makamai mai linzami samfurin Ghadir wanda ake iya cilla shi daga cikin teku ya shiga hannun sojojin kasar Yemen sannan bisa bayanan wasu kasashen yamma...
Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula. Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile...
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus. Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga...
Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran. Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya. Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa. Shin ko me...
Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka. Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar...
A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya. Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Najeriya, musamman a fannin tattalin...
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata....
Fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal, ya bayar da tallafin Naira miliyan 80 don taimaka wa mutane masu fama da cutar mafitsara da matsalar gwaiwa domin yi musu tiyata kyauta. An gudanar da tantance marasa lafiyar a Asibitin Ƙashi na Amadi Rimi kafin a fara aikin tiyatar a ranar Asabar da ta gabata....

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu....
Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka. A...
Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bayan shafe shekaru 30 suna rikici Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Rwanda sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, shekaru talatin bayan rikicin da ya barke a shekara ta 1994 da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane daga bangarorin biyu. An rattaba hannu kan...
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin...
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu. A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira ga mazauna wani kauyen dake yankin Nyingchi na jihar Xizang mai cin gashin kai, da su rungumi akidar ‘yan uwantakar kabilarsu, da samar da yanayin gudanar da rayuwa mai kyau. Shugaba Xi ya yi kiran ne cikin wasikar da ya mayar ga mazauna kauyen, wadda a ciki...
Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila. Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta. Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara...
Tsohon tauraron ƙungiyoyin Manchester United da Real Madrid, Ruud van Nistelrooy ya ajiye aikinsa na horas da Leicester City bisa fahimtar juna. Wannan na zuwa ne bayan da a ƙarƙashin jagorancinsa ƙungiyar ta yi wasanni 27 da ta gaza taɓuka abin a zo a gani a cikinsu, lamarin da ya kai ta ga faɗawa gasa...
“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60,...
Har ila yau, Maishaddar ya ci gaba da bayyana cewa; dangane da batun da mutane ke yi na cewa, alaka tsakaninsa da jarumi kuma mawaki Umar M. Sharif ta yi tsami, duba da cewa; an daina ganinsa a ci gaban shirin ‘Gidan Sarauta’ da Maishadda ke daukar nauyi, Bashir ya bayyana cewa; wannan magana ko...
Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”. Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji. Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar...
Sojojin mamayar HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yammacin kogin Jordan, inda a safiyar yau lahadi su ka kutsa cikin wani gida a garin Jenin,kamar kuma yadda ‘yan share wuri zauna su ka kutsa gidan wani bafalasdine a kudancin Nablus. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu suna cewa; an yi taho mu gama...
Kwamandan rundunar Kudus dake karkashin IRGC Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni ya bayyana cewa; Iran ta samu nasara, kuma nasara ce wacce za ta dore da yardar Allah. Birgediya janar Isma’ila Ka’a’ni wanda ya halarci jana’izar shahidan ta’addancin HKI ya bayyana cewa; Daga yanzu zuwa gaba abinda yake gabanmu shi ne ci gaba da samun nasarori....
Kwamitin koli na tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran. Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar...

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Kira Da A Gudanar Da Bincike Kan Wuce Gona Da Irin Amurka Da Isra’ila Kanta
Iran ta yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a hukumance kan zaluncin ‘yan sahayoniyya da Amurka Mataimakin babban jami’in kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar shari’a kuma sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta Iran ya yi la’akari da matakin wuce gona da iri na baya-bayan nan da yahudawan...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta san mika wuya ba, kuma tana rubuta tarihin mutunci da jinin shahidanta A jawabin da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi bayan halartar jana’izar shahidan Quds ya jaddada cewa: Iran ba ta san ma’anar mika wuya ba, yana mai fayyace cewa tarihi...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Cewa: Iran Tana Da Hakkin Tace Sinadarin Uranium A Kasarta
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a...
Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba! A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa...

Jakadun Kasa Da Kasa Sun Bayyana Muhimmancin Hadin Gwiwa Wajen Amfani Da Makamashin Nukiliya Ta Hanyar Lumana
A nata bangare hukumar CAEA ta ce za ta hada hannu da hukumar kula da makamashin nukuliya ta duniya IAEA da sauran abokan hulda daga kasashe masu tasowa, wajen inganta kirkire-kirkire da raya makamashin nukiliya. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
Ya ci gaba da cewa, Hukumar ta NPA, ta yi kasafin da dara haka, na wannan adadin, musaman ganin cewa, ta na burin, kara inganta ayyukanta, yadda za su yi dai-dai, da yadda ake gudanar da ayyukan, a sauran Tashoshin Jiragen Ruwa na duniya. Shugaban Hukumar ya kuma sanar da cewa, a shekarar 2024, Hukumar...
Albarkacin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa, ofishin dakile miyagun kwayoyi na kasar Sin ya gabatar da rahoton halin da kasar take ciki a wannan bangare, inda alkaluma suka nuna cewa, a shekarar 2024, hukumomi masu alaka sun binciki laifuka masu nasaba da miyagun kwayoyi fiye da dubu 37, da cafke masu...
Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da...
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta. An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan. Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani...
Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da...
Har yanzu dai gwamnatin Syriya ba ta komai ba game da barna da hasarar rayuka da makamai da kuma jiragen da ake amfani da su da ta sararin samaniyarta ke haifarwa ba. Shafin Intanet na kafar Enab na kasar Syria ya wallafa wani labari a ranar 15 ga watan Yuni game da shirun da gwamnatin...
Mahaifin angon da ’yan uwan angon na jini da danginsa na daga cikin mutane 13 da aka yi wa kisan gilla a hanyar ɗaurin auren ango, inda aka ƙona gawarwarkin wasunsu a cikin motar da ta ɗauko su, a yankin Mangun da ke ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Mahaifiyar angon, Malama Faji Sani da...
Iran ta gudanar da gagarumin jana’izar tare da karramawq ga kwamandojinta da masana kimiyyar nukiliya da wasu ’yan kasar da Isra’ila ta kashe a yankin kwana 12 da aka gwabza a tsakanin ƙasashen. Iran ta shirya gagarumin jana’izar a ƙwaryar birnin Tehran kwana huɗu bayan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya...