Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba.

Jihad Taha kakakin kungiyar ya bayyana cewa Hamas tana nazarin shawarar da Witskoff ya gabatar da tsagaita wuta a gaza wanda ya amince da dakatar da wuta na wucin gadi sannan a sake komawa yaki da kuma shigo a kayakin agaji.

Y ace shawarar bata ambaci ficewar sojojin HKI daga yankin ba.

Taha ya bayyana cewa shawarar bata da wani abin dogaro wanda Hamas da kungiyoyin masu gwagwarmaya zasu riki na tsagaita wuta a gaza. Amma dukm da haka suna nazarinsa kuma zasu bayyana ra’yinsu nan gaba.

Ya Zuwa yanzu dai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da 54000 a cikin shekara da rabi da suke fafatawa.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 

Kamfanonin wutar lantarki sun yi barazanar katse wutar a fadin Najeriya saboda tarin bashin da ya haura Naira tiriliyan 5.2 da suke bin gwamnati.

Taurin bashin, wanda ke barazana ga ci gaba da ayyukan kamfanoni, ya hada da Naira tiriliyan 1.2 na wutar da aka samar a watanni shidan farkon shekarar 2025, da Naira tiriliyan 2 daga 2024, da kuma bashin da aka gada tun daga 2015 wanda ya kai Naira tiriliyan 1.9.

Shugabar ƙungiyar kamfanonin samar da wutar lantarki, Dakta Joy Ogaji, ta bayyana cewa kamfanonin sun daɗe suna nuna kishin ƙasa ta hanyar ci gaba da samar da wuta duk da rashin biyan su kuɗaɗensu, amma yanzu sun gaji.

Ta bayyana cewa kudin da ake kashewa wajen samar da wuta a kowane wata yana kaiwa Naira biliyan 250, amma Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan 900 kacal a kasafin kuɗin 2025, kuma har zuwa yau ba a samu cikakken tabbacin samun wannan kuɗin ba.

An rufe masana’antu 1,724 bisa rashin bin dokokin aiki a Guinea NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa

Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnati tana ƙoƙarin rage wani ɓangare na bashin, amma har yanzu ba a bayyana yadda hakan zai faru ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
  • Shugaban Amurka Trump Ya Bukaci Gurfanar Da Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama A gaban Kuliya
  • Sheikh Qasem: Nuna Halin Ko In-Kula Na Duniya Ne Ya Jawo Kisan Kiyashi A Gaza
  •  Kungiyar Malaman Musulmi Ta Yi Fatawar Wajabcin Kawo Karshen Killace Gaza
  •  Netanyahu: Ba Za Mu Daina Yakin Gaza Ba
  • Kamfanonin lantarki za su katse wuta kan bashin N5.2trn da suke bin gwamnati 
  • WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
  • MDD Ta Gargaɗi Isra’ila Kan Tilasta Wa Al’ummar Deir al-Balah Na Gaza Tashi
  • Wata Kungiyar Ta Bukaci Shugaban Kasa Ya Cika Alkwarin Marigayi Shugaba Buhari Game Da Shehu Usman Aliyu Shagari
  • Kungiyar Hamas Ta Yi Suka Kan Kame ‘Yan Gwagwarmaya Da Hukumar Falasdinawa Ke Yi